43

67 1 0
                                    

Sai azahar ya dawo yana dawo suka koma gidan Umma sukayi sallama suka tafi tare da Sultan. Sai ga su a Duste har gidan Mahmud, hakan baƙaramin daɗi ya yayiwa Mahmud ba, dan zuwan bazata ne, be san maganar accident ɗin Aliyu ba sai shi ma be yi masa ba. Anan suka kwana washegari suka wuce Bauchi nan ɗin ma kwana ɗaya suka yi suka juyo dan haka kawai kawai yake so ya koma gida, ya yi niyyan su yi ko da sati ne a Bauchi amma babu halin yin haka saboda hankalin sa yaji kawai yayi gida, ji yake kamar da wani abu da suke ɓoye masa, tunda ya zo be yi waya da Aliyu ba, be gan shi a platform ba, dole hankalin sa ya tashi kuma ance masa bashi da lafiya. Haka suka juyo cike da kyautar ƴan uwa da abokan arziki. Koda tsohuwa taji labarin Sajjad ya zo, ya sha gori kala da kala harda su gorin ai ya iya fulfulde shiyasa be zo ba kuma zata wanke shi tas. Yana hanya ya ji labarin abinda tace sai kawai yayi murmurshi yana kashe wayar.

"Wannan murmurshin naka ko?

"Ke de kawai ki ce na sanar da ke".

"Kar ma ka sanar dani".

Wani shegen murmurshin ya kuma yayi yana canza giyar mota be ce komai ba. Ba su ne suka iso ba sai ƙarfe ɗayan dare, iya gajiya sun gaji, Nilah suna isowa ta buɗe wani ɗakin kawai ta  kwanta babu abinda ta cire dan sun yi Sallah sun ci abinci. A ɗakin sa ya kwantar da mazan su kuma matan ya kai su ɗakin su Aliyu. Ɗakin su Hafiz ya buɗe ya ganta a ciki ta kwanta tayi rufda ciki, girgiza kai kawai yayi ya shiga ya cire mata takalmi ta rage mata kayan jikin ta ya gyara mata kwanciyar ta. Shikam sai da ya watsa ruwa sannan ya kwanta. Washegari da sukayi sallah kam sun yi ramakon baccin su daga su har yaran, babu wanda ya san ya dawo, sai da aka ga motar da ya tafi da ita. Ba kuma a neme su ba dan ansan sun gaji ne. 

Sai da suka tashi sukayi wanka suka shirya sannan suka fito gidan abin su fes da su ga kuma yaran su.

Yusuf yace, "Innalillahi, wannan kuma daga ina?

Ya faɗa yana kama hannun Sultan, dan karya yaron yayi masa daga kallo ɗaya ya shiga ran sa.

Sajjad yace, "Ɗan mu ne".

Hafiz yace, "Ku kam ƴaƴa nawa zaku ƙwace ne kam? Ga Hauwa'u kun ƙwace ta ga kuma wani kun samu".

Murmurshi kawai Nilah tayi tana gaida su tare da wucewa ciki.

Yace, "Daɗi na da ku sa ido bala'i ne ne da ku wallahi".

Shima ya faɗa yana wuce su, a wurin Ummi ya same ta ita da Bintu Ummi sai faɗa take yiwa Bintu akan fitowar ta kullum, tunda ta tare kullum sai sun fito anan take wuni sai dare idan ya zo su tafi. Duk sanda ya zo zai shiga part ɗin Anty sai ya tuna da Antyn sa, yanzu shikenan ta tafi ko? Yayiwa kan sa tambayar yana bawa kan sa amsa da ehh baza ta dawo ba. Sannan yayi mata addu'a ya shiga fuskar sa ɗauke da murmurshin zallar kewa da kuma na tuno wani abu ne.

"Sajjad kai ne?

Cike da kunya ya ƙara so ya zauna a wajen ƙafar ta. Yana gaida ta.

"Ina Maryam?

"Tana gidan Ƙaramin".

"Kuma ya zai ɗauke mana ita?

"Nidai ba ruwana kun fi kusa".

"Anty laifin ki ne. Kawai ki ce kina san ƴar ki".

"To zan sanar da shi. Idan hakan zai faran ta ran autana".

Kunya autan da ta kira shi da shi ya bashi hakan yasa shi yin murmurshi jin kunya yana sunne kai. Ita kam dariya tayi kawai tana girgiza kai. Kafin ta ɗaura kan sa a cinyar ta ta fara shafa wa cike da wata irin kulawa, yayinda Sajjad ya ji shi wani iri, ta tuno masa da Anty gaba ɗaya sai yaji kewa ta dabaibaye shi. Da wata irin muryar lallashi mai nuna da bada hakuri.

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now