23

49 1 0
                                    

Koda ya dawo daga meeting ɗin be same shi a office ɗin ba, yasa aka kawo masa coffee ya yaje bakin window ya tsaya yana sha yana tunanin da ya saba. Jin an shigo office ɗin nasa ya sa shi, da kuma ƙamshin turaren da ya ji yasa shi ƙin juyowa sanin cewa Aliyu ne.

"Sajjad".

Shiru yayi be amsa ba.

"Sajjad!".

Ya faɗa da ƙarfi. Ɗan juyowa yayi tare da cewa.

"Uhm". 

"Nima ko ka dena min maganar?

Kallan yarinyar yayi, ganin hannun ta riƙe da alawa, tana sha, kallan da yayi mata ne yasa ta dena shan alawar ta shiga hankalin ta. Yayin da Aliyu ya girgiza kan sa, ya je ya ajje ta akan kujera, ya dawo gaban table ɗin sa ya zauna yana kallan sa.

"Sai nace ka zauna zaka zauna?

Haɗe rai yayi yaje ya zauna, tare sa janyo plate ɗin da aka kawo masa cake, ya ɗauka ya fara ci yana haɗawa da coffee.

"Me yasa ba zama rabu da ita ba?

"Wa?

"Kafini sani".

Ƙara haɗe fuska yayi yana tauna cake ɗin. Wallahi da ace yau shine Babba Yaya Aliyu be isa ba ya zo yana masa wannan maganar, bama zai ɗauke ta aiki ba, bare kuma har takai ga yin haka.

"Abinda nake so da kai. Tun mun biyu, tun muna shaida juna, tun wani be ji ba, ka dena shiga harkar ta da yarinyar ta. Na faɗa maka, wannan ya zama karo na farko kuma ya zamana na ƙarshe da zan yi maka magana".

"Uhmm".

Yace, be kuma cewa komai ba, amma a zuciyar sa wani irin ƙudiri ne danƙare a ciki.

"Na faɗa maka, kada kuma na sake naji labari wallahi".

"In Sha Allah".

Ya tashi yayi ya fice bayan ya ɗauki yarinyar, da kallo ya bishi  kafin ya saki wani irin murmurshi na zaki sani.

Sai da ya gama abinda zai yi sannan ya fito daga office ɗin, yana fitowa kuwa itama tana fitowa zata tafi, a gaban ta ya tsaya.

Yace, "Wannan ya zaman karo na ƙarshe da zan sake ganin ki da yarinyar nan a cikin companyn nan, ko ki zaɓa ko aikin ki? Ko kuma yarinyar ki".

Yana faɗa ya juya zai tafi da sauri ta zagayo ta gaban sa.

Tace, "Dan Allah kayi haƙuri har  zuwa sanda zata warke. Wallahi bata da lafiya kamin rai".

"Wato reni ya fara shiga tsakani na dake ko? Har na faɗi abu ki zo kina magana akai ba?

Sunkuyar da kan ta tayi hawaye na zubo mata.

"Kayi haƙuri".

"Na miki rai ko? Kashe ki nace zan yi ?

"Zaɓi na baki. Idan kin zaɓi zaɓin da na baki, idan yarinyar ki kika ɗauka gobe naga resignation letter, idan kuna ƴar ki kika zaɓa naga baki zo da ita ba".

Daga haka ya wuce ta ya barta hawaye na zaryar zubo mata tana sa hannu tana sharewa a gaban ta suka wuce kafin itama ta sa kai ta wuce. Duk ita ta jawowa kan ta.

Yana zuwa ya tarar da Inna a sashen Anty, hakan yasa shi duba iya lafiyar mahaifin shi be ko kalle ta ba ya wuce, dan a yanzu shima baya san hayaniya da de dane sai ya tsokane ta, koda kuwa bazata amsa ba, amma a yanzu shima ta kan sa yake bata lokacin ɓatawa ba.

"Sajad".

Inna ta kwala masa kira. Dawowa yayi ya tsaya daga bakin ƙofa.

Yace, "Gani".

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now