2

125 2 0
                                    

   

Cikin  dare ya tashi da zazzaɓi gashi da wani irin raki rashin lafiya ko yaya ne indai yana ciwo to sai ya nuna bare wannan da ya haɗu da damuwar maganar da za'a faɗa masa,  wanda ya rasa ina ta nufa bare kuma ya san abin yi,  kasa cigaba da zama yayi shi kaɗai yayi ya fito, ɗakin su Al-ameen ya shiga ya kwanta a kujera sai dai kuma wani irin sanyi yake ji kafin kace me ya fara rawar sanyi, lokaci guda kuma jikin sa ya rikice.

Kusan lokaci guda suka tashi suna kunna lamp ɗin dake gefen su.

"Sajjad".

Suka faɗa a tare suna nufo shi, Aliyu ne ya fara taɓa shi da sauri ya ɗauke hannun shi tsabar zafin da yaji jikin sa yayi, kafin ya ƙara kama shi ya zaunar shi yana zama a gefen sa.

Al-ameen yace, "ko ruwa sanyi za'a goge masa jikin sa dashi ko zazzaɓin zai ragu".

Aliyu yace, "Ko mu kira Daada ba?"

Al-ameen yace, "A'a Daada da wannan daren? Kar hankalin Anty ya tashi".

Ganin yana neman kwanciya yasa shi, kwantar dashi a cinyarsa yana shafa masa kai, bargo Al-ameen ya ɗauko ya rufa masa ya ɗauko Pcm ya bashi tare da maganin malaria, Aliyu ya zuba masa ido, jini ɗaya ba wasa ba, ko yane dole sai kaji kana san ɗan uwan ka bare su biyu kawai Mahaifiyar su ta haifa duk da babu shaƙuwa a tsakanin su amma akwai wata irin soyayya dake tsakanin sa da ɗan uwan sa shi kan sa yasan yana yi masa wani irin so da shi kan sa be yiwa kan sa ba, sai dai ko da wasa be taɓa nuna hakan ba, saboda irin gidan da suka ta so yasan da ace su biyu ne a gidan su ya tabbatar da soyayyar da yake masa sai ta fito fili.

A hankali ya fara ƙoƙarin kwantar dashi ganin ya sami bacci, amma ko kan sa be gama ɗauke wa ba ya damƙe hannun sa tare da ƙara shigewa jikin sa, ajiyar zuciya ya sauƙe yana ƙara gyara masa rufar da bargo, ya jinjina da kujerar, a haka bacci ya ɗauke shi, shima ba kuma farkawa ba sai da Al-ameen ya tashe shi sallah har lokacin Sajjad na bacci, daƙyar ya kwantar da shi saboda irin ƙwaƙumar da yake masa, yana ajje shi kuwa shima ya tashi. Koda sukayi sallah kasa baccin yayi kawai kwanciya yayi maganar bawan Allahn nan tana dawo masa a rai. Be san gari ya waye ba sai sa yaji muryan Anty da Mama suna magana da alama sun sanar masa, zaune ya tashi yana kallan su.

Daada yace, "Ka tashi ka shirya mu tafi asibiti".

Mama tace, "Ashe baza'aje ba, kamar ka manta jinyar Sajjad wanka ma yi masa ake".

Ummi tace, "Wallahi kuwa, ba abinda yake sai sallah ita ma da anayi nasan yi masa za'ayi".

Aliyu yace, "Sai shegen ragwanta ba, jiya be barmu munyi bacci ba".

Anty tace, "Allah sarki Auta na, rabu da su kaji ko? Ya jikin?"

Ya faɗa tana hawa kan gadan da yake shi kuma ganin haka yasa shi kwanciya a kafaɗar ta.

Inna tace, "sai kuyi sauri ku tafi asibitin kar jikin ya rikice ku shiga uku".

Su duka suka rangaya suka tafi asibitin amma banda Inna, Baba dake sa wuri ya fita be ji labari ba sai sa suka je asibiti dan haka  asibitin shima ya nufa lokacin har an sa masa drip ya sami wani baccin.

"Sai wasu su koma gida ai anyi yawa haka, ku wuce aiki".

Bintu tace, "A barni zan kula da shi".

Hafiz yace, "baki da hankali shiyasa kika ce zaki kula da shi".

Yusuf yace, "Bata san waye Sajjad ba shiyasa tace haka".

Kumbura fuska tayi, tana hararan su.

Ummi tace, "ku faɗa mata waye shi da har take nema masa shishshigi".

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now