25

65 2 0
                                    

Be tsaya wai ɗaukan waya ya kira ɗaya daga cikin masu sojojin sa ba yayi kawai ya kwashi kayan a hannun yayi gaba, tsabar yarda yake sauri yau ji yayi elevator ɗin bata tafiya, tana buɗewa kuwa ya fice, sai ganin sa sukayi kamar an koro shi ya fito.

"Sir..."

"Waya baka wannan abun?

Ya faɗa a wani hanzari gami da sauri kai kace mai saurin baki ne.

"Wata ce ta bani".

"Wacece?

"Ai bata faɗi sunan ta ba".

"A office ɗin da ka nuna min kuma take aiki?

"Ehh".

Be ƙara magana ba, ya nemi shigewa mota har buɗe zai shiga, sai kuma ya daka yana kallon su ganin duk sun shishiga motar su zasu bishi, ganin ya dakata yasa su zuwan sa.

Yace, "Ni ku ke yiwa aiki ko?

Jinjina masa kai sukayi.

Yace, "To ku tsaya ku kula da wannan companyn kada a kuskura a bar koda mai gadi ne".

"Akwai masu kula da irin wannan ɗin da ka samu, amma mu kai kawai aka ce mu kula da shi. Zan turo a kula da nan ɗin, ku bishi ni zan jira har sai team ɗin sun zo".

Wani irin mashahurin takaici ne ya kama Sajjad, ji yayi kamar ya make shi tsabar haushi da takaici, be ƙara magana ɗaya ba ya shiga motar sa ya ƙara gaba, wannan tsaro da Abba yasa ake bashi kai kace shine Abban, shi ba soja ba, ba komai ba ana zaune lafiya, ƙara fitowa yayi ya koma office ɗin sa ya ɗauko system  ɗin sa, sannan suka tafi, amma ko a mota tunanin abinda ya ki kuma ya faru kawai yake yi, sai kuma ya fara tunani anya ba Sagirun nan ya gani ba kuwa? Ba kuwa zai sanar da Yaya Ƙarami ba? Amma idan ya sanar da Yaya Ƙarami kuma yasan bincike zai fara, kawai ya san abinda zai yi, ganin ya sami mafita yasa shi jingina da kujera ya lumshe ido, sai kuma tunanin su Jiddah ya zo masa akai-akai yana sakin murmurshi har suka ƙara so gida, sai da yayi Sallahn la'asar sannan ya shiga cikin gida suna main parlour yau ba su fita ba, saboda sanyin da aka ɗan fara duk da be shigo sosai ba. Sai da yaje ya ɗauko grapes sannan ya zo ya gaida su ya  zauna a kusa da Abba suna hira sama-sama.

Inna tace, "Ku bani hankalin ku nan?

Jin haka yasa su Mama tashi zasu tafi ita da Ummi tare da Anty da suke neman turawa.

Tace, "Ai maganar harda ku".

Ba musu suka dawo suka zauna.

Tace, "Aure ne nake so a haɗa da Sajad da Bintu".

"Aure?

Kowa ya maimaita na wurin don su dukan su anan suka sauƙa babu wanda be ji mamaki ba, sai su Abba da Baba, ita kuwa Bintu kallan sa kawai take ji me zai ce?

Sajjad yace, "Aure kuma?

Tace, "Aure na gaji da zaman ka ace babu aure..."

"To akan ki nake zaune?

Ya bada kai tsaye babu wani dar ko shamaki a tattare da shi, banda zuciyar sa dake wani irin bugu na tashin hankali, kowa na parlourn kallan sa yake da mamaki dan babu wanda yasan Sajjad da rashin kunya ko makamancin haka( irin wannan mamakin ma sai ka ga kowa ya kasa magana, to hakan ne ya faru da wannan ahali) ganin sun yi shiru yasa shi cewa.

"Ni ƙaramin yaro ne? Ko bansan ciwon kai ne ba? 

"Sajjad".

Ya faɗa da mamaki a fuskar sa, Sajjd kuwa ƙara ɗaure fuska yayi tare da mai kan sa wurin TV kamar yana kalla tvn nan be kuma kallan kowa, yayin da kowa shi ya maida TV.

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now