30

66 0 0
                                    

Koda aka wurin meeting ɗin bata shigo ba har suka fara aka dawo kan su shiru, yayin da Sajjad yayi ta kallan ƙofa yaga ko zata shigo amma shiru bata shigo ba, be kuma dena kallan ƙofar gashi ana jiran su, suyi magana amma ko kallan mai masa maganar be yi ba da zimmar wai zai yi magana. Yayin da ita kuwa Nilah a nata ɓangaren research ɗin abinda suke yi ta ke yi taga akan me ake maganar ma, ita ba kasuwanci ta iya ba, ba komai ba, amma ya zo yace wai ita ce zatayi magana, to tace me? Tana cikin binciken nan har bata san an dawo ba, sai da ta duba taga lokaci ya kusa har da kusan minti talatin da hanzari ta tashi, ya nufi wurin meeting ɗin.

A hankali ta tura ƙofar suka haɗa ido ya sakar wani irin kallon da bata san shi ba, gashi de, harara za'a kira shi ko kuma gargaɗi shi de ya sani, ta ƙaraso ta nemi waje ta zauna. Ganin kowa yayi shiru aka tambaye ta ko tana da abin cewa, batare da tace komai ba, ta tashi ta nufi ɗan board dake gaban su tare da ɗaukan marker tayi zane tayi rubutu, kallan ta kowa yake yi, yayin da ita kuma gaban ta yake faɗuwa dan tabbas batasan ya zata juyo ba ta fara gudanarwa da wannan abun da take yi, tas ta gama abinda take so kafin ta juyo ta kalle shi, kallan irin what next.

Cikin wata irin murya ta fara gabatar da abinda ta rubuta daki-daki, batare da wani bayani ba sosai, tana de yi har ta gama sannan ta sami waje ta koma wurin zaman ta, tambayar da wani Bature yayi mata ne yasa ta kallan shi, ganin bata da amsar tambayar da yayi mata yasa shi cewa wai ba za su karɓi wannan shirmen da tayi ba, sai a lokacin Sajjad ya tashi, ya ƙara bayani akan wanda tayi fiye da wanda tayi, ganin kowa yayi shiru ana ji jina kai alamar gamsuwa yace, tunda kowa ya gane abinda ake nufi companyn da suka zo sai sun bashi kaso mai tsoka kafin ya aiwatar da nufin sa gare su, muddin sukayi hakan, shi kuma zai aiwatar musu su gane, idan kuma ba su bashi ba, companyn sa ne zai cigaba, kuma ya danne na su. Ganin sun fara kallan-kallan alamar neman shawara ya tashi kawai ya fice, a wurin batare da ya ƙara bi ta kan su ba.

Ganin haka yasa ta kwasar masa jotter ɗin taga yayi rubutu da kuma biron sa, ta bi bayan sa a wurin mota ta gan shi yana waya, sai da ya gama.

Tace, "Meye hakan kayi? Idan aka zo aka sami matsala kuma ya zakayi da kuɗin da ka karɓa?

Wani shegen murmurshi yayi.

Yace, "Ai kece kika fara bani ba, ni kawai nawa ƙarashe ne".

"Ni kuma? Ni me nace?

"Tambaya na kike?

Rufe idan ta tayi ta buɗe tare da sakin numfashi alamar fara gajiyawa da zancen nan, yayin da shi kuma ya kafe ta da ido.

Tace, "Kada ka karɓi kuɗin nan dan Allah".

"To Anty".

Ya faɗa yana shigewa mota ya bar ta a tsaye tana kallan sa. Glass ɗin motar ya sauke.

Yace, "Hajiya ke nake jira".

Haɗa rai tayi taje ta shiga motar ta ɗayan side ɗin.

"Ka gane abinda nake so ka fahimta".

"Baiwar Allah idan na nayi asara mene naki a ciki ne wai? Ba ke kika so ayi asarar ba?

"Ni kuma?

"Idan na ƙara Magana kika kuma cemin ke kuma Allah ranki sai ya ɓaci, baki da aiki daga an miki magana. Ni kuma".

Ya faɗa cike da faɗa da takaici irin abun ya dame shi ɗin na. Harda su ƙwafa daga ƙarshe, taɓe baki tayi bata kuma cewa komai ba, har suka zo wani companyn ɗan ƙarami ne amma kuma tsaruwar sa tafi komai burgeta, tun daga wurin ƙofar tagane cewar wannan wurin shuke-shuke ne, sai da ta karanta wurin kuma taga 'NAH farm Garden' ita kadai kawai ta fara murmurshi ta cikin face mask ɗin ta, har wani leƙowa take yi tana gani abin ba ƙaramin burgeta yayi ba.

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now