PROLOGUE

907 40 2
                                    

Kaddara!
Mece ce ita?
Yaya rayuwar yarinya mai karancin shekaru za ta kasance a lokacin da ta tsinci kanta cikin mummunar kaddara, irin kaddarar da ba ta da saukin runguma?
Shin dukkanin mutane ne ke jingine mafarkai da burikansu, su sadaukar da duk wani farincikinsu domin aminnansu?

Da yawan mutane sun san kalmar 'Sadaukarwa' sai dai mafi rinjayen mutane ba su san mene ne ainahin ma'anarta ba.

Sadaukarwa na kunshe da abubuwa mabambanta, kamar yadda ma'anarta ke kunshe da tarin kalmomin da fadarsu kadai zai sanya zubar hawayen dubban mutane.

Akwai rayuwar da ba ta taba yin tasiri idan babu sadaukarwa a cikinta.
Shin wace irin rayuwa ce wannan?

Abokiya, kawa, ko kuma dai aminiya.
Idan har aminci ya yi aminci, to sadaukarwa ce gaba da komai.
A mataki na aminci, idan har babu sadaukarwa to akwai babban nakasu.
Aminci ba zai taba cika ba idan babu sadaukarwa a cikinsa.
Kawaye biyu na iya rayuwa ta tsayin shekaru ba tare da wasu sun taba hasashen babu alakar jini a tsakaninsu ba, matukar suka kasance masu SADAUKARWA.
Rayuwa na tafiya ne bisa tsarin Ubangiji, Ubanigijin da Ya halicci so da k'i. Wanda Ya halatta sadaukarwa ya kuma haramta cin amana.

Rayuwar aminnai biyu ba za ta taba tafiya daidai ba idan babu SADAUKARWA.
Aminiya ta gaskiya ita ce wadda za ta iya jingine duk wani tsaruka da burika nata domin farincikin aminiyarta.
Aminiyar kwarai tana aikata komai matukar bai saba wa mahaliccinta ba, domin inganta aminci.
A takaice dai, SADAUKARWA ita ce aminci.

Babban burin Khayri shi ne ta ga ranar da burinsu ita da babbar aminiyarta Ummu zai cika na ganin sun zama likitoci, kamar yadda ya zama babban mafarkinsu tun kuruciya.

Sai dai, ba koyaushe ba ne burin mutum yake cika, ba koyaushe ne mutum yake samun abin da yake so ba.
Hausawa suka ce wai kana naka Allah na naShi, kuma naShin shi ne na gaskiya.

Wani yana yankar zaren kaddararsa dogo, sannan kyakkyawa; yayin da wani ke yanko nashi gajere, sannan ba mai kyau ba sosai kamar yadda yake buri.

Ba matsalarta ce kadai ta dauka matsala ba, har matsalar aminiyarta ta mayar da ita tata, yayin da ta ci alwashin daukar fansa , ta ajiye burinta a gefe.

Ku biyo ni a cikin labarin Ummulkhairi da Ummulkhairi, kawaye, aminnan juna, masu suna iri daya, sannan masu mafarki iri daya, wadanda kaddara ta sauya musu dukkan mafarkansu.

Kar ku manta, dare dubu na barawo, yayin da daya tak yake kasancewa na mai kaya.

DARE DUBUWhere stories live. Discover now