Page 46- Barrista Khairi

147 20 0
                                    

Page 46

Cike da soyayya da kauna muka ci gaba da rainon Ummunmu. Haidar irin mazan nan ne masu kula, ko sau daya bai taba runtsawa ba matukar ni da Ummu ba mu runtsa ba. Ita kuwa sai ta zabi tashin dare, ba ta bacci sai wuraren ukun dare ko hudu. Da safe kuwa ta sha baccinta har rana.
Haka muke lalacewa kanta ni da shi har wani lokacin ma shi ke daukar ta ya yi ta rirriga har sai ta yi bacci.
Ana cikin haka hutunmu na makaranta ya kare, dole Mami ta samo mana nanny, sunanta Kuluwa, saboda ba zan iya ba da renon Ummu tare da karatu.
A makarantar ma wasu lokutan zuwa yake yi ya duba mu, musamman idan muna da evening lectures.

A hankali Ummu ta fara gyagijewa, ta yi gubul-gubul da ita, ga fara'a, sannan farar fata tas, sumar kanta a kwance luf irin ta mahaifinta. Kowa sha'awar Ummu yake yi tun daga kan malamai har zuwa dalibai.
Wata irin shakuwa ke tsakaninta da mahaifinta, idan zai fita dole ne sai an boye ta, kuma da zarar ta ankara ba ya nan ta dasa kuka kenan, da kyar za a shawo kanta ta yi shiru.

Rayuwa ta ci gaba da tafiya, har zuwa lokacin da na samu wani cikin, a lokacin shekarar Ummu biyu, muna shekara ta karshe a makaranta. Wannan cikin sam ban sha wahala ba kamar wancan. Kasantuwar nanny din Ummu na nan ya sa ban ce Nusaiba ta zo ba.
Muna cikin jarabawar first semester ta final year, na haifi kyakkyawar 'yata mai kama da Ummu sak, har kalar fatarsu da idanuwan da suka dauko na mahaifinsu. An sha shagali sosai kamar na haihuwar farko, Haidar na tsananin kaunar yaransa, sannan ni ma babu abin da ya ragu na daga soyayyar da yake yi min. A take ya yi mata huduba da sunan Mami, Radiya. Su Nusaiba suka zabar mata Afreen a matsayin alkunyarta.

Afreen na da wata shida muka kammala makaranta. Gagarumar walima Haidar ya hada min, inda 'yan'uwa da abokan arziki suka zo, aka ci, aka sha, aka gyagije. Wani irin farinciki nake ciki na irin ci gaba da kullum yake samun rayuwata. Hakika duk wanda ya ce kunci zai dore a rayuwar mutum ya yi karya. Idan na tuno da yadda kaddara ta yi gararamba da rayuwata sai dai kawai in yi murmushi, a wani sa'ilin kuma in yi kuka.
Ga wata irin soyayya da Mami ke gwada mana ni da yarana, tamkar ita ta haife ni.
Sadda aka tashi bikin Safra ita da kanta ta sanya Haidar daukar nauyin kayan daki. A lokacin ba karamin faranta raina ta yi ba, kasantuwar ina matukar tausayin Ummanmu, na kuma san za ta sha wahala sosai tunda ba mataimaki gare ta ba sai Allah. Ina samun kudade sosai saboda ko scholarship da ake ba mu na gwamnati ba kananan kudi ba ne. Idan na karba kuwa kusan duk ga Umma da kannena suke karewa. Ni da kaina na hada wa Safra kayan ado na kawata daki, irin su luxury interiors din nan. Kayan kitchen kuma da ma Umma duk ta gama hada kayanta. Sai kayan dakin ne muke tsaka da neman mafita, sai ga Haidar ya ce ya dauki nauyin komai shi da Maminsa, kuma ita ce ma ta kirkiro shawarar, saboda da ma can suna yi wa marayu kayan aure ita da Haidar, ko da ba su san su ba. Sai dai idan ba su ji ana nema ba.

Na ji dadi, na yi kukan farinciki tare da mika dukkanin ragamar rayuwata ga Haidar Turaki. Sannan Maminsa, Allah ne kadai zai iya biyan ta.

***

Afreen ba ta isa yaye ba amma dole na yaye ta saboda Law School da zan tafi, kuma a ka'ida ba a zuwa da yara, idan ma ba su isa yayen ba dole sai dai ka yi hakurin wata shekara. Wannan dalilin ne ya sanya Haidar ya ba ni goyon bayan yaye ta tunda ta shekara, na tafi na bar ta a hannun Umma tare da Kuluwa; nanny dinsu, da kuma taimakon Sadiya.

A lokacin da zan tafi har da kuka na yi, na shige jikin Haidar don ji na yi ba karamin kewar sa zan yi ba. Da kyar ya rarrashe ni ya kai ni Airport. Ina kuka sosai na tafi na bar shi.
Babu jimawa jirginmu ya tashi. Kabba Law School campus da ke jahar Kogi, a can ne zan yi.

Bayan mun isa na kira Haidar nake shaida masa mun sauka.
"Har na fara kewar ka wallahi Daddy."
Na fada cikin sanyin murya.
"Hmm...ke kenan ma Buttercup. To ni in ce me? Ban san yadda zan yi ba idan dare ya yi, na saba jin ki a cikin jikina."
Na yi gajerarar dariya.
"Ka dauki pillow dina, ka saka a jikinka za ka ji tamkar ni ce."
"Ba ki da abokin tarayya fa, babu abin da zai iya cike min gurbinki. Shekarar nan guda jin ta nake kamar shekara goma."
"Saukin ma ana visiting sweat heart, duk sadda ka samu dama sai ka dauko su Afreen ku kawo min ziyara. Ba zan iya jurar shekara guda ban gan ku ba."

DARE DUBUWhere stories live. Discover now