Page 05- Masauki

239 26 0
                                    

Page 05

Ban san me ya sake faruwa ba daga nan, kawai dai abu daya da na sani shi ne na ji kamar wani hayaki ko hoda a ido da hancina.

Tsakanin kwanaki da awanni, ban san adadin da na salwantar ba, illa dai na bude ido na gan ni yashe cikin kashi da fitsari, Ummu daga gefena ita ba ta ma farka ba. Na yi firgigit ina kokarin tuna abin da ya faru, sai dai na gagara tuna komai sai hirar nan tamu ta karshe da murmushin da Ummu ta yi min.
Cikin azama na hau jijjiga ta, sai dai tamkar mai baccin mutuwa haka ta kasance. Na sake bugunta da karfi, ta yi firgigit ta tashi zaune tana bi na da kallo, sannan ta ci gaba da kallon mataccen dakin da muke yashe, zarnin fitsari mai garwaye da wani irin hamami na ratsawa a na'urar shiga da ficen iskanmu.

Dif! Dif! Dif, haka muka dinga jin karar taku tana kusanto mu, can sai ga wani sangamemen mutum, fuskarsa duk dinke-dinke tamkar dinkakkiyar kwarya, sannan idanuwansa jajur masu ban tsoro.
Kallo na ya yi sannan ya kalli Ummu, ta yanayin kallon kawai na san cewa alkiyarmu ta tsaya!

"Ku taso ku zo, Oga yana son ganin ku."
Ya fada da kakkaurar muryarsa mai kama da duman girke.
Alamar motsi babu wacce ta yi a cikinmu, har sai da ya daka mana tsawa sannan muka mike cikin azama muka mara masa baya.

Mun yi tafiya mai dan nisa, kafin muka isa cikin wasu bukkoki, irin asalin na fulanin nan masu tafiya kiwo. Bayan mun isa cikin wata babbar bukka, mutumin nan wanda a take zuciyata ta yi masa huduba da Sangami, ya ba mu umurnin shiga. Babu musu kuwa muka afka, zuciyata sai biya salati take amma bakina ya gagara furtawa.

Kasa ya zube, cikin girmamawa ya ce
"Oga, ga sabuwar ganima nan. Sai dai a inda muka samo su, babu alamun za a samu abun kwarai."

Dariya da karfi wanda ya kira da Ogan ya yi, kafin ya murtuke fuskarsa tamkar ba shi ba ne ya gama dariya, cikin muryarsa ta Fulanin daji ya ce
"Wa yake raina kadan? Ai ko gidansu ne a sayar a biya kudin fansarsu."

Na kalli Ummu, ta kalle ni. Sai a sannan ne muka fahimci komai, kenan dai wadannan su ne ake kira da 'yan garkuwa da mutane. Kamar Ogan ya fahimci maganar zucin da nake yi, sai cewa ya yi,
"Ku 'yan gata ne idan har aka yi mana yadda muke so, babu wanda zai yi muku ko kwarzane, za ku koma gida lami lafiya."
Sannan ya sake kyakyacewa da dariya.

Dukkan gabban jikina kyarma suke yi, na kalli Ummu da jikinta ya jike sharkaf da zufa, sannan na dawo da duba na ga Ogan da ke magana da Sangami.

"Daga mafari suke yanzu?"
"Eh, Oga. Daga can na dauko su."

Da alama wurin nan da muka farka can ne suke kira da mafari. Ban gama dawowa daga tunanin da nake yi ba, na ji ya ci gaba da cewa,
"Ka umurci Zaki da ya ba su wajen kwana, sannan Lanti ta ba su duk abin da ya dace. Kar a cunkusa su cikin wadanda suka kwana biyu, don wadannan ina tsammanin an kusa aika su lahira, saboda ba zan lamunci rikonsu a nan su zame mana wani nauyi ba alhali an ki kawo kudin fansarsu."

Dariya Sangami ya yi, sannan ya juye ya kalle mu ya ce
"Ku wuce mu tafi."

Babu musu muka bi bayansa, ya kai mu can wata bukkar inda muka samu ire-irensu da yawa, wasu na zukar sigari, wasu na daga kwalba da alama ta giya ce, sannan wasu karta suke yi, kuma abun mamakin har da mata.

"Zaki."
Ya kwala kiran sa. Wanda ya kira da Zakin ya ce
"Ya dai? Mutum na tsaka da harkarsa za a nemi takura masa."

Sangami ya tsuke fuska tamau ya ce
"Oga ya ce a ba su masauki. Ke kuma Lanti, an ce ki ba su duk abin da ya dace. Sababbin kamun nan ne na shekaranjiya."

DARE DUBUWhere stories live. Discover now