Page 19- Kura Da Fatar Akuya

148 30 0
                                    

Page 19

Da dare ya yi yau kuma sai bacci ya sace ni ba tare da na yi aune ba, ballantana kuma Aysha da ta kwaso gajiya kuma da ma ita bacci gare ta sosai.
Wannan dalilin ne ya sa ba mu sani ba ko an sake fita ko kuma ba a fita ba. Sai gabanin sallar asuba na farka, a lokacin biyar saura. Na tashi na bude wasu documents da aka tura min daga Office, dukkansu wasu assignments ne da aka taba yi wadanda suke da kamanceceniya da nawa. A hankali nake dubawa na ga irin gwagwarmayar da aka sha kafin daga baya a yi nasara. Na bude wani, shi ma dai kusan hakan ne amma shi an yi failing don har ma'aikacinmu aka kashe, amma daga baya an sha gumurzu don wannan kisan shi ya balle komai aka kama duk masu laifin.
Gabana ne ya dan fadi, sai kuma na yi gaggawar gayyato wa kaina karfin hali ina tuna yadda komai ke zuwar min da sauki, duk da har yanzu babu wani takamaimai suspect tunda ban gane ko wace ce a gidan ba. Sai dai na sani tunda har akwai din, sannu a hankali zan gane ta.

***
Kwanaki suka ci gaba da tafiya har muka cinye wata daya ba tare da komai ya faru ba, duk da koyaushe cikin dari-dari muke, don Oga ya fada mana a kowanne lokaci muna iya jin an sace mu, duk da ba fatan haka muke a yanzu ba har sai mun tabbatar da suspects din namu sannan.

A makaranta muna kebe ni da Mallam Shamsu, don a tsayin lokacin nan wata irin shakuwa ce ta kullu tsakaninmu tamkar mun shekara da sanin juna. Ya fada min yana so na sai dai ban amince masa ba har yanzu jiran amsata yake yi, ni kuwa irin abun nan ne sai na gama wana shi, ta yadda ba zai ketare duk wani zabi ko umurnina ba.

Ya dube ni ya ga wayata nake latsawa, sai ya yi yunkurin fizgewa amma na yi gaggawar tamke ta tam a jikina. A take na daure fuska, don duk shirina da mutum ban yarda ya ce zai karbi wayata ba, ballantana kuma wannan da yake cikin wadanda nake zargi.
Ganin na daure fuska ya sanya shi fadin
"Ki yi hakuri idan na yi laifi."
"Kar ka sake yi min irin haka in dai kana so mu shirya. Ba na so."

Ya yi gajeren murmushi,
"To shi kenan 'yan matana, ba zan sake ba in shaa Allah. Ki yafe min."

Na jinjina kai alamun na hakura. Ya ce
"To ki yi murmushi mana."

Murmushin kuwa na yi hade da kallon shi.

"Wai ni kam har sai zuwa yaushe ne zan samu amsata? Na yi hakurin, na jira amma har yau dai ban ji komai ba. Ba ki san yadda nake ji ba ne Safina, komai zai iya faruwa idan aka wuce yau ban samu amsata ba."

Na dan sunkuyar da kaina irin alamun kunya.
"Kafin in ba ka amsa ni ma akwai alfarmar da nake nema a wurinka."
Na fada ina karantar yanayinsa.
"Aikin nan da na taba jin kana fada wa su Mallam Abu kana samun kudi da shi, nake so ni ma a dora ni a kai."

Idanuwa ya bude alamun mamaki. Na gane ya tsorata ainun da maganata, kuma da ma abin da nake so kenan. Sai na sake maimaitawa idona na kansa.
"Idan kuma ba zan samu ba shi kenan."
Da wata irin murya na fadi haka, muryar da ni kaina ban taba tsammanin ina da irinta ba.

Cikin rawar murya ya ce
"Wannan aikin namu mai wahala ne...ba za ki iya shi ba Safina, ba irin aikin da ya kamace ki ba ne."

Na yi kokarin boye mamakina na ce
"Kamar yaya ba zan iya ba? Kallon ragguwa kake yi min ko me?"

Ya gyada kai,
"Ba haka ba ne. Kawai dai..."
"Kawai dai me Shamsu? Me kake nufi?"

Sai da ya dan waiga haggu da damansa, ya tabbatar da babu kowa da zai iya jin sa sannan ya ce
"Aiki ne mai matukar hatsari, ni ma kaina a tsorace nake da shi, sam-sam babu kwanciyar hankali a cikinsa."

DARE DUBUWhere stories live. Discover now