Page 14- Assignment

164 29 0
                                    

Sakon gaisuwa gami da jinjina ga masoyan labarin Dare Dubu. Alkhairin Allah Ya iske ku har gadon baccinku. DSS UmmulKhairi na gaishe ku kyauta.

Page 14

***

Cike da nishadi nake da har muka iso garin na Katsina ma ban sani ba sai da muka tinkari tasha sannan na farga.

Janye da akwatina na karasa gida. Aikuwa sai aka hau ihu, kannena da Ummata, sannan ga Mama da ta zo shirin tarbata tunda duk sun san yau ne zan dawo.
Abinci kala biyu aka yi har da su farfesu, don ban rage su da komai ba, monthly allowance dina na shiga zan raba su gida biyu in tura wa Ummana rabi. Kullum kuwa cikin shi min albarka take don yadda nake tsaye kansu ba za ka zaci diya mace za ta iya wannan namijin kokarin ba.

Mun ci mun sha mun koshi sai aka hau hirar yaushe gamo. Ko da wasa babu wani abin da ya shafi aikina a duk cikin hirarrakin saboda wannan ya taka dokar aikin namu.

Bayan sati biyu posting dinmu ya fito kuma an bar ni nan cikin Katsina, na yi godiya ga Allah sannan na kira Oganmu na kara yi masa godiya don na san wannan kokarinsa ne.
"Kanin nan nawa da na fada miki, sunanki kawai ya karba ban ko je inda yaken ba. Zan turo miki lambarsa sai ki yi masa godiya don kokarinsa ne ba nawa ba."
"Duk da haka dai Sir, ai da ba ka yi masa maganar ba da ba zai san ni ba ballantana har ya taimaka min. Na gode kwarai Allah Ya kara girma."
"Ameen Uwata. Ya aka tarar da su Umma? Ina gaishe su duka?"
"Lafiya kalau suke yallabai. Za su ji kwarai, a gaishe da takwarata."

Muka yi sallama na isar da sakonsa ga Umma. Tashi na yi na nufi daki, a cikin manyan littattafan nan na Ummu da Mama ta ba ni, na duba wannan da marubuci Bamai Dabuwa ya rubuta na dauka. Yanzu ne daidai lokacin da zai yi min amfani. Na bude shi na hau karatu.

Tun ina jin babu dadi saboda rashin sabo, har na fara jin dadinsa, har ma aka kai gabar da ba na son ajiyewa. Irin matsalolin da suke addabar kasarmu na rashin tsaro ne, har aka kai gabar adadin jami'an tsaron da ke kasar amma duk yawansu sun kasa tabuka komai, sannan ga hanyoyin da jami'an tsaron za su iya bi wajen dakile yawaitar 'yan ta'adda a kasar.
Babban abun burgewar, daga cikin hanyoyin magancewar har da samun jami'an tsaro mata, kasantuwar akwai irin wuraren da maza ba za su iya shiga ba, amma mace za ta iya shiga har ta nakalto halayyar mutanen.
Na dad'a godiya ga Allah da wannan aiki da na samu, sannan na ci gaba da karatuna. Sosai nake samun mafita. Ko rabin karatun ban yi ba na ajiye shi saboda a washegari zan fara zuwa Office.

Washegarin kuwa na sanya bakaken kayana sannan na dora after dress na fito.
"Jami'ar tsaro har an fito?"
Umma ta tambaya tana murmushi.
"Wallahi kuwa na fito Umma. Ba na so ne na makara tunda ban san yaya yanayin wurin yake ba."
"To shi kenan, Allah Ya tsare Ya bayar da nasara."
"Amin Ummana."
Na fada hade da rataya handbag dita na fice.

***

Ko da na isa office kai tsaye na je wurin Oganmu domin yin reporting, sai dai na tarar da wasu a kofar office din, muka gaisa cikin sakewar fuska tunda duk wadanda muka yi training tare mun san juna, mun zama tamkar family. Tsayawa na yi ni ma sai ga Aysha kawata da muka fara haduwar ranar farko a Kaduna, muka rungumi juna.
"Kin ga yadda kika yi kiba."
Na fada ina dariya.
"Ke ma ai kin yi kibar. Kina ta murna za ki ga Umma, to how is she?"
"She is fine wallahi. Kawai sai ga ki a Katsina."
"Wallahi ke dai bari, ban tsammaci nan za a kawo ni ba, tunda ni gaskiya so na yi a bar ni can Jigawa jihata ko kuma Kano da muke makwaftaka."
"Babu komai Allah Ya sa hakan ne mafi alkhairi."
Na fada hade da kallon wani da ke gefena na ce
"Wai ni kam Ibrahim layin nan na mene ne haka?"

DARE DUBUWhere stories live. Discover now