Page 10- Fushin Masoyi...

180 25 0
                                    

Page 10

Umma ta hada kudade masu dan kauri ta ba ni ta ce in je kasuwar tsaitsaye inda ake sayar da wayoyi in sayi mai kyau daidai da kudina. Na yi farinciki sosai na kuma jinjina wa kokarinta don fiye da rabin jarin nata ne ta kwashe don kawai ta faranta min rai. Ni kuwa me zan yi na biya wannan baiwar Allah bisa ga jajircewarta duk da babu bango abun jingina a rayuwarta?
Ni da Safra muka je, wata Tecno karama mai kyau muka samu kuma kirar android da ban taba mafarkin samu a yanzu ba. Na sayi layi a take aka yi min rijista muka dawo gida. Ai ranar na yi nishadi irin wanda ake jimawa ba a ga na yi ba tun bayan da aka yi garkuwa da mu.

Wata kawata Salma ta kawo min ziyara take shaida min aurenta ya kusa za ta zo ta kawo min katin gayyata. Na harare ta
"Ba ki kyauta ba Salma, sai da aka kusa bikin ma sannan za ki fada min?"
"Ba haka ba ne Khairi, tun sadda aka sa ranar ba ki da lafiya ne, kuma kin ga babu dadi kina fama da jinya in zo da batun aurena. Amma ki yi hakuri in shaa Allahu ana buga kati ke ce ta farkon kawowa."

Na yi murmushi kawai ina tunanin rayuwa. Ni ko sai yaushe ne ma zan baiwa wani damar yin soyayya da ni ballanta har in yi auren? Na tuna ko wancan satin sai da wani matashi ya zo har gida ya nemi ganawa da ni amma na kore shi. Haka cikin muna jarabawa ma wani har gida ya biyo ni na masa korar kare. Ba na jin zan iya ba wani dama, dukka auren ma ba ya kaina, ba na tunanin zan yi rayuwa irin ta kowacce diya mace. Tunin duniya aka yi fatali da martabata, ni kuwa me ya yi saura a rayuwata da zan yi tinkaho da shi?
Sai kawai na ji gumi a fuskata ashe kwalla ce nake yi ban sani ba. Salma da ba ta san dawan garin ba ta tsorata da kukan nawa amma a karshe sai kawai na yi mata murmushi ina mai ba ta tabbacin wani dalilin ne can daban ya sanya ni kuka ba saboda ita ba ne.

Bayan na fita rakiyar ta ne take ce min yaushe admission dinmu zai fito?
"Ba burina in ci gaba da karatu ba Salma, ko da zan ci gaba to gaskiya ba yanzu ba. So nake in samu aikin tsaro ko ma wanne iri ne."

Ido ta zaro mamaki na bayyanuwa a fuskarta.
"Aikin tsaro kuma Khairi? Ta yaya ke da kike mace za ki yi shi? Wahala fa ake sha."
"Wahala ba ta kisa Salma, idan dai zan samu na yi alkawari zan jure. Sa kai aka ce ya fi bauta ciwo."

Ta sauke ajiyar zuciya hade da fadin
"Haka ne. Amma dai na tausaya miki wallahi."
"Babu komai fa in shaa Allahu zan iya. Ni dai burina kawai in samu."
"To yanzu jamb din taki hakura za ki yi da ita shi kenan ki yi asarar duk wannan uban makin da kika samu? Oh! Abin da mutane ke nema yau ga wata ta samu amma tana neman barin ta ta bi iska."

Na kirkiro murmushin da bai da alaka da nishadi na ce
"Ba ita nake buri ba, shi ya sa tun farko na nunar da ba na son cikewar aka tilasta ni."

Mamaki bai kau daga fuskar Salma ba ta ce
"Ai shi kenan, Allah Ya taimaka. Ki dinga dubawa ta online duk sadda za a yi daukar ma'aikata ki cika ko Allah zai sa a dace. Na ji ma an ce an bude portal na Nigerian army. Ki gwada ko Allah zai sa ki haye tunda dai abun dace ne."

Na ji dadi kwarai muka yi sallama ta fita. Ban yi shawara da kowa ba na shiga shafin Nigerian army din, na kuwa ci karo da wurin da mutum zai cike tunda a bude yake. Na cika komai a raina ina addu'ar Allah Ya sa in dace.

Ina zaune daki sai ga Safra ta shigo tana ce min wai in je Mama na kira na. Na yi mamaki kwarai don wannan din wani sabon abu ne amma dai na amsa da to na fita. Umma ba ta nan tun safe ta je sare-saren kayanta da suka ja.
Ko da na je gidan na tarar kwalema suke yi ashe, kusan komai an fitar da shi waje. Bayan na gaishe ta ta amsa min da sakin fuska, ta miko min wata leda mai makimancin girma ta ce
"Wasu daga cikin abubuwan Ummu ne wadanda ba ki da irinsu. Wannan kyauta ce daga gare ni a matsayina na uwa. Idan kuma ba za ki iya amfani da su ba ki ba Safra da Sadiya. Ko kuma ki ajiye a matsayin tarihi."

DARE DUBUWhere stories live. Discover now