Page 02- Damuwa

312 34 0
                                    

Page 02

Na so daurewa sai dai na kasa.
"Likita ki yi mini allurar mutuwa."
Na faɗa da wata irin raunanniyar murya.
"Subhanallahi! Khayri ya da haka kuma? Anya kanki guda?"
Na runtse idanuwana hawaye na sauka daga cikinsu.
"Na rasa duk wasu kawuna nawa tun daga lokacin da abu mafi daraja ya kufce mini. Kai gudan ma ba ni da shi Anti. Don Allah ki taimaka mini, ki ji ƙaina ki yi mini allurar da za ta mika ni barzahu. Sista rayuwata ba ta da sauran amfani. An illata ni illa mai girma."
"Na sani Khairi, na sani an zalunce ki. Amma kin san wani abu? So nake ki daure in kula da ke, so nake ki warke, da kanki nake so ki ƙwatar wa kanki fansa, da kanki nake so ki zama jagorar mata 'yan'uwanki."

Maganarta ta shige ni, sai dai ta yaya?
Ganin na yi shiru ya sanya ta ɗorawa da,
"Na sani da zafi da ciwo Ummulkhairi, na san kina jin raɗaɗi mara misaltuwa a zuciyarki. Sai dai kin san wani abu? Raɗaɗin da za ki zuba wa waɗanda suka keta miki haddi sai ya zarce wanda ke kike ji a yanzu. Lokaci zai zo wanda za ki yi dariya su kuma za su yi kuka da idanuwansu, a lokacin da suka gama shagalta da duniya, suka ma manta da ke da fuskarki. Za ki yi dariya, za ki zuba musu dafi a zukatansu!"

'Ta ina? Ta yaya?'
Nake tambayar zuciyata. Ban taɓa jin nadamar zuwa duniya ba sai a wannan lokacin. Tunda nake a rayuwata ban taɓa tunanin akwai ranar da mutum zai ji cewa ya tsani kansa da komai nashi ba sai yanzu da nake ganin duniya ta juye mini.

"Ki gode wa Allah Khairi. Da yawa daga cikin ire-iren matan da suka shiga cikin irin rayuwar da kike kanta a yanzu sun rasa kowa da komai nasu. Wasunsu hatta iyayen da suka kawo su duniya sun guje su. Masu aure mazaje sun rabu da su, ƙananan yara wasu sun mutu, wasu kuma an kashe su alhali da rayuwarsu. Ina mai ƙara rokonki  da ki cire tsananin damuwa daga zuciyarki. Matuƙar kina cikin wannan halin to duk yadda za mu ba ki kulawa ba za mu ga ci gaban kulawar ba. Idan har raunukanki suka warke to na cikin zuciyarki za a yi ta kwan-gaba kwan-baya ne. La'antar biri ba ta ƙara masa komai sai kaurin jela, Khairi. Damuwar ki ba za ta taɓa amfana miki komai ba, ba za ta kai ki inda nake son ki je da ƙafafuwanki ba."

Na kalli nos ɗin da ke ta ƙoƙarin ganin ta kwantar mini da hankali, sai kawai na ji ta janyo ni a jikinta ta rungume ni, na dinga sauke ajiyar zuciya tamkar wacce ta yi tseren gudu.

"Yawwa ƙanwata. Ki ci gaba da ƙarfafar zuciyarki. Na sani da nauyi sosai amma a hakan dai za ki daure. Ina jiyo ƙamshin alkhairi a rayuwarki ta gaba. Sannu a hankali komai zai zamto labari. Ki ci gaba da addu'ar neman sassauci daga wurin Ubangijin da ba Ya da tamka. Ba Ya gyangyaɗi bare barci. Yana sane da halin da kike ciki, Zai kuma tsaya miki komai daren daɗewa."

Kasa raba jikina na yi da nata. Ina jin daɗin kalaman da suke ratsowa daga tsakanin laɓɓanta. Cikin wata irin murya na ce,
"A lokacin da suke tanɗar leɓo, a lokacin ne ni kuma nake matsar idanuwa. Lokacin da suke murnar sun samu ganima, lokacin ni kuma matsar idanuwa nake. Farin cikinsu sun yi nasara a gareni, ƙuncina nasararsu gare ni. Suka yi dariya suka ce 'Mun gama da ita.' Na yi kuka na ce 'Gatana ya ƙare.' Suka miƙe da dukkanin ƙarfinsu, na kasa ɗaga ko da hannuwana. Sun gama, sun manta da duniyata, ni kuma sun buɗe mini babin ƙunci a duniyata.
Su yi aure a duk sadda suka so.
Su yi aure da mutuncinsu.
Su yi rayuwa mai kyau da iyalinsu.
Su ci gaba da cin duniyarsu da tsinke.
Ni ga ni nan sun zuba mini dafi a zuciya, sun bar ni da rauni mai wahalar warkewa."
Na sake dubar yadda ta ƙanƙame ni, ina jin ruwan hawayenta yana ratsa tufafina, sai dai ɓoyewa take yi, ta dake, ba ta son in fahimci raunin da kalamaina suka saka ta, ba ta son ta dakusar da ɗan sauran ƙwarin guiwata. Na ci gaba da cewa,
"Anti ko kin san halin da ire-irena suke shiga?"
"Na sani mana Ummulkhairi."
Ta yi gaggawar ba ni amsa.
Sai na gyaɗa mata kai. A hankali na ce,
"Ba duka kika sani ba shi ya sa kike tunanin komai zai iya gushewa.
Ta yi aure ta fuskanci tsangwama da kyara.
Ta rabu da mijinta saboda rashin budurcinta.
Ta dawo gida ana kiran ta da bazawara.
Ta fuskanci kyara daga dukkan kowa.
Ta yi kuka, ta shiga damuwa, ta nemi agaji babu, ' 'yar iska' shi ne sunanta a duk ta inda za ta gitta. Daga nan sai ciwon zuciya, sai cutar hawan jini, za ta rame, za ta zube, za ta lalace, dariya za ta yi mata ƙaura, murmushi sai dai na takaici. Za ta rasa madafa, za ta rasa agaji, manemi ma za ta rasa shi. Daga nan sai a hantare ta a gidansu saboda rashin aure. Za su gaji da ganin ta, za su gaji da ciyar da ita. Idan ta samu jari ta fara sana'a za ta rasa masu saye. A ƙarshe jarin zai karye, sai talauci ya yi mata kamun kazar kuku.
Daga nan sai me zai faru kuma?"
Na sharce hawayena, muryata na sake karyewa amma a haka na dake, na ci gaba da faɗin,
"Haka ake salwanta rayuwarmu. Haka ake mayar da mu marassa amfani. Mu yi shigar banza a keta mana haddi, mu yi shigar kirki ma ba mu tsira ba. Ƙaramar yarinya ma a haiƙe mata. Hatta jaririyar da ba ta san komai ba haiƙe mata ake, babu tausayi babu imani. A shigi mace ta ƙarfi da yaji. A haiƙe mata cikin zalunci. A dasa musu cuta; ta zuciya da ta gangar jiki."
A tsayin wannan lokacin sosai kukan nos ɗin ya bayyana, jikinta har karkarwa yake yi. Da alama kalamaina shigar ta suke yi, sai na ƙara tabbatar da duk abin da take faɗi kawai tana faɗi ne don ta kwantar mini da hankali, ba wai don tana da tabbacin zai yiwu ba. Ni da ma tuni na sani, na san cewa farin cikina ya ƙare shi ya sa nake ta fatan mutuwa ta zo ta ɗauke ni. Dan sauki na daya shi ne da aka ba ni tabbacin ita Ummu da sauki sosai har ma ta farfado.

Sai da ta share hawayenta sannan ta raba jikinta da nawa. Ta ƙirƙiro murmushin da iyakarsa bisa leɓonta. Da farin hijabinta ta hau share mini nawa hawayen.
"Duk abin da kika faɗa gaskiya ne Ummulkhairi. Sai dai ki sani ba a kan kowa ba ne hakan za ta faru. Idan kowa ya guji Mero, to ke sunanki Ummulkhair, ba lallai ba ne kowa ya guje ki. Idan Kande ta rasa mijin aure, ke sunanki Khairi, kina iya samun ingantaccen miji wanda zai ba ki dukkanin gata. Idan Sahu ta rasa farin cikinta, ke sunanki Ummulkhairi. Mahaifiyarki ga ta nan tana so da ƙaunarki. Ƙannenki kuka suke tunda aka kawo ki asibitin nan, alamun suna tare da ke duk wuya duk runtsi. Sannan ga ni, duk da ba ni da alaƙa da ke ta jini, ban taɓa sanin wanzuwar ki ba doron duniya sai zuwan ki asibitin nan amma ina tare da ke. Ba zan guje ki ba, zan kuma tallafi rayuwarki daidai iyawata."

Na ɗaga kaina na kalli Ummata da ke zaune tana shartar hawaye, sannan na kalli ƙannena da ke kuka bilhaƙƙi. Na dawo da duba na ga nos ɗin da ke ƙoƙarin ba ni ƙwarin guiwa, sai kawai na ji kamar ana sace tayar da ke cike fam da iska, zuciyata tana ƙanƙancewa daga cikar da ta yi da ɓacin rai da damuwa, wani irin yanayi na maye gurbin damuwar, wanda ba zan iya cewa ga shi ba.
"Na gode sosai Anti Maryam."
Na furta ina yi wa nos ɗin murmushin yaƙe.
Ta ɗan bubbuga bayana tana murmushin ita ma.
"Allah Ya ba ki lafiya Ummulkhairi. In shaa Allahu za ki zama abar alfahari ga dukkan kowa."

Umma ma murmushin ta yi ganin yadda nos ta ƙoƙarta shawo kaina, sai kawai ta matso inda nake ta rungume ni tana sauke ajiyar zuciya.

"Umma ki kira min Ummu a waya, ki hada mu. Zuciyata sai bugawa take tare da tashin hankalin rashin jin ta. Ki kira ki fada mata idan za ta iya zuwa ta zo, sai a kama mata wancan gadon. Ina son ganin ta, ina son jin yaya nata jikin. Duk da takamaimai ban san me ya same ta bayan tafiyarta ba."

Ina kallon yadda fuskar Umma ta sauya, sai dai na rasa gane dalilin da ya sanya ta sauyawar, dazu ma da na yi zancen Ummu sai da makamancin hakan ya faru, yanzu ma kuma ga shi.
Sai zuciyata ta hau cunkushewa, ina son hasashen wani abu amma ta kasa ba ni hadin kai.

"Don Allah Umma. Idan kuma hakan ba zai samu ba, ki je ki dubo min ita, ki hada ni da ita a wayarki, ban san yadda aka yi ba nake jin wani abu mai kama da tashin hankali a kanta. Umma ko kuma ni a mayar da ni inda take, zan fi samun kwanciyar hankali."

Sai Umma ta yi murmushi, ta kama hannuna ta ce,
"Na fada miki, Ummu ta ji sauki sosai, ta ma fi ki lafiya  fa. Kawai matsalar likitoci ne ba za su bari a hada ku wuri guda ba, musamman ke da kike da danyen rauni. Amma da zarar kin samu sauki ni da kaina zan je in taho da ita, zan kawo ta gare ki."

"Umma kin min alkawari?"
Ta jinjina kai, sai ni ma na jinjina nawa kan, ina jin sosai na matsu in ji saukin nan, ko zan ga aminiyata, rabin jikina.



Amrah A Mashi❤️

DARE DUBUWhere stories live. Discover now