Page 18- Tarko

150 29 0
                                    

Page 18

Da alama aikin da na zo yi ba shi kadai zan yi ba kafin in tafi, duk da ba anti corruption nake aiki ba amma ina da damar da zan fitar da ire-iren wadannan malaman makarantar wadanda ba su san muhimmancin aikinsu ba.

"Zauna mana, ga kujera sai tsayuwa kike."
Ya furta yana nuna min wata rubabbuyar kujera, kallon kujerar na yi da kyau, ina ma iya zamewa in fadi in dai na ba ta karfi. Na gyada masa kai.
"A'a na gode kawai ba sai na zauna ba. Zan tafi wancan office din idan an yanke ajin da zan koyar sai a kira ni."
Daga haka na kama gabana, zuciyata cike da takaicin mutumin, don da alama kwata-kwata ba mutumin arziki ba ne saboda yanayin kallon da yake bi na da shi ba irin na mutanen kirki ba ne.

Dayan Office din na shiga, na tarar da malamai biyu zaune suna cin gyada. Dukkansu babu wata alama wacce za ta alamta cewa su malamai ne. Da sallama na shiga sannan na gaishe su suka amsa.
"Sunana Safina Ibrahim, kamar yadda kuka gani, ni 'yar bautar kasa ce, an turo ni ne daga garin Katsina. Ina fatan za ku ba ni hadin kai wajen aiwatar da abin da ya kawo ni, har zuwa lokacin da zan kammala in tafi."

Dayan wanda da alama ya fi kirki, ya dube ni ya ce
"Barkanki da zuwa kauyen Kanya. Allah Ya sa ki gama lafiya ki tafi cikin aminci."

Dayan kuwa dariya ya kwashe da ita, ya ce
"Ai gara da ka yi mata wannan addu'ar, duk da ba lallai din ta koma lafiyar da ka yi mata fata ba."

Kwarai na gane inda ya dosa, amma sai na yi gaggawar tambayarsa,
"Mallam, me kake nufi da wannan maganar?"

Ya kara kwashewa da dariya.
"Kar dai ki ce min ba ki san halin da kauyen nan yake ciki ba? Tabdijam! Ai mu kanmu da muke cikinsa ba tsira muka yi ba, koyaushe cikin fargaba muke. To ballantana kuma ke da kika zo daga birni, jikinki ga shi nan alaman hutu ya zauna."

Na sauke ajiyar zuciya sannan na zaro hankacif daga cikin jakar goyona na hau goge kujerar da zan zauna a kai, da alama wadda suka zauna din ma haka take tunda Monday ce yau, hutun karshen mako aka dawo. Amma ko a jikinsu, su ma jikin nasu kurar ce ai.

Bayan na gama kakkabewa na zauna, na fiddo katon littafina na Bamai Dabuwa na ci gaba da karantawa daga inda na tsaya.

***
Ko da aka tashi aiki sai da na tsaya wurin network na yi magana da Oganninmu na wajen aiki, sannan na kira Aysha ma da na tsinci text dinta a kan batun zuwan ta kauyen. Mun yi magana sosai na kara yi mata bayanin irin tashin hankalin da ke ciki, da kuma tsarin da nake son mu bi idan ta zo.
Sai da na gama duka sannan na shiga cikin gida. A yanzu din ma ina zuwa sai ga kwanon silver cike da fura damammiya. Duk so na da fura haka na dangana, ina ji ina gani sai dai na sha lemo da biscuit, furar kuwa su Farida na ba na ce su shanye a wurin don ma kar su fita da ita labari ya isar wa maigari cewa ban sha ba, tunda na sani babu dadi a ce yana bakin kokarinsa na kawo min abinci amma ban taba ci ko sha ba.

Da dare ya yi na baza ido da kunne ko zan kara jin motsin nan za a fita amma shiru, har karfe uku, har hudu ta yi sai na cire rai kawai na kwanta da zummar bacci ya dauke ni amma shiru kake ji, ban ji motsin ba tunda ban yi bacci ba har sai bayan sallar asuba ya dauke ni, kuma karfe bakwai na safe na farka.
Yau ma kamar jiya, bayan na yi wanka na fice zuwa wurin aikina, amma sai da na kira Oga na fada masa update, daga nan ya ba ni tabbacin Aysha na nan ta taho tun da sassafe, ya san ba da jimawa ba za ta iso.
Na ji matukar dadi saboda ko ba komai zan samu kawar hira, kawar shawara kuma. Kodayke dole mu yi taka-tsan-tsan don nan din ba wurin da ya kamata mu yi shawarwari ba ne.

DARE DUBUWhere stories live. Discover now