Page 50- Luck

114 25 1
                                    

Page 50

Raina a dagule na koma gida. Haidar ya dinga kokarin kwantar min da hankali amma ko kadan hankalin nawa bai kwanta ba. Idan har ban samu hujjojin da zan mika wa kotu ba na tabbata next zaman da za a yi alkali zai yi watsi da shari'ar tunda ban tanadi komai ba.
Ganin yadda na gaza samun nutsuwa ya sanya shi fadin,

"Ni dai ina da shawara guda daya. Ban san ko za ta yi amfani ba."
Na dube shi a sanyaye na ce,
"Go ahead Daddy. It might help ai, ba a san inda rana ke faduwa ba."

Idanuwansa a cikin nawa ya ce,
"Ko zuwa gobe da yamma idan kin taso daga aiki, kina iya zuwa ki dauki Hannatun, ku je ta raka ki har inda abun ya faru, next village daga wurin za ku tsaya. Watakila za ku ga kauyawan nan da ta ce sun gani."

Na gyada kai, cikin damuwa na ce,
"Ta ce ko ta gan su ba za ta iya gane su ba ai."

Ya dan yi shiru jim, kafin ya ce,
"Ni a gani na sai dai idan ba ta gan su ba din. Da ta gan su kina iya ganin ta gane. Idan ma ita ba ta gane su ba ai su sun san ta ko? Za su iya gane ta, ina kyautata zaton idan sun gane ta din za su taimaka wajen zuwa kotu su bayar da shaida."

Wannan ma shawara ce mai kyau. Na kama hannunsa, fuskata dauke da fara'a na ce,
"Thanks for this idea my darling husband. Tabbas hakan za a yi. Sai dai kuma ka san kauyawa da tsoro fa."
Ya ce,
"Tun da har suka taimaka suka dauke ta a cikin mawuyancin hali suka kai asibiti, duk da tsoron da aka san bakauyen mutum da shi, ina tunanin a yanzu ma za su taimaka din."

Na jinjina kai.
"Haka ne. Amma tare ya kamata mu yi tafiyar nan da kai, ba zai yiwu mu kadai mata mu tafi ba. Ka ga ko ba komai mu tafi tare da jami'in tsaro ai ya fi ko?"

Murmushi ya yi ya ce,
"Matsoraciya. Ke dai kawai ki ce kina jin tsoron kar a kama ku a cikin daji."
Murmushin na yi ni ma na kai masa dukan wasa,
"Ba wani tsoro fa. Tsaro ne kawai."
Ya daga kai.
"Haka ne. Amma tare da abokin aikinki ya kamata mu tafi, idan suka gan mu da dan yawa za su fi sauraren mu."
"E kuma fa. Goben da safe muna isa zan fada masa. Ba ma zan fita da motata ba sai ka sauke ni wurin aikin. Za mu jira ka idan mun gama."
Da wannan shawarar na kwana cikin raina tare da fatan za ta yi aiki.

Washegari muka tafi, Hannatun ita ke gwada mana hanyar da mai napep ya shiga da ita, har zuwa daidai wurin da komai ya faru. Sai da na dauki hoton tsarin wurin, da jikin katangar da ke zagaye da poly inda suka manna ta. Sannan muka wuce.

Mun yi tafiya mai nisa kafin muka isa wani kauye. Da yara muka fara cin karo sun yi tsaitsaye sai kallon motarmu suke.
Barrista Fa'iz ya ce wa Haidar
"Allah dai Ya sa kar mu tsorata su ma. Ka ga yadda suke bin mu da kallo sai ka ce ba su taba ganin mota ba."
Dariya Haidar ma ya yi muka ci gaba da tafiya har zuwa inda gidaje suke. Kauyen bai da wani girma amma sai yawan jama'a, mun fahimci hakan ne daga yanayin yawan yaran da ke yawo ko'ina.

"To wai yanzu ta ina za mu fara ma? Ni dai wallahi kaina a cikin duhu yake."
Na fada ina kallon Haidar ta cikin mirror, da yake bayansa nake, Fa'iz ne a gaba kusa da shi.

"Ku da kuke barristers ma ba ku sani ba sai ni ne zan sani?"
"Sai ka sani mana Daddy. Kai fa jami'in tsaro ne."
Ya ce
"To amma kuma ai ba zan yi amfani da shi ba a yanzu. Don ina nunan musu da haka ba za su yarda su bi mu ba wallahi, duk yadda zan yi da su kuwa."

Barrista Fa'iz ne ya ce,
"Ina da idea guda daya. Allah dai Ya sa ta haifar mana da d'a mai ido."

Haidar ya dube shi ya ce,
"What? Allah dai Ya sa ba kana planning mu bi gida-gida ba ne. Sunan wani gwamna."
Duk muka sa dariya.
Ya ce,
"Ba haka ba ne. Gidan mai gari dai ya kamata mu nema, mu fada masa gaskiyar abin da ya kawo mu, watakila ya fahimci manufarmu."
"Ta yaya kenan? Kana tunanin daga mun fadi haka shi kenan kuma sai a same su?"
Na gaggauta tambayar sa.
"A'a. Ina tunanin watakila idan mun shaida masa ranar da abun ya faru, a yi shela ana neman magidanta, daga nan idan an dace shi kenan."

DARE DUBUWhere stories live. Discover now