Page 09- Dream

181 24 0
                                    

Page 09

Ina kwance na ji Umma na kwala kiran Safra a kan ta zo za ta aike ta bakin hanya. Caraf na fito ina fadin
"Umma ki aike ni, na gaji da zaman gidan nan."

Ta dube ni da sauran 'yar kwalla a idona ta ce
"Ba na son aiken ki a cikin wannan halin Khairi. Duka ma ba na son fitan ki daga gidan nan har sai kin gama wartsakewa kin dawo daidai."
"Babu abin da zai faru Umma in shaa Allah. Zaman gidan nan ba ya min dadi ne babu abun yi."

Ta jinjina kai sannan ta miko min kudi.
"Ga shi ki je shagon Rabilu ki sayo min sabulun wanka da na wanki. Sannan ki biya gidan Hassana ki ce ta ba ni kudin nan idan sun samu."

Na karbi kudin sannan na fita tana min fatan dawowa lafiya.

Lafiya lau na isa shagon Rabilu, bayan na fito, a kokarina na in tsallaka titi ban san me ya hau kaina ba, ban duba haggu da dama ba kawai na afka wa titin tamkar dai zan shiga dakina na kwana, sai kuwa ji na yi kiiiiiii! Da karfin gaske an taka burki yayin da na fadi kasa dabas, zuciyata sai bugawa take da wani irin karfi.

Cikin hanzari wanda ke jan motar ya fito, a maimakon ya tambaye ni ya nake ko kuma duba yanayina, sai kawai ya hau ni da fada.
"Ke wace irin dabbar yarinya ce da za ki tsallako titi ba tare da kin duba ba? Ke makauniya ce ko kuwa mahaukaciya? Wannan ma ai kidahumanci ne!"

Ban san sadda na saki kuka mai zafi ba, tabbas ni ce ba ni da gaskiya tunda ya kamata a ce na duba titin amma ban duba ba. To kuma tunda mai afkuwa ta riga ta afku ba sai ya yi hakuri ya kyale ni ba? Kokarin mikewa na yi na kasa, sai a sannan na duba yadda guiwata duk ta guggurje. Kafin ka ce kwabo wurin har ya dauki mutane. Mutumin bai fasa yi min masifa ba har sai da wani dattijo ya hau ba shi hakuri.
Jin ya yi shiru ya sanya ni daga kaina na dube shi, a cikin sakanni goma na gane dalilinsa na wannan masifar, irin wadanda kudi suka bayyana a jikinsu ne, kyakkyawa kamar mijin novel, wadanda nake yawan ba Ummu labarinsu ina dariya tare da karyata wanzuwarsu a duniya, don a gani na babu irinsu a zahirin sai dai a duniyar kirkira. Sajensa kwance yake luf-luf, idanuwansa da kansu suke lumshewa, sai kawai ya yi mini yanayi da Mayank, jarumin Sapne Suhane, sai dai bambanci, fuskar Mayank annuri gare ta, yayin da ta wannan take turbude kamar ma bai san wani abu wai shi annuri ba.

"Kun gani ba! Ai na fada muku ba ta da hankali, ga shi nan kuna mata magana amma ba ta ma san kuna yi ba."
Maganar mijin novel ce ta dawo da ni daga tunanin da nake yi. Can na ji wani mutumi ya ce
"Sai an yi mata uzuri bawan Allah. Watanta hudu cif a hannun masu garkuwa da mutane. Ba ta fi wata biyar ba da dawowa, kuma sun sha zarya asibitin masu hankali (yana nufin asibitin marassa hankali)."

Kallon mutumin na yi ina jin takaicin yadda yake neman kira na da mahaukaciya, sai na ji hawayen da suka zarce na farkon suna fitowa, sai mutumin da ya kade nin ya gyada kansa kawai hade da barin wurin. Na ji kamar in tashi in shake wuyansa don tsabar takaici amma sai na kyale shi kawai, na dafa a hankali na mike ina dangyashi na nufi gida.

Ko sallama ban yi ba na afka gidan ina kuka. Ganin yadda duk jikina ya gurje ya sanya Umma saurin tarba ta tana tambaya ta abin da ya faru.

"Mota ta yi kusan kade ni Umma, amma da sauki bai taba ni ba, faduwar da na yi ce ta janyo gurjewar nan ma."

A take yanayin Umma ya sauya, cike da tashin hankali ta ce
"Sai da na hana ki fitan nan Khairi amma kika nace kina so. Ni da ma ko kadan hankalina bai kwanta da fitarki a wannan halin ba. Watakila ma kina can kina tunanin banza kika tsallaka titin ba tare da kin duba ba."
Tana magana tana sharce kwalla. Ni dai shiru kawai na yi ina kokarin nufar kitchen.
"Me kuma za ki yi a can?"
"Gishiri zan diba in barbada a ciwon."
Na ba ta amsa ina dan cije lebe.

DARE DUBUWhere stories live. Discover now