Page 26- Arrest

143 26 0
                                    

Page 26

Cikin sanyin murya yake rarrashina, yana kokarin kwantar min da hankali amma ban yi shirun ba har sai da na yi mai isa ta sannan na tsagaita.
Jin na yi shiru ya sanya shi fadin
"Ki kwantar da hankalinki Khairi, ki fada min abin da ya faru. Ko ba ki da lafiya ne? Akwai wani abu da ya kamata in sani?"
Cikin rawar murya na shaida masa komai, tun hirar mu da Shamsu har zuwa kiran sa da aka yi da labarin mutuwarsa.

Ina jin yadda ya sauke nannauyar ajiyar zuciya, ya ce
"Yanzu Khairi duk wannan uban kukan da kike na mutuwar Shamsu ne? To idan kuma labarin tawa mutuwar kika ji wane irin kuka za ki yi?"
Na yi shiru ina sauraren sa.

"Ya isa haka kin ji. Mutumin nan fa da ma he deserves it. Don ko ba su kashe shi ba soyayyar da yake yi miki ba za ta hana mu kama shi a hukunta shi a kan laifinsa ba. Kin ga kenan sun taimaka masa da suka kashe shi ai ko?"

Ban taba jin takaicin kalaman Oga Ahmad ba irin wannan lokacin. Duk da ba son Shamsu nake ba, ban taba jin soyayyarsa ba ko sau daya ba amma ba na kin sa, musamman da na ji tarihin mafarin fara aiki da su.
Ba tare da na ce komai ba na yanke kiran. Ina kallo yana ci gaba da kira amma na ki dauka. A karshe ma barin wurin na yi na koma gida ina jin zuciyata babu dadi.

Mutuwar Shamsu na daga cikin abubuwan da har in koma ga mahaliccina ba zan manta da su ba, saboda kamar abun ya zo ne baghtatan ba zato ba tsammani.
Daren ranar haka na kwana ban runtsa ba sai tunanin duniya, tunanin Ummu da ta tafi ta bar ni, don da a ce tana nan tare da ni, da yanzu ta rarrashe ni, da ta dora fuskata a saman kafadarta ta yi ta ba ni baki har sai sadda na samu sassauci. Sai dai tuni mutuwa ta yi mana yankan kauna, ta dauke min Ummu ba tare da noticing ba.

Washegari da sassafe ko karyawa ban yi ba sai ga kira ya shigo ta cellular phone dita ta Office, kai tsaye na gane daga wurin aiki ne, official call. Sai da na dudduba babu kowa ko a kusa da dakin sannan na dauka,
"Sagir is on the way, Sagir and Usman. Za ku yi arresting matar gidan nan, sannan za ta kai ku inda sauran informers din garin suke. Make sure everything goes smoothly. Mu ma muna hanyan shiga daji ne."
"But Sir...?"
"Na sani, you are not supposed to arrest them tunda silent assignment ne aikinki. But you have to. Tunda hakan ya kama ne, idan kika riga kika tafi tunda matar nan ta san ko ke wace ce, za ta iya guduwa ko kuma ta kawo wani dalili da zai bata mana aiki. So ki yi hakan kawai. Just arrest her, ki share da batun silent."
"Okay Sir."
Na furta ina jin wani irin yanayi mai kama da fargaba, shakku-shakku, mai sirke da farinciki kuma. Muryar Oga Ahmad ce, sai dai a yau cike take da seriousness, kamar ranar da na fara ganin sa, da kuma rana ta biyu da na gan shi a Kaduna. Wannan ba Oga Ahmad din nan ba ne mai nishadi, idan an shiga fagen aiki babu wasa, ba sani ba sabo.

Na ajiye wayar daga gefe na tashi na cire kaya na saka bakaken khakina da ban taba sanya su ba tunda na zo garin. Na mayar da cellular dina a cikin jikina, da ma bindigata tana cikin pant dina, na soka ID card a gaban aljihuna, na dora hula a bisa kai, sannan na zuba dogon hijabi ina jiran isowar su Oga Sagir.

Kasa cin komai na yi saboda yanayin da nake ciki, yau ce ranar farko da zan fara irin wannan aikin, dole ne komai taurin zuciyar mutum ya karaya ko yaya ne. Don haka sai na samu kaina da faduwar gaba.

Ban wani jima ba sai ga kira ya sake shigowa, na dauka na ji Oga Sagir ne, ya ce min ga su nan sun iso, suna kofar gida, ni ce mace, ni nake da damar arresting Inna Azumi su kuma za su karasa wurin fada domin su sanar da maigari abin da ke tafe da su.

Na zare hijabin da ke jikina sannan na cire har kaina, dan karamin hijabi mai tsayawa daidai wuya, irin wanda aka amince mana mu saka ne na sa sannan na dora hular khakina a saman hijabin. Na bude jakata na ciro dayar bindigata ba karamar da ke boye ba, na daura rufaffun takalmana sannan na taka a hankali na fice zuwa tsakar gida.
A lokacin duk matan gidan suna zaune kowa na sha'anin gabanta, Azumi kuwa tagumi ta rafka da alama hankalinta ma ba ya tattare da su.

DARE DUBUWhere stories live. Discover now