Page 08- Zalunci

184 31 0
                                    

Page 08

Rayuwa ta ci gaba da tafiya har zuwa lokacin da muka shiga makarantar secondary don a wancan lokacin muna aji hudu ne. Ranar da muka fara zuwa a ranar ne muka dawo muka riski mummunan labari na rasuwar Abbana. Na yi kuka duk da ban gama sanin takamaimai mene ne mutuwar ba.

Tun daga nan na fara dandanar rayuwar maraici, saukin ma daya Umma ba mace ba ce ragguwa, tsaye take tana neman kudi ka'in-da-na'in, wannan dalilin ya sa ko kadan ba mu yi rayuwar babu ba. Sannan ga Baba, in dai za a ci a gidansa to duk runtsi mu ma sai mun ci. Idan har muka kwana ba mu ci ba, tabbas nasu gidan ma ba su ci ba.
Baba ya tsaya mana a dukkan komai, sannan tsaye yake a kan iliminmu.

A daidai lokacin nan ne kuma dangin Umma suka yi ta surutun ta yi aure tunda dai ba ta wuce yin auren ba, ko ba komai za ta samu mai tsaya mana, sannan za ta fita daga zargin mutane tunda ba wani tsayayye ke akwai a gidan namu ba.
Duk da karancin shekaruna amma kishin mahaifina nake yi, na goyi bayanta a lokacin da ta ce ita babu abin da za ta ci da aure, don haka aka kyale ta da zancen tunda ba uwa gare ta ba ballantana uba, tuni suka rasu sai dai dangi. Dangi kuma babu mai taimaka mana da ko sisinsa, ba su da bakin da za su tilasta mata yin abin da ba ta yi niyya ba.

Maraici bai janyo nakasu ko kadan daga amintarmu da Ummu ba, sai ma kara kullewa da muka yi, da wani irin hadin kai wanda da daman mutane ke mana daukan 'yan'uwan juna duk da ba mu kama ko kadan.
Tsabar sanya wa rai, idan ciwo Ummu ta kwanta yau, zai yi wuya gobe ko jibi ni ma ban kwanta ba. Haka ita ma in dai zan fara ciwo ba wuya ta kamu da shi. Mama ko Umma su yi ta mana fada wai wannan shegantaka ce amma ni a raina ban taba daukan hakan da komai ba face tsantsar soyayya da aminci.

Ko a makaranta ba a taba ganin daya ba a ga daya ba. Haka idan laifi na yi Ummu za ta are ta yafe ta ce tare muka yi, ko kuma ma ta saye laifin duka ta ce ita ta aikata, a karshe sai dai a hukunta mu tare.
Akwai wata Malama Zainab a makarantar, haka kawai Allah bai hada jinina da ita ba, ni ma kuwa sai na samu kaina da tsanar ta musamman ganin yadda ta dauki karan tsana ta dora a kaina ba tare da na yi mata laifin komai ba.
Da yawan 'yan ajinmu suna cewa wai don ta ga ina da kokari ne, ita da ma haka take, a maimakon malamai da aka sani da kaunar dalibi mai kokari, ita ta sha bamban, daukan tsana take ta dora masa ta yadda ba zai taba yin gwaninta a gabanta ba sai ta kushe. Da fari ni kadai ta tsana, amma ganin yadda Ummu ke tare da ni a dukkan komai, ta sanya ita ma din ta tsane ta, zai yi wuya ta shigo ajinmu ba tare da ta duke mu ba.

Akwai ranar da ta shigo ta tarar na hade kai da guiwa saboda kaina da ke tsananin sarawa har ina jin tamkar kwayar idanuwana za ta zalzalo waje tsabar azaba. Ina jin sadda duk 'yan ajin suka mike tsaye suka gaishe ta amma ni ban mike ba, haka Ummu ma tana dafe da keyata tana ba ni baki. Sai ji muka yi da karfi ta lafta mana bulalar da ta gigita mu. A gaggauce Ummu ta kama ni ta mikar tunda har a lokacin ba ta ba sauran daliban izinin su zauna ba.

Nan da nan ta hau zaginmu tana ci gaba da dukanmu har sai da bulalar ta tsinke a daidai lokacin da na zube a wurin saboda yadda nake jin kaina kamar zai tsage.
Na dai ji ihu hade da salatin Ummu, sannan na ji sadda wasu daga cikin dalibai suka yo kaina suna ambatar sunana, daga nan kuwa ba zai iya fadan komai da ya faru ba face farkawar da na yi na gan ni kwance bisa siririn tilon gadon da ke cikin clinic din makaranta. Ga Ummu tsaye a kaina idanuwanta sun kumbura suntum da alama kuka take ta yi har wannan lokacin. Ganin na farka ya sanya ta saurin kama hannuna tana kiran sunana.
"Yaya jikin naki? Me kike ji yanzu? Ina yake miki ciwo?"

Ban ba ta amsa ko daya ba sai hannuna da na duba na ga ruwan drip makale yana shiga cikin jikina.

"Wallahi Khairi wannan malamar muguwa ce, amma alhamdulillahi, silar abin da ta yi miki Principal ta yi suspending dinta for good two months. Ta ce wannan zalunci ne da a ce fa kin mutu me take tunanin zai faru? Ke an sha case dai wallahi. A kashe ta yi wa Principal rashin kunya ta tafi."

DARE DUBUWhere stories live. Discover now