Page 15- Kudin Fansa

153 21 0
                                    

Page 15

Bayan isha'i maigari ya shigo gidan nashi sannan ya sa aka kira ni. Sake gaishe shi na yi cikin girmamawa, har a lokacin ban cire kayan bautar kasar daga jikina ba.
Da sakin fuska ya ce
"Ina mai kara yi miki barka da zuwa cikin wannan kauyen namu. Ina fatan za mu ji dadinki kamar yadda muke jin dadin sauran masu zuwa bautar kasa a wannan kauye. Yaranmu suna karuwa sosai da 'yan bautar kasa, wannan dalilin ne ya sa kai tsaye muka aminta da ke tunda mun san gwamnati kike yi wa hidima."

Na jinjina kai, cikin girmamawa na ce
"Haka ne Yallabai, na ji dadi, na gode da yadda aka karrama ni. Sannan ina fatan za a amfana da ni kamar yadda aka amfana da sauran 'yan'uwana."

Jinjina kan shi ma ya yi, cikin maganarsa ta dattako ya ce
"Sai dai wani hanzari ba gudu ba. Ban sani ba ko kina da labarin cewa akwai karancin tsaro a wannan bangaren namu ba."

Duk da na sani, amma sai na yi saurin zabura, irin zaburar da ke nuni da mutum ya tsorata, ko kuma bai san labarin da ake fada masa ba.

"Tabbas babu tsaro a kauyen nan da ma na kusa da mu. Ina jiye miki tsoron kar a ji labarin zuwan ki kauyen nan masu farautar mutane su far miki. Don kusan shekara biyu kenan babu dan bautar kasan da ya sake zuwa kauyen nan, tun wani matashi da aka sace, ina jin sai da aka karbi miliyan daya daga wurin danginsa kafin aka sake shi. Tun a wancan lokacin ma da abun bai ta'azzara ba kenan, to ina ga yanzu kuma da komai ya karasa lalacewa."

Tamkar saukar aradu, haka maganganun maigari suka dinga shiga cikin dodon kunnuwana. Na san halin da 'yan garin suke ciki, don duk sai da muka binciko komai tun ma kafin a tabbatar da zuwa na. Amma a yanzu da nake jin batun daga bakin da ba zai yi min karya ba, sosai na karaya, irin karayar da zuciyar mace ke yi saboda rauninta.

"Saboda haka, ni a matsayina na shugaban kauyen nan na fada miki gaskiya, kuma na fita hakkinki. Idan da yadda za ki yi ki kaurace, bi ma'ana ki canja wuri, gara tun wuri ki yi, kafin a zo daga baya ana da na sani. Mu kanmu 'yan kauyen ba tsira muka yi ba; idan yanzu suka bukaci wani abun daga gare mu, sai dai mu ji zancen an sace wani namu. Daidai da noma, sun yankar mana daidai inda za mu noma, matukar kuwa muka wuce iyaka, komai suka yi mana mu muka ja."
Na dukar da kaina ina ci gaba da sauraron bayanin dattijon mai cike da kamala.

"Kin ga da can suna shiga kasuwannin kauyuka ko gidajen mai idan suna da bukata, to sai suka gane ana harinsu ta nan, an ma taba kama musu wasu yaransu a wani gidan mai da ke Meshe. Ganin haka sai suka canja taku. Idan kayan abincinsu ko mansu ya kare, shi ne suke kama mana yara su ce ba za su sake su ba har sai mun sayi kayan abinci mun kai musu. Za su yankar mana adadin kwanakin da idan muka ketare ba mu kai ba wallahi sai dai mu ga gawar yaranmu."

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un kawai nake maimaitawa a saman lebena. Da gaske ne dai duk yadda labarin ya je mana kenan. Ya ci gaba da cewa,

"Kin ga akwai wani kauye can gaba kadan da mu, shi kam kusan ma sun mamaye shi zan ce. Saboda kusan duk sun aure 'yan mata da zawarawan kauyen. Mace ko da mijinta da zarar sun gan ta ta yi musu, za su saita bindiga a kan mijinta su tilasta masa sakinta. Komai son da yake yi mata dolen sa ya sake ta din. Kwanaki can an samu wani da ya yi musu taurin kai ya ki sakin matar tasa, a karshe sai dai gawarsa aka binne." Tamkar mai bayar da labarin film ko littafi haka maigari ke fada min komai, na yi mamakin yadda ya yi saurin yarda da ni har yake fada min wadannan zantukan. Kodayake ya ce ba a kaina aka fara zuwa bautar kasa kauyen ba, sun riga sun saba shi ya sa ya yarda da ni.

"To kuma Baba, har yanzu ba a taba samun wasu jami'an tsaro da suka kai musu hari ba?"
Na tambaye shi. Ya yi murmushin takaici ya ce
"Ai da a ce an tashi tsaye kansu da tuni an samu saukin lamarin. To gwamnati ta yi biris da su suna ta cin karensu ba babbaka. Mu nan muna ji muna gani ba mu da 'yancin kanmu. Komai muke yi a tsorace don kar mutum ya zama gawa."
Sai yanzu na lura da hawayen da mutumin yake gogewa.

DARE DUBUWhere stories live. Discover now