Page 56- Confess 2

116 23 2
                                    

Page 56

Cike da farinciki muka fito daga kotun. Yayin da iyalan Alhaji Abdulkadir suka kasance cikin alhinin wannan al'amari tare da mamakin matar da ta sanya a kuntata wa Hannatu.

A mota na samu Haidar bayan mun gama tattaunawa ni da Fa'iz. Da annuri ya kama hannuna ya rike yana fadin,
"Barka da arziki Buttercup."
Na sakan masa murmushi.
"Na sani ba komai ba ne ba face karfin addu'a Daddy. Addu'a ce ta yi tasiri har Allah Ya matsi bakinsa ya tona asiri."
"Gaskiya ita ce tabbas."
Ya tayar da motar.
"Mu je ko City Restaurant mu ci abinci ko? Tunda akwai wadataccen lokaci."
Na daga masa kai.

"Wato mutum mugun icce ne Daddy. Kodayake ni fa ban ma yi mamaki sosai ba Allah. Dan wannan matar ba karamar muguwa ba ce."
Daga nan na hau ba shi labarin yadda ta dinga zaluntarmu ni da Ummu kawai saboda ba ta kaunarmu don muna da kokari, ashe ita haka take, hassada gare ta."
"Ai ga shi nan yau dubunta ta cika."
"Tabbas kuwa Daddy. Don yanzu hukunci iridaya za a yanke musu; da su da suka aikata fyaden, da ita da ta sanya su, zunubinsu iridaya ne, ba za a bambanta su ba a wurin hukunci."
Haidar ya yi kwafa,
"Ai gara a kashe matsiyata."
Na saki murmushi ina kallon shi.
"Ai a dokar kasarmu ba kashe su za a yi ba. Daurin rai da rai ne za a yi musu. Amma ka ga China, hukuncin kisa ake yanke wa Rapist, haka ma Egypt, Saudi Arabia, da kuma North Korea. Su ma duk kisa ne hukuncinsu. Amma ka ga India, UK, da US duk life imprisonment ne irin na Nigeria. Su kuma Israel 16 years imprisonment."
Haidar ya yi tsaki.
"Ai wallahi da ma mazakutarsu aka dinga cire musu. Da an raba su da abin da ya aikata aika-aikar, kila da wasu sun hankalta sun daina."

Dariya na dinga yi sosai har muka isa restaurant din.

***
Karfe daya da rabi aka dawo kotu. Bayan shigowar alkali, sai ga su Ahmadu ma an shigo da su, sannan Malama Zainab, wata 'yar sanda mace na tura ta amma tana tirjiya. Har sai da alkali ya daka mata tsawa sannan ta nutsu ta shigo wurin tsayuwar masu laifi.

"Ko za ka maimaita mana abin da ka fada kafin mu tafi hutu?"
Alkalin ya tambaya idonsa a kan Ibro.
"Yallabai, duk abin da muka aikata wannan muguwar matar ce ta saka mu. Ta kashe mana rayuwa tun da kuruciya muke yi mata aiki. Da ta ga kamar muna neman kama gabanmu ne ya sa ta saman mana wannan aikin a cikin estate dinsu, tunda abokin mijinta ne mallakin estate din. Sannan da tsiya ta cusa mu wurin mijinta, har ya aminta da mu. Daga nan ne sai muka samu kwanciyar hankalin ci gaba da mu'amala da ita, amma cikin taka-tsan-tsan. Ba gida daya suke da kishiyarta ba amma duk cikin estate guda ne.
Ranar goma sha tara ga watan tara na wannan shekarar, muna zaune a cikin daya daga cikin gine-ginen da ake yi, ta kira wayar Saminu. Ta ce tana son ganin mu, sannan ta fada masa a inda za mu same ta.
Ko da muka je, jakar kudi ta nuna mana, kudi ne makil 'yan dari biyar-biyar. Ta ce,
"Wani aiki nake so ku yi min, idan har kuka yi shi ba tare da kun bar wata alama da za ta darsa zargin wanda ya yi abun ba, duk kudin nan naku ne."
Muka hau tafa hannuwa, sai ta ci gaba da cewa,
"Kun san Hannatu ai. Ita nake so ku aika lahira."
Dukkanmu mun tsorata da jin hakan, saboda diyar Oga ce, kuma yarinyar ba ta da matsala. Wani lokacin har abinci take ba mu idan muka je gidan.
"An riga an cire wa uwarta mahaifa, ba za ta taba sake haihuwa ba. To ni kuma nake so har ita Hannatun ta fita daga jerin 'ya'yan Alhaji AK. Ya zamana daga ni sai 'ya'yana kawai. Kafin ita ma uwar tata a aika ta inda diyar ta tafi."
Ta fiddo bandir hudu na kudin ta mika mana kowa guda-guda.
"Wannan somin-tab'i ne. Idan kuka aiwatar da aikin, zan ba ku irinsu sau hurhud'u, kun ga duk mutum daya zai tashi da dubu dari biyu da hamsin kenan."

Jin hakan sai ya faranta mana rayuka. Muka kara tafa hannu muna shewa.
"Abu mai sauki ma kenan Hajjatu. Ai ki sa a ranki an yi an gama. Kamar yadda ba a taba samun mishkila ba a aikinmu, haka wannan din ma ba za a samu ba."

DARE DUBUWhere stories live. Discover now