Page 36- I Love You

132 26 2
                                    

Page 36-

Ana tashi daga office muka nufi gida tare da shi ya sauke ni sannan ya wuce. Na tarar gidan har yanzu da mutane ana ta zuwa yi wa Umma murnar kambun girmamawar da na samu. Bayan na gaisa da mutane na shige daki saboda ina da bukatar hutawa. Wanka kawai na yi ko abinci ban nema ba na kwanta sai bacci.

Sai daf da mgahriba sannan na tashi na nufi sallah na zuba abinci. Ina cikin ci Haidar ya kira ni. Ban dauka ba sai da na gama tas don na san idan na dauka abincin da ba zan gama ci ba kenan zai cika ni da daddad'ar hirarsa har sai abincin ya fice daga raina.
Ina gamawa na kira shi ya kashe sannan ya biyo kiran.
"Babydoll, yaya gajiya?"
"Alhamdulillahi. Na sha bacci sosai, ban jima da tashi ba. Kai fa?"
"Ban yi ba fa wallahi. Hidimarki ba za ta bar ni hutawa ba buttercup har sai na ga na kammala da komai."
Na yi murmushi don na gane hidimar tawa da yake nufi.
"Thank you baby boy, I mean thanks for everything."
"Godiyan fa ta mece ce Muffin?"
Ya fada cike da shauki a cikin muryarsa.
"Thank you for loving me, a yadda nake din nan. Thank you for supporting me, thank you, thank you, thank..."
"It's okay dan Allah. Na ji, ni ma thank you for loving me. Shi kenan."
Na saki murmushi. Komai na Haidar abun so ne gare ni. Na gama yarda cewa Haidar shi ne cikon farincikina, shi ne duniyata bakidaya.
Sai kawai na saki kuka, irin kukan da ake kira da na farinciki. A baya, na cire tsammanin samun soyayyar namiji, sai dai a yanzu da Haidar ya shigo cikin duniyata, na yakice wancan tunanin nawa. Ashe shi ya sa ba a so bawa ya yanke wa kansa kauna.
"Kukan fa?"
Ya tambaya yanayin muryarsa na sauyawa.
"Na tsantsar soyayyarka ne Aliyu Haidar..."
"Ki taimaka ki adana min hawayen nan da duk kalaman har sai na zo ki yi su a gabana. Na miki alkawarin samun kyakkyawan martani."
"Na ki wayon."
Na fadi ga dariya ga kuka.
"I love you so much."
Na fada hade da yanke wayar, ina jin cewa na gama samun dukkan farincikin duniya tunda na samu Haidar a matsayin mijin aurena.

***

Bayan sati uku da daura aurenmu ina zaune ina karatun wani katon littafi, daya daga cikin wadanda Mama ta ba ni na Ummu, sai Umma ta kwala min kira. Ajiye littafin na yi bayan na amsa na nufi inda suke zaune ita da Sadiya, Safra sun fita da wata kawarta.
Zama na yi, na mata sannu da hutawa ta amsa, sannan ta ce,
"Da ma game da batun tarewar ki ne, mun yi shawara da Mamanku, da su Marwa, a kan karshen watan gobe za a yi biki ki tare. Tunda dai Aliyun ya saukaka mana komai ya ce ba ya bukatar a kai ki da komai. Amma duk da haka akwai kayayyankin kitchen da na fara tara muku ke da Safra, ai kin san da su ko?"
Ba ta jira na ba ta amsa ba ta ci gaba da cewa,
"Zan kara wadansu abubuwan sai a kai miki. Hankalina zai fi kwanciya ki kalli wani abun ki tuna naki ne na aure da mahaifiyarki ta saya miki."

Cike da tausayi da kaunar mahaifiyata na ce,
"Umma, don Allah kar ki ba kanki wahala. Tunda ya ce ba sai an kai komai ba, ki bar wa Sadiya nawan, kudin hannunki kuma ki ci gaba da tara wa Safra. Ita ma Sadiyar ai ba wuya kin ga lokaci ya yi, tunda girman mace ba wuya gare shi ba. Ki yi saving kudinki don Allah."

Ta gyada kai da guntun murmushi,
"Ba za ki gane ba a yanzu Khairi, sai nan gaba kadan za ki san hakan da na yi daidai ne. Kowacce mace tana alfahari da abin da iyayenta suka yi mata na aure. Ban ki ta Aliyun ba, ba kuma zan hana shi ba tunda da kansa ya yi niyya. Amma ni ma zan kara nawa a kan nashi, ko da za ki hada abu biyu iri daya ne, ai dai watarana za ki kalla ki tuna da ni ko? Akwai ma sadda za ki gwada wa 'ya'yanki ki ce wannan naki ne na aure da mahaifiyarki ta saya miki."

Hawaye na saki tare da gamsuwa da maganarta. Ga wata irin kunya kuma da ta lullube ni.

"Idan kun yi waya da shi Aliyun, ki shaida masa in shaa Allahu karshen sabon watan da za a shiga jibi za a yi taron biki. 'Yan'uwa da dangina su zo su shaida, tunda an daura aure a gaggauce ba tare da an gayyaci kowa ba."
Kaina sunkuye kasa na amsa mata, hade da mikewa na koma daki.

DARE DUBUWhere stories live. Discover now