Page 60- Komai Ya Yi Farko...

268 32 2
                                    

Page 60

Sai da muka tsagaita da dariyarmu sannan na ce mata,
"Kin san Allah, tun da na tashi na yi wayo burina kenan in zama likita. Ni da Ummu. Don ba zan manta ba har akwai lokacin da muka dinga musu da wata kawarmu a kan wai ba za mu iya zama likitoci ba, saboda yaran masu kudi su kawai ke iya zama likita. A lokacin har hawaye sai da na yi, don ba karamin sace min guiwa ta yi ba. Ummu ce mai karfin halin ce mata ba wani mai kudi, mu tare muke da Allah kuma Shi zai zama jagoranmu.
Kuma wai kin san abun haushin ma?"
Ta gyada kai murmushi bai bace daga fuskarta ba. Na dora da
"Ina dawowa gida nake ba Ummata labarin yarinyar, sai cewa ta yi wai ai gaskiya yarinyar ta fada mana. Waye zai tsaya mana mu zama likitoci? Ai kuwa sai na kara barkewa da kuka. Da na ba Ummu labari duk da hakan ba ta karaya ba. Ta ci gaba da karfafar guiwata har na ji cewa za mu iya din; da kudi ko babu. Tun daga nan sai muka fara kiran kanmu da Dakta. Sai da Mama ta yi tsaye sannan muka daina. Ta ce wai muna ce wa junanmu Dakta sai ka ce da gaske."
Na dire maganar da dariya sosai.
"A lokacin har sai da Baba ya ce ta bar mu da sunayenmu mana, tunda mu muka zabi hakan yana mana fatan wata rana mu tabbata likitocin. Ta ce idan mun zama daktocin gasken ma kira kanmu da haka, amma dai ba yanzu ba. Muna ji muna gani muka hakura da Dakta Ummu da Dakta Khairi."
Muka ci gaba da dariya sosai.

Can kuma sai na koma serious, na ce,
"Kin san Allah ni dai kina macenki ban san me za ki yi da Psychology ba. Da a ce ma second degree ne da sauki."
Da murmushinta ta ce,
"Idan kika ce in sauya wani sai in sauya Anti. Ai ke din Yayata ce."
Na gyada kai,
"A'a Hannatu. Ba zan hana ki karantar ra'ayinki ba. Ki je ki yi, ina yi miki fatan alkhairi."

Hakan ba karamin yi mata dadi ya yi ba. Ta ce,
"In shaa Allahu Anti, kamar yadda ke da marigayiya kuka kasa samun cikar burinku na zama likitoci, Ummu ga ta nan, takwararku, ita za ta cike muku wannan burin. Za ta zama likita, babbar likita. Da izinin Allah."

Ummu da ke tsaye tana jin mu ta saki murmushi, ta ce,
"Ai da ma Daddyna ya ce so yake idan na girma in zama Doctor saboda in dinga duba marassa lafiya ina samun lada."
Murmushi kawai na yi ina kallon su.
Hannatu ta kalle ni ta ce,
"Da izinin Allah za ta cika muku wannan mafarkin."

Mun jima muna hira sai daf da maghriba Hannatu ta tafi. Sai na hau tunanin lokacin da take kuka tana sanar da ni nunatan da ake yi a Poly. Wai duk inda ta gitta sai ta ga ana zund'enta, wasu ma a bayyane suke gulmarta wai ita ce wadda aka yi wa fyade. Don dole tana ji tana gani ta hakura da zuwa makarantar, saboda zuciyarta ba za ta iya dauka ba, sai ma tayar mata da tsohon tabo da suke yi.
A lokacin na yi ta ba ta baki amma ta ce ita fa ba za ta iya ci gaba da zuwa makarantar nan ba. Dole na bar ta. Ta rubuta jamb kuma still ba ta samu ba. Shi ne Allah Ya taimake ta ta samu Havard din, kuma babanta ya tsaya mata, saboda tsananin tausayin rayuwarta ta yake yi.

***

Kwanaki sun ci gaba da shudewa har cikina ya isa haihuwa. Tun kafin cikar lokacin haihuwar aka shaida min ba zan iya haihuwa da kaina ba saboda an hango 'yar matsala. Dole sai dai idan EDD dina ya cika, in je a yi min CS.
Yana cika din kuwa muka tattara komai na bukata, tare da Nusaiba da Sadiya muka isa asibitin, a lokacin Haidar ya yi tafiya zuwa jihar Rivers a kan wani aiki.

Babu bata lokaci aka yi min aiki, aka ciro min sunkucecen yarona, mai kama da mahaifinsa.
Kwananmu hudu aka ba ni sallama saboda jikin nawa ya yi kyau sosai. Kuma a ranar Haidar ya dawo don da ma bakidaya hankalinsa na gare ni.

Da ya zo ya ga jaririn, tamkar zai yi kuka saboda farincikin yau ya samu magaji mai kama sak da shi. Har sai da na dinga yi musu dariya shi da Ummu yau an samu wanda ya shiga tsakaninsu. Ya dubi Ummu da ke shirin yin kuka ya ce,
"Rabu da ita my darling, ba ki da mahadi har abada. Kowa ya sani da tsohuwar zuma ake magani. Don haka ke daya ce a nan,"
Ya nuna saitin zuciyarsa. Sai kuwa ta hau dariya har da tsallen dadi, ta fita tana kwala kiran Afreen wai ta zo ta ji Daddy ya ce ya fi son ta a kan baby brother dinsu.

DARE DUBUWhere stories live. Discover now