Page 27- Dare Dubu

145 26 2
                                    

Page 27

A hankali na dago kaina ina son neman izinin tashi in tafi, kwatsam idanuwana suka shiga cikin nashi idanuwan, lumsassun nan farare tas. Na yi gaggawar sauke kaina amma sai na ji nashi har yanzu suna kaina, duk sai na tsargu na kasa fadin komai ma.
Mun dauki tsawon lokaci a hakan, kafin ya dan yi gyaran muryar da ya sanya ni sake dago kai sai kawai ya kara sakin murmushi.
"Sir...sir...permit me to..."
"You can go. Ki huta sosai at least for a week kafin ki dawo aiki."
"Sir, zan iya zuwa wurin kidnappers din nan in gan su? I want to confirm something."
"Are your really sure za ki iya ganin su? Ba za su tayar miki da kowanne irin tsohon tabo ba?"
Na daga kai, tabbas za su tayar min din, amma ina son yin magana da ko da daya ko biyu ne daga cikinsu.
"Sir, I want to discuss something with them. Ina son yin confirming ko su suka kashe min Ummu."
"Ko su ne ko ba su ba ne ba dole za a hukunta su Khairi."
"Yes Sir, na san za a hukunta su. Kawai dai..."
Ya katse ni,
"They raped you aren't they?"
Na jinjina kai.
"Za a hukunta su, mummunan hukunci. Kin san cewa ya halalta mu kashe su ba dole sai mun tura su kotu ba?"
Na sake daga masa kai.
"So ki kwantar da hankalinki, ba ki da bukatan ganin su don kar ma ki koma gida a rikice, ki rikita mana Umma, alhali ya kamata a ce kin koma ne cike da nishadin samun nasararki."

Na dan shafi fuskata, ba kuma zan iya sake musa masa ba, sai godiya da na yi na tashi bayan ya ba ni izinin tafiya.

***
Na yi murmushi, na yi dariya, na yi nishadi, sannan na yi farincikin ganin mahaifiyata. Da farko na ma rasa ta inda zan nuna farincikin nawa saboda tsananin kewarta da na yi. Na yi kewar kannena, na yi kewar girkin Ummana, sannan na yi kewar gida bakidaya; duk kuma ban tabbatar da hakan ba sai da na dawo, muka yi kicibis da su.

Uwa-uba kuma ita Umman, na tsinci nishadi da walwala a saman fuskarta, musamman sadda nake ba ta labarin nasarar da muka samu.
"Umma, addu'arku na da matukar tasiri a gare ni, na yarda har da ita, ita ce jigon nasarar ma bakidaya."
"Na san tasirinta gare ku Khairi, shi ya sa ba na kasa a guiwa wurin sanya ku a addu'o'in dukkanin sallolina. Alhamdulillahi! Ina kara godiya ga Allah da Ya nuna min samun nasararki Khairi, ina rokonSa AzzawaJalla da Ya ci gaba da ba ku nasara a dukkan komai."

Tuwon shinkafa da miyar ganye wadda ta ji ganyen ugu aka dafa, nan da nan Safra ta cika gabana da shi, Sadiya kuma ta kawo min kunun ayar da ta yi dazu na tarbar saurayin Safra.
Na yi mamakin jin wai Safra ce da saurayi, na hau tsokanarta tana rufe fuska.
"Wai Umma da yaushe aka fara soyayyar nan ne? Duka-duka yaushe Safran ta girma da har ta fara samari ban sani ba? A ina ta same shi?"

Umma ta yi murmushi ta ce
"Ke dai ki zauna a nan kawai. Bambancin ke da ita fa bai cika shekara biyu ba, kuma ke kanki yanzu kin zarta ashirin a duniya. Kin ga kenan ba abun mamaki ba ne don wadda ta haura wa shekara goma sha takwas ta yi aure. Ni din na  ma ina da sha shida cif aka daura aurena da mahaifinku."

Na kai lomar tuwo a bakina ina jin wani irin dandano mai dadi, dandanon nan da na yi kewa kwarai.
Na ci gaba da ci ina sauraron Umma da ke fadin ni ma ya kamata in samu mijin aure na ci gaba da aikin a gidan mijina idan ya yarda.
Ba ta sani ba ne, amma har yanzu ban taba jin ina sha'awar yin aure ba, saboda ba ni da abin da duk wata mace ke tutiyar zuwa gidan miji da shi. Tuni an raba ni da shi, kuma ba na son in yi aure a zo ana goranta min daga baya; ba na son a fama min tabon da ya riga ya shafe daga zuciyata.

Har ta yi ta gama dai ban ce komai ba, na gama cin tuwona na wanke hannu sannan na shige daki.
Wanka na yi na dauko kaya marassa nauyi na sanya sannan na zira doguwar hijabi na fito.

"Umma, ina son zuwa gidan Mama, na yi kewarta sosai ita da Baba."
"Kin kuwa san Baban naku ma yana nan ya zo, yana ta addu'ar ki dawo kafin ya koma. A dawo lafiya to, ki gaishe su."

DARE DUBUWhere stories live. Discover now