Page 04- Mafarin Komai

227 31 0
                                    

Page 04

Sati uku na yi a asibiti aka ba ni sallama. A tsayin wannan lokacin sosai na samu sauƙi, raunuka da ɗinkin da aka yi min duk sun warke, na gama shan magungunana ma duka. Sai dai abin da ya yi saura har yanzu shi ne wannan firgitar da nake yi wadda har cikin barci ma ba na sanin sadda nake yi, hakazalika idan na ga namiji tamkar zan haɗiyi zuciya in mutu, na kasa daina tsoron maza, daga zarar na haɗa ido da su sai in nemi ficewa daga hayyacina.
Wannan dalilin ne ya sa aka ce daga wannan asibitin za mu koma asibitin mahaukata (psychiatry) a can zan ci gaba da ganin likita domin a duba ƙwaƙwalwata a ga lafiyarta, don babu tabbacin idan ba ta samu taɓuwa ba. Daga jin an ambaci asibitin mahaukata sai hankalinmu ya sake tashi. Ganin haka ne ya sa Anti Maryam ta hau kwantar mana da hankali,
"Ba dole sai wanda yake da taɓin hankali ba ne yake zuwa wannan asibitin, wasu da dama wani larurin ne na daban yake kai su. Misali akwai masu matsalar barci, ba su yin barcin kirki to ana tura su sakatiri. Haka masu ciwon kai mai tsanani ma ana tura su can. Kada ku ɗauka wai don an ce ki je can shi kenan kanki ya taɓu, ko kaɗan ba haka ba ne. Yanzu dai yana da kyau ki ga likita mai ilmin sanin ɗan'Adam (psychologist), saboda ku tattauna, shi ne kaɗai zai warware miki matsalar da ta yi miki saura."
Ita da kanta ta raka mu har asibitin muka sayi kati da duk wani abu da ya dace, daga nan muka shiga layin ganin likita.

Da muka shiga wurin likitan abin da ya fara tambaya ta shi ne mene ne silar firgitar?
Ban iya ba shi amsa ba sai Anti Maryam ce ta faɗa masa.
Ya ɗan kalle ni da murmushi a fuskarsa sannan ya ce,
"UmmulKhairi ko za ki iya faɗa min abin da ya faru?"
Biji-bijin da nake ganin fuskarsa, da sauyawar da ya dinga yi min cikin ƙanƙanin lokaci shi ya sanya ni fasa ƙara da ƙarfi ina ƙanƙame Anti Maryam. Ita ɗin ma sai ta ƙanƙame ni tana bubbuga ni a hankali sai dai na kasa daina ihun saboda gani nake kamar ƙara kusanta ta yake yi.

"Ki nutsu da kyau Khairi, babu abin da zai same ki, shi ba mugu ba ne ba kin ji? Ki daina kuka ki yi masa bayanin abin da ya faru."
Anti Maryam ta faɗa cikin sigar rarrashi.
"Ya isa haka rabu da ita kawai. Ba na jin wani babban damuwa ne gaskiya, ba ta tattare da taɓuwar hankali, firgici da tashin hankali ne ya janyo mata haka, za kuma ta daɗe kafin ta wartsake. Ciwon ta ba ya buƙatar wani magani. Lallaɓi, rarrashi, da kuma kwantar mata da hankali shi ne babban abin da ta fi buƙata, shi ne kuma zai kawo mata waraka. Idan da a ce za ta samu kyara da tsangwama a cikin wannan halin da take ciki to da shi ne ciwon zai yi ta'azzarar da samun sauƙinshi zai yi wahala. Amma tunda ga ki, muna kyautata zaton komai zai zo mata da sauƙin. Ke dai kawai abin da nake so da ke shi ne ki ba ta dukkanin kula a matsayinta na ƙanwarki, a ja ta a jiki, a dinga fahimtar da ita cewa abin da ya faru ba shi ba ne ƙarshen farin cikinta ba. Za ta warware, komai zai zamto labari wata rana."

Ni dai jin sa kawai nake yi amma har yanzu na gaza samun nutsuwa, na ji Anti Maryam ta ce
"Likita kenan dai yanzu babu wani gwaji da kake tunanin za a yi mata? Kana ganin idan muka bi wadannan shawarwarin za ta warke kamar ba a yi ba?"

"Am 90% sure za ta warke, amma dai duk da haka zan hada ku da Dakta Gumel, Psychology Doctor dinmu, daga yanzu shi za ku ci gaba da gani, zai yi muku duk abin da ya dace da yardar Allah."

"Mun gode sosai Dakta."

Wayarsa ya dauka ya yi kira, bai yi wata doguwar magana ba ya sauke, sannan ya rubuta mana takarda hade da sabon file dina, ya mika takardar ga Anti Maryam sannan ya ce file din zai bayar a kai kamar yadda dokar asibitin ta tanadar.

Daga ofishinsa babu wani nisa sosai, da tambaya muka gano ofishin Dakta Gumel din kamar yadda yake rubuce daga sama. Babu wani layi don haka kai tsaye muka shiga. Ni dai har yanzu tsorace nake da shi amma Anti Maryam ko a jikinta, bayan ta gaishe shi, tun kafin ta fara yi masa bayani sai ga file dina wani dattijo ya kawo.
Sai da ya dudduba shi sanna ya dago kansa ya kalle ni, na yi gaggawar shigewa jikin Anti Maryam ina jin tamkar kaina zai rarrabe tsabar tashin hankali.

DARE DUBUWhere stories live. Discover now