Page 03- Fargaba

281 30 0
                                    

Page 03

Washegari ina zaune a bakin gado na ɗan jingina da bangon gadon da Anti Maryam ta ɗago don in ji daɗin zama, ita da kanta ke ba ni abincin da ta zo min da shi. Sai da na ƙoshi na gyatse sannan na mata alama da na ƙoshi. Ta buɗe robar ruwa ta ba ni na sha sannan ta rufe. Ta ce,
"Yanzu Ummulkhairi so nake ki ba ni labarin matakin karatunki, kafin mu kai batun yadda abubuwan can suka kasance, kodayake wannan ba yanzu ba, zan ba ki dama har sai sadda kika ji kina da muradin faɗa mini da bakinki, a lokacin da zuciyarki ta fara samun aminci daga wannan mummunan aika-aikan."

Kafin in buɗe baki sai ga likita ya shigo tare da wasu malaman jinya guda biyu. Anti Maryam na ganin shi ta yi saurin miƙewa, ta gaishe shi ya amsa a hankali sannan ya matso sosai kusa da ni.
"Yaya jikin naki?"
Ya tambaye ni. Sai dai a hankali na dinga ganin kammaninsa suna juyewa, suna rikiɗewa i-zuwa na Zaki, ɗaya daga cikin mutanen da suka haiƙe mini. Da ma tun daga faruwar abun nake tsoron namiji. Ko ta tagar ɗakin da nake kwance na hango namiji sai na zabura saboda juyewar da kamanninsu suke yi zuwa waɗancan mugayen mutanen.
Kanular da ke jikina ya fara ƙoƙarin zarewa amma sai na ga kamar kayan jikina ne zai cire mini. Murmushin da yake ƙoƙarin shimfiɗawa a saman fuskarsa sai na ga kamar na mugunta ne irin yadda su Zaki suka yi mini. Sai kawai na ɗora hannuwana har mai kanular bisa kaina, na ƙwalla wata irin ƙara wadda ni kaina sai da ta jijjiga jikina.

"Ku yi haƙuri! Don Allah ku yi haƙuri kada ku raba ni da suturata, kada ku raba ni da mutuncina, ku bar ni da martabata!"
Haka na dinga faɗi ina gyaɗa kaina, tamkar mahaukaciya, tamkar ba na cikin hayyacina, sai dai sarai na san me nake yi, kamar yadda nake riƙe da dukkanin abubuwan da suka faru da ni. Rikiɗewar likitan ita ce ta sanya nake ganin kamar za a maimaita ne, kamar kuma wancan na farkon ne yake sake maimaita kansa.

Ina jin sadda Anti Maryam da waɗancan malaman jinyar suka yo kaina amma ina! Na hau fizge-fizge, na ƙanƙame jikina gudun kada a raba ni da suturata.
"Ya isa haka Khairi. Babu abin da za a yi miki, ƙoƙarin sama miki lafiya ne ake yi. Kuma ba waɗancan azzaluman mutanen ba ne, likita ne wannan ya zo ya duba yanayin jikin naki, ba zai yi miki komai ba kin ji? Ba yanzu ba ma, har abada da izinin Allah ba za a sake maimaita irin wancan ba. An yi na farko kuma an yi na ƙarshe da yardar Ubangijin al'arshi mai girma."

Ina jin kalamanta sai dai har yanzu ban gama gasgata ba cikin wancan mutanen ba ne. A hankali ta kwantar da ni kan gadon, ta hau ɗan bubbuga bayana da kalamai masu daɗi da kwantar da hankali, cikin ƙanƙanin lokaci kuwa ta yi nasarar shawo kaina. A hankali na dinga sauke ajiyar zuciya har na gama samun dukkanin nutsuwata.
Ko da na duba babu likitan, ya tafi. Wani irin daɗi na ji ya saukar mini, duk da Anti Maryam ta ce mini likita ne amma ba na son ganin shi. Burina ya yi nesa da ni, in daina ganin wulgin kowanne namiji ma.

Magungunana wata nos da na ji an kira da Sista Khadija, ta ɓallo ta ba ni, sannan ta sake auna jinina na ga ta gyaɗa kai kawai ta fita, waccan gudar ma ta bi bayanta.

Bayan sun tafi Anti Maryam ta ce
"Tsoronsa  kike yi UmmulKhairi?"
Na ɗaga mata kai.
"Ba na son ganin shi Anti Maryam. Ba na son ganin kowanne namiji ma."
Murmushi Anti Maryam ta yi, har yanzu tana ɗan bubbuga bayana, kafin ta ce,
"Ba mugu ba ne, ba duk maza ba ne mugaye. Ƙalilan daga cikinsu aka samu mugayen da suka keta haddinki, kuma su ɗin ma da sannu asirinsu zai tonu. Mu a nan asibitin duka maza ne likitocinmu, dole su ne za su duba ki Khairi. Da akwai mata da ni da kaina zan roƙi alfarmar mazan su daina zuwa tunda tsoron su kike ji. Amma tunda babu, dole sai mazan. Idan kin daure nan da kwanaki kaɗan za a sallame ki idan kin ji sauƙi, sai ki daina ganin su ma duka. Ko?"

Na ɗaga mata kai ina ƙoƙarin cire wa kaina tsoron, sai dai ba na tunanin har abada zan iya.
"Yanzu dai mu ci gaba daga inda muka tsaya. Na tambaye ki matakin karatunki ba ki faɗa min ba."
Na fara yunƙurin tashi zaune Anti Maryam ta taimaka min ta jinginar da ni jikin allon gadon kamar yadda nake ɗazu.
"Na tsaya a matakin aji biyar na Sakandare. Ban ci jarabawata ba (qualifying), kuma ba mu da kuɗin da za mu biya, shi ya sa ban ƙarasa zuwa aji shiddan ba, sai kawai na haƙura da karatun na ci gaba da taimakon Ummata."
Anti Maryam ta dafe kanta, da alama tausayi na ba ta saboda yanayin fuskarta ya nuna hakan. Ta ce,
"To ina Abbanki?"
"Ya rasu." Na ba ta amsa kai tsaye.

Ta sake gyaɗa kai tana duƙar da kanta.
"Abbana ya jima da rasuwa, tun bayan haihuwar ƙanwata Sadiya."
"Allah Sarki! Kenan tare da Umma kawai kuke?"
Na jinjina mata kai.
"Baba ne yake taimaka mana da ma, kuma ya yi alwashin biya mana jarabawar WAEC da NECO, ko ba yanzu ba, ni da Ummu."
"Wane ne Baba?"
"Mahaifin Ummu, da ma can halin biyan ne babu. Ya so biya mana wannan shekarar sai dai ya yi tafiya, kafin ya dawo kuma har an rufe biya."

"Khairan in shaa Allah, UmmulKhairi. Za ki ƙarasa karatunki, burinki zai cika. Sannan za ki yi zurfi a ilmi, za ki zama abar alfahari ga iyayenki, da al'umma ma baki ɗaya. Ke dai kawai abin da nake so da ke shi ne dagewa. Ki ba da himma da kyau ki rage damuwa. Saboda damuwa ba za ta taɓa barin ki yin abun kirki ba."
Na jinjina mata kai kawai amma ina tunanin ta inda zan iya cire wannan damuwar daga zuciyata.

"Ni ba mai kuɗi ba ce ba Khairi, ba ni da halin saka ki a makarantar da za ki karanci fannin da kike so ki karanta. Sai dai na yi miki alƙawarin za ki ƙarasa Sakandare ɗinki, zan biya kuɗi ki zana jarabawa. Kafin nan, za mu fara da lesson a gida, ki ƙara samun ilmi mai kyau, daga nan sai ki ci gaba da zuwa daga farkon aji shida. In dai kika samu wannan ilmin, za ki tsallake jarabawarki da sakamako mai kyau. Idan sakamakonki ya yi kyau kuma mai gidana yana da hanyar da za ki iya samun scholarship, ki yi karatu mai kyau ba tare da ko sisinku ba."

Na yi murmushi, a wannan karon, murmushi ne na kirki, murmushi ne ingantacce, murmushin da na jima ban shimfiɗa irinshi ba a saman fuskata. Tuni na ɗauka fara'a ta yi ƙaura daga fuskata, ashe da saura na, ashe akwai alamun nasara a rayuwata. Ko da abin da Anti Maryam ta faɗa bai tabbata ba, ta samu lada mai yawa a wurin Allah, domin kuwa ba zan daina yi mata addu'a ba har ƙarshen rayuwata.

"Na gode..."
"Ya isa haka Khairi. Ki daina yi mini godiya kin ji? Ni Yayarki ce, jin ki nake har cikin zuciyata. Ina so ki ɗauke ni tamkar yadda na ɗauke ki, ki raba dukkanin damuwar ki tare da ni. Kada ki yi ƙasa a guiwa wajen sanar da ni matsala ko buƙatarki. In dai ina da dama, in dai bai fi ƙarfina ba to zan taimaka miki ko da da shawara ne."
Na ɗaga mata kai.
Na so tambayar ta ko za ta biya mana tare da Ummu sai ga Ummata, sun shigo ita da ƙannena Safra da Sadiya, hannun Sadiya dauke da kwanon silba makimanci, Safra kuma samus ne ƙarami a nata hannun.

Cikin girmamawa suka gaisa da Anti Maryam. Sosai Umma ta ji daɗin ganin sauyi a tattare da ni. Na gaishe ta ta tambaye ni ya jiki tana matsowa kusa da ni.
"Jiki da sauƙi."
Na ba ta amsa ina ƙoƙarin shimfiɗa murmushi a saman fuskata.
"Kai alhamdulillahi, tabbas na shaida an samu ci gaba sosai Sista. Ki ga har da murmushinta take amsa min da ta ji sauƙi. Gaskiya na ji daɗin lamarin nan, yadda kika san uwata ta kayar da kishiyarta."
Dariya sosai Anti Maryam ta ɗauka jin maganar Umma, sauyin yanayina shi ya janyo musu dukkan nishaɗin nan.

Anti Maryam ta faɗa wa Umma ƙudurinta game da ni. Sai dai daga dukkan alamu Umman tsoro take ji, ta yadda babu dangin iya babu na baba, daga haɗuwa asibiti amma mata ta ce ta ɗauki nauyin jarabawata.
Jin Umman ta yi shiru yanayinta kuma ya canja ya sa Anti Maryam ta kwantar da muryarta, cikin girmamawa ta ce,
"Ba Khairi ba ce farkon yaran da na taimaka Umma, ba kuma ita ba ce ta ƙarshe da izinin Allah. Ko a kan hanya idan na ga yaro ko yarinya masu buƙatar taimako ina tsayawa in taimake su, ballantana kuma 'yan'uwana mata, waɗanda taimakon su ma shi ne babban burin zuciyata. Ina son ganin mace ta samu ɗaukaka, ta samu madogara saboda dogaro da kai na ɗaya daga cikin manyan abubuwan da suke sayen darajar 'ya mace. UmmulKhairi yarinya ce ƙarama mai tsananin buƙatar taimako. Idan har ba a ɗaga irinsu to babu ranar da mugayen mutane za su san darajar mace. Babu ranar da za a san ita ma mutum ce wadda Allah maɗaukakin Sarki Ya karrama kamar kowa. Ci gaban ire-iren su Khairi zai kawo daƙilewar fyaɗe a tsakanin al'umma. Domin ko ba komai za ta yi karatu tare da fushin abin da aka yi mata, wannan fushin shi zai sanya ta dagewa wurin ganin ta yi nasara domin a ƙarshe ta cim ma burinta.
Umma ina ji a jikina Khairi za ta zama fitila a cikin mutane. Za ta zama haske abar haskaka wa mata 'yan'uwanta. Ba wai na ce dole ra'ayina shi zai zama tsani a gare ta ba, sai dai ina da yaƙinin za ta yi alfahari da ƙudurina a gare ta, za ku yi alfahari, al'umma duka za su yi alfahari. Da wannan nake roƙon ki da ki karɓi wannan tayin nawa, na yi alƙawarin ba zan cutar da ita ba."

Cikin gamsuwa Umma ta jinjina kanta ta kalle ni, sannan ta mayar da kallon ta ga Anti Maryam, ta ce,
"Babu komai Sista. Mun gode ƙwarai da wannan yunƙurin naki, ina roƙon Allah Ya cika mana wannan burin, Ya kawo mana ƙarshen duk wani azzalumi da zaluncinsa. Ke kuma Allah Ya ba ki abin da kike nema duniya da lahira."
Da ni da su Safra duk muka amsa da amin.



Amrah A Mashi❤️

DARE DUBUWhere stories live. Discover now