Page 43- Class Rep.

144 26 3
                                    

Page 43

Mun jima a asibitin, don har goma ta wuce ba mu tafi ba sai da Mami ta ce wai ba za mu tashi mu wuce ba saboda dare. Sannan ne muka yi musu sallama muka kama hanyar gida.

Ko a cikin motar ma hannuna yana makale cikin nashi haka ake tukin. Na dai fahimci sosai yake son in kasance a cikin jikinsa, kamar hakan yana yi masa dadi. Na kuwa kuduri aniyyar zama cikin jikinsa tunda yana so, babban burina shi ne ganin shi cikin farinciki, yayin da na tsani ganin kunci komai kankantarsa a saman fuskarsa.

Washegari Umma ta je ganin Mami a asibiti, sun ji dadin ganin juna, cike da nishadi suka rabu, na raka Umma har bakin keke napep din da ta sa ya kawo ta ya jira ta. Haidar ya ba shi kudinsa sannan muka koma cikin asibitin zuciyata fal da farincikin yanayin haduwar ta iyayena guda biyu.

Bayan kwana biyu aka sallami Mami bayan ta ji sauki sosai.
Haka dai kwanaki suka ci gaba da shudewa har zuwa lokacin fara lectures dinmu. Ranar farko Haidar da kansa ya kai ni makarantar kuma lokacin tashi ma ya je ya dauko ni. Haka rana ta biyu ma. Daga nan kuma sai ya dinga sanyawa a kai ni a dauko ni. Ganin duk hakan ba zai yi ba ya sanya shi fara koya min tukin. Cikin sati uku hannuna ya goge.
Ranar ina dawowa daga makaranta sai ga dalleliyar mota kirar vibe kalar ruwan siminti girke a parking space. Shi da kansa ya janyo hannuna daga cikin motarsa ya kawo ni har gaban motar, ya yi min albishirin cewa tawa ce halak malak.
Ai ban san sadda na yi masa kyakkyawan runguma ba hade da sumbatarsa.
"Thank you so much sweat heart, Allah Ya saka maka da alkhairi."
Na ma rasa inda zan tsoma raina saboda murna.
A take na kira Umma na shaida mata, ita ma din ta yi murna sosai ta ce in ba shi wayar ta yi masa godiya kafin mu je kai mata motar har gida ta gani, don ba za ta iya zuwa gidana da sunan ganin motata ba.
Daga nan na kira Mami, cikin nishadi nake shaida mata an saya min mota, kamar ma ta so ta fi Umman murna, ta sanya mana albarka sosai tare da fatan alkhairi.

Ai ranar ya ga yadda ake nuna farinciki, a jikinsa na karasa wunin, haka da dare ni na aikata duk abin da ya saba aikatawa a saman shimfidarmu. Da safe weekend ne babu makaranta, sai ga su Safra sun zo ganin mota. Haidar ya ce mu fita in dana su. Mu duka muka fice har shi, ni nake tuki yana zaune a gaba, sai Safra da Sadiya baya.
Mun sha yawo sosai kafin muka wuce gidan Mami. Nusaiba ta ce me ya sa ba mu fara zuwa mun dauke ta an yi yawon da ita ba. Na ce
"Ki sha kuruminki kanwata, naki ai na musamman ne. Sai mun zagaye kaf Katsina."
Aka sanya dariya har da Mami.
Ana cikin haka sai ga Hannatu ta zo. Cikin walwala muka gaisa ta ce ai har gidana da ma Nusaiba za ta raka ta. Na ce sai mu tafi tare tunda yanzu za mu tafi.

Da muka koma ma nishadin muka ci gaba da yi har dare. Haidar ya tafi da su duka har su Safra ya kai su gida sannan ya dawo.

Duk duniya babu wanda yake cikakken goma, amma zan iya cewa Haidar ya zarce goman da mutane ke fadin mutum tara yake bai cika goma ba. Bai taba nuna min bacin ransa ba duk zaman mu, abu daya da na fahimta shi ne yana da kishi, to sai na kiyaye duk wata kafa da za ta darsa masa kishin ballantana har bacin rai ya gitta a tsakaninmu.
Koyaushe ina kokarin ganin na faranta masa, kamar yadda burinsa a kullum bai wuce ganin murmushi shimfide a saman fuskata ba.

Ranar wata Asabar na tashi da matsanancin zazzabi, irin mai tsananin zafin nan. Bakidaya hankalinsa ya tashi, masallaci ma kasa fita sallar asuba ya yi, cikin jikinsa nake har gari ya karasa wayewa. Shi da kansa ya shiga kitchen ya soya min plantain da kwai, sannan ya hada min shayi mai kayan kamshi tunda ya san madara ba ta dame ni ba. Duk jikinsa babu walwala saboda ciwon nawa.
A hankali ya tasar da ni zaune, ya hau ba ni a baki. Sai dai a loma ta biyu, na wanke sa da amai tun daga kan kirjinsa har zuwa bisa cinya.
"Sannu..."
Kawai yake ce min. A fuskarsa babu ko alamar nuna jin haushin aman da na yi a jikinsa, duk da yadda nake jin cewa maza sun tsani amai.
Plantain din yake kara sa min a baki yana fadin,
"Daure ki ci ko ita kadai ce Buttercup. Saboda mu je asibiti ko?"
Na gyada masa kai. Don a yadda nake ji na ko na kara ci wani aman zan yi. Duk yadda ya dage a kan sai na ci ban cin ba, saboda ba na son na sake wanke shi da wani aman. Dole ya kama ni ya mikar muka nufi toilet.
Shi da kansa ya yi min wankan, da muka fito ma shi ya shafa min mai ya ciro min bakar abaya, khumra ya shafa a jikina sannan ya zura doguwar abayar ko inners bai tsaya nema ba. Ni ma kuma saboda zafin jikina, ga rashin kwari ya sanya ban koma ta kan sai na sa inners din ba.
Ya kama ni ya kwantar, ya ce,
"Ki jira ni yanzu in yi wanka sai mu tafi asibiti."
Har ya juya na kama hannunsa, cikin sanyin murya, hade da kyarmar zazzabi na ce,
"Kai fa...ba ka ci komai ba."
Ya gyada min kai.
"Ke ma ba ki ci komai ba babydoll. How do you expect me to eat something alhali ke ma babu komai a cikinki?"
Ya fice kawai.

DARE DUBUWhere stories live. Discover now