Page 49- Court

120 23 2
                                    

Page 49

Barrister Nuruddeen ya dago ya dube ni, ya ce,
"Kun san da wa za ku kara a shari'ar Hannatu Abdulkadir?"
A tare muka gyada kai. Ya sauke ajiyar zuciya,
"Barrister Rafiq Mu'az, all the way from Kaduna, shi ne lauyansu."
Kallon juna muka yi, ido bude na ce,
"Barrister Rafiq?"
Ya jinjina kai,
"Tabbas shi ne lauyansu."
Na dan tauni lebe a hankali, cikin sanyin murya na dubi Barrista Fa'iz na ce
"Tabbas akwai wanda ya tsaya musu. Kana ganin masu aikin gini ko caretakers na estate za su iya daukar Barrista Rafiq da ba ma zai fara sauraren mutum ba sai an dire masa naira miliyan biyar?"
Ya gyada kai,
"An tsaya musu ne fa. Watakila wanda ya sanya su aika-aikar shi ne ya dauko musu lauyan. But anyway, nasara na tare da mu in shaa Allah."
Barrista Nuruddeen ya amsa da
"In shaa Allah. Amma duk da haka ku ma sai kun dage sosai, seriously mutumin nan ya san abin da yake yi, ya san hanyoyin samun nasara ko da kuwa clients dinsa ne ba su da gaskiya."
"Za mu kokarta in shaa Allahu Sir."
Na fadi ina jin jikina ya yi sanyi tamkar kazar da aka watsa wa gishiri.
"Kuna da wata hujja ne so far?"
Ya tambaya yana kallo na.
"Medical reports din asibitin SARC Division kadai gare mu a hannu Sir, sai kuma ita raped victim din, duk ta ga fuskokinsu."
Ya gyada kai,
"Wannan duk bai isa ya gamsar da kotu ba. Kodayake ita shari'a tamkar mace ce mai ciki, ba a san me za ta haifar ba. Sannan akwai hujjojin da sai an fara shari'a ne suke fitar da kansu. Da yardar Allah za a dace. Abu daya dai da nake son sanar da ku shi ne; dole sai kun cire shakku da tsoron abokin karawar ku, don shi yana son ganin an nuna shakkarsa sai ya samu damar shigar da mutum ta hanya mai sauki. Ko da wasa kar ku taba nuna masa wani abu wai shi tsoro ko kuma kasawa. Ku je da confidence dinku, Allah Yana tare da ku."
"Haka ne."
Muka fada a tare.
"You can go. Best of luck."
Muka bar Office din. Zuciyata sai bugawa take da sauri.

Ko da na koma gida Haidar ya gan ni suku-suku ya tambaye ni dalili, na shaida masa babban Barrista din da aka dauko. Murmushi kawai ya yi bayan ya kama hannuwana, ya ce,
"Ke ma din ai babbar ce. Ko ba haka ba? Ba na jin ki my wife, in shaa Allahu za ku yi nasara. Ni kuma a bangarena zan taya ki da addu'a, zan sanya su Afreen ma su taya ki. Sannan Umma da Mami, su ma duk za su yi tasu. Addu'a ba ta faduwa kasa banza."

Sai a yanzu na samu kwarin guiwar yin murmushi. Na rungume shi ina furta masa kalmar I love you shi kuwa sai murmushi yake.

Da gari ya waye kafin in nufi office sai da na je asibiti na sake duba Hannatu. Na jaddada mata da dole sai ta cire tsoro idan an je kotu, ta yi bayanin gaskiyar abin da ya faru, idan ba haka ba tana ji tana gani za a zalunce ta a tauye mata hakki, a bai wa wasu gaskiya, bayan irin ta'asar da suka aikata mata. Riba biyu kenan.
Daga nan na wuce Office muka ci gaba da tattaunawa da Barrista Fa'iz.

BAYAN KWANA BIYU

KOTU

A cikin takuna mai cike da nutsuwa na shigo cikin kotun, doguwar bakar pencil gown ce a jikina, sai chiffon top wadda ta wuce guiwata. Sai kuma samanta robe dita ce wadda kadan ya rage ta kai bisa guiwar ita ma. Jabot ne nannade da wuyana sannan wig hade da handbag rike a hannuna.

Kai tsaye inda aka tanadar domin zaman mu na nufa, kusa da Barrista Fa'iz, sannan daga can gefe, Barrista Rafiq ne zaune yana aiko mana da murmushi. Murmushin ni ma na mayar masa, hade da cewa,
"Good morning Barrister. Tare za mu kara kenan."
Ya daga kai,
"Tare za mu kara. Ina fatan dai kun shirya tarbar faduwa."
Na gyada kai,
"Ba a cika baki Barrister. Ita shari'a tamkar mace ce mai ciki ai. Sai ta haihu ne za a gane abin da ke cikinta. So, ina ganin daga ni har kai ba za mu iya gane mai nasara ba har sai sadda shari'ar ta kai karshe. Wa ya san baccin makaho?"
Ya saki murmushi,
"Haka ne kuma. Sai dai kuma Bahaushe ya ce alamun karfi yana ga mai kiba."
"Kamar yadda kuma ya ce sarkin yawa ya fi sarkin karfi ba."
Na ba shi amsa ni ma da murmushin.
"Barrista UmmulKhairi. Tabbas ana marin matacce don rayayye ya ji tsoro. Na dauka marin da na dinga yi wa matattu zai tsorata ke da kike rayayya?"
Sosai maganganun nashi suka fara bata min rai, amma sai na daure na ce,
"Duk gaggawar asara ai ta jira samu ko Barrista? Ni ina ganin bai kamata ka yi gaggawar yanke hukunci ba. Ba a iya gane mai nasara tsakanin mu da kai har sai sadda shari'a ta bayyana mai sa'a."
Bayyananniyar dariya ya yi a wannan karan, ya ce,
"Ko giwa ta mutu gawarta ta fi karfin kiyashi. Ke ma kin san babu hadin biri da gada."
Na gyada kai,
"Ka manta an ce rabon kwado ba ya hawa sama."
Ya dan tabe baki hade da fadin,
"Ana ruwa ya ci makadi kina ganga ta jike. Ba maganar rabo ba ne wannan shari'ar, magana ce ta sa'a da kuma kwarewa. Ke kanki kin san ruwa ba sa'an kwando ba ne."
"Kar ka manta Barrista, da rashin kira karen bebe ya b'ata. Sai an gwada ne akan san na kwarai."
Na ba shi amsa idanuwana a cikin nashi.
"A banza, wai talaka ya hangi motar Sarki. Ke a ganin ki sai in bari kananan alhaki masu kananan shekaru su kayar da ni? Ai kuwa da na tafka babbar asara, sakin kashin kwance."
Ya karasa maganar yana cije lebensa.
Na gyada kai kawai na ce,
"To shi kenan Barrista, ma ji ma gani, wai an binne tsohuwa da ranta."

DARE DUBUWhere stories live. Discover now