Page 31- Alkalamin Kaddara

151 20 4
                                    

Page 31

Shi ne a gaba sai Nusaiba na bin bayansa, sannan Sadiya, sai ni da Safra jere da juna. Wata irin kunya ce lullube da ni ta yadda ko daga kaina na kasa.
Bayan mun shiga, muka gaishe da mata biyun da ke dakin, sannan na gaishe da Mamin kaina sunkuye na yi mata ya jiki.

"Jiki da sauki sosai UmmulKhairi. Na ji dadin ganin ku wallahi. Allah Ya yi muku albarka, Ya tabbatar mana da alkhairi."

Duk suka amsa da amin, ban da ni da Haidar.
Kamar an ce in daga kaina, karaf idanuwana suka shiga cikin na wata mata, a daidai sadda ita ma din ni take kallo. Da mamaki take kallo na, ni kuwa kallon ina na san ta nake bin ta da shi. Kafin in ce komai sai ita ta ce
"Laaah! Don Allah wannan ba Khairi ba ce, wadda ta taba kwanciya asibitinmu?"

Tabbas na san ta, kuma a asibiti lokacin da aka yi min fyade, kamar tana cikin nurses din da ke kula da ni, tare take da su Anti Maryam.
Na amsa da
"Eh, ni ce."
A kunyace, saboda ko motsin kirki na kasa tsabar kunya.

Mami ta yi murmushi ta ce
"Ashe ma kun san juna Khadija. Allah mai iko."

Ita kuwa Khadijar na ga sadda makoshinta ya motsa da karfi, da alama ta hadiyi kakkauran yawu ne, sai cewa ta yi,
"Eh, mun san juna kam. Ban dai sani ba ko ita ta manta ni, amma ni ban manta da ita ba saboda wahalar da ta sha, da kuma ciwon depression din da ya ba ta wahala. Ban san yadda aka kare ba, amma dai Sista Maryam ta fada min ta sha jinyar watanni."

"Allah Sarki! Allah Ya kara mana lafiya."
Mami ta fada tare da kallon Nusaiba ta ce ta dauko mana ruwa daga cikin fridge Safra ta yi saurin cewa mun koshi, mun gode.

Mikewa Haidar ya yi ya ce mu same shi a mota idan mun gama. Ni ma na yi saurin mikewar saboda duk a darare nake, kamar idan aka ce min kyat! In zura da gudu.
Bayan ya fita ni ma din na bi bayansa, amma sai na tsaya a bakin kofar ina jiran su Safra su fito, kuma suna fitowar kafin mu wuce, ta hangi kawarta ta ce mu dan jira ta ta je ta gaishe da Mamanta mu wuce. Na yi tsaki ina cewa ta yi sauri kar mu bar Haidar da jira.

"Allah Ya ja zamanin love birds. Ba zan jima ba..."
Ban gama sauraren maganar Safra ba na tsinci wani mummunan zance da ke fitowa daga dakin da muka fito.

"Wai Anti Radiya kina nufin wannan yarinyar ita ce Haidar zai aura? Ai kuwa da sakyal! Dan ni dai wallahi ban goyi bayan kingin 'yan ta'adda ba."

Muryar Mamin na ji tana tambayarta me take nufi? Ba ta gane nufinta ba.
"Kidnapping dinta fa aka taba yi, shi ne aka yi raping dinta, silar kawo ta asibitinmu kenan. Kuma kina ji kina gani sai ki bari Haidar ya aure ta? Wa ma ya sani ko akwai wata boyayyar cuta..."

Gam! Da karfi Nusaiba da ke tsaye kusa da ni ta buga kofar dakin hade da shigewa.
"Haba Anti Khadija! Wannan wace irin magana ce kike yi dan Allah? Idan ma a matse kike da yin me ya sa ba za ki bari su bar asibitin ba? Ga ta nan tsaye a bakin kofa fa tana jiran kanwarta ta zo su tafi. Kuma ta ji komai wallahi..."

Ban ko gama sauraren abin da Nusaiba ke fadi ba na bar wurin da gudu ina sakin wani irin kuka. Irin abin da nake gudu kenan da ma, watakila dalilin da ya sanya ni faduwar gaba kenan sadda muka iso asibitin.
Kasa kai kaina inda motar Haidar take na yi; daidai fitowa daga reception na duke ina wani irin kuka, sai ji na yi Sadiya tana kokarin kama ni ta mikar don a gabanta aka yi komai, tare muke tsaye har shigar Nusaiba dakin.

Zuwan Safra ta taimaka mata suka mikar da ni hade da nufar motar Haidar. A cikin yanayin da ya gan ni ya tsorata shi, ya hau tambayar su Sadiya, sai dai kafin ta ba shi amsa wayarsa ta yi ringing, ya dauka da sallama a bakinsa.
To kawai na ji ya ce, sannan ya saka wayar a cikin aljihunsa.

DARE DUBUWhere stories live. Discover now