Page 44- Happy Birthday

129 27 1
                                    

Page 44

Yanayin yadda fuskarsa take ya sanya hawaye tsinke min, na hau gyada kai ina fadin,
"Ba yadda kake zato ba ne, please ka saurare ni baby boy..."
Daga min hannu ya yi, cikin bacin rai ya ce,
"Dakata UmmulKhairi! Ya ishe ki haka. Babu wani abu da za ki fada min kuma."

Cike da mamaki nake kallon sa. UmmulKhairi? Wannan shi ne karo na farko da ya kira ni da UmmulKhairi tun bayan aurenmu. Idan har bai kira ni da sunayen soyayya ba to sai dai ya ce Khairi, shi ma Khairin sai idan zai yi min serious magana.
"Baby...yau ni kake kira da UmmulKhairi haka kai tsaye?"
Na fada cikin tashin hankalin da ke tinkaro ni.
Fuskarsa a tsuke ya ce
"Don me ya sa ba zan kira ki da sunanki na gaskiya ba? Me ya sa za ki boye min ki ce karatu kike alhali waya kike yi da wanda ba muharraminki..."
Fuskata da ta wadatu da ruwan hawaye na dago na saita kallo na a gefensa. Cikin bacin rai na dakatar da shi.
"Idan za ka kira ni da komai ka kira ni, idan ka so ma ka hada har da Abubakar din sunan ubana ka kira ni da shi, amma kar ka zarge ni a kan abin da ba ni da hakki a kansa. Me kake tunani? Wayar Soyayya muke ko me?"
Cikin nashi bacin ran da har muryarsa ta bayyana ya ce,
"Duk abin da zuciyarki ta ba ki shi nake tunani. Don me za ki bar ni a daki tun dazu alhali na fada miki da sassafe zan fita, ki zo nan kina waya da wani katon banza? Ko kin zaci na shiga kenan ba zan fito ba?"
Kuka nake sosai ina duban sa, duk yadda na so yi masa bayani a yanzu ba zai gane ba, saboda zuciyarsa ta riga ta rufe, kishi ya mamaye idanuwansa ta yadda ya kasa ganin hawayen da nake yi ballanta ya tausaya min; hawayen nan da ya tsani ganin ina yin su.
Har ya juya zai tafi na janyo hannunsa, ya fizge da karfi. Na sake rikewa sai ya juyo ya ce,
"Please let me be. Ki je can ki ci gaba da uzurinki."
Kawai ya shigewarsa daki.

Zuciyata idan ta kai dubu to ta baci. Shi a ganin sa ni na yi masa laifin, amma har ga Allah na fi shi jin haushi a yanzu. Sosai na ji haushin abin da ya yi min, kuma zargi na da ya yi shi ya fi bata min rai fiye ma da tsawar da ya kwatsa min. Kuka nake da girman tashin hankalin da kaddara ta zo min da shi.

Karatun da ban karasa ba kenan, a nan na tafi na bar takardun, a karo na farko tun bayan aurenmu da muka raba wurin kwana.
A runtse ban runtsa ba, tunda na kwanta in ban da kuka babu abin da nake yi. Da na gaji sai na mike kawai na yo alwalla na fara jera nafilfili har zuwa lokacin sallah. Da na yi sallar a nan bacci ya dauke ni, abin ku ga mai ciki, ga kuma rashin bacci. Ni ce ban farka ba sai kusan sha dayan safe.

A daburce na mike bayan na duba agogo na ga lokaci. Shi kenan na yi missing CA din Doctor Zubair, amma duk wannan ba shi ba ne babbar damuwa ta ba, fushin da Haidar ya yi da ni, duk da ni ma fushin nake yi da shi.
Tun da muka yi aure bai taba zuwa office ba tare da ya ci abinci ba. Idan ma fitar sassafe ce ta kama shi irin wannan, to zan dafa masa ya tafi da shi. Amma yau, fushinsa ya hana ya tada ni in girka masa wani abu. Ni kuma Allah Ya sani bacci ne da ya kwashe ni.

Cikin rashin kuzari na je na yi wanka, daga nan kuma sai wani irin zazzabi ya lullube ni, har dare ina kwance daki sai rawar sanyi nake yi.
Hakan ya kara bata min rai, ta yadda ya ji ni shiru duk da na dan jiyo motsinsa a parlor amma ya gagara zuwa ya duba lafiyata bayan ya san ina da laruri.
Haka na ci gaba da zama har goman dare, kamar daga sama sai ji na yi an bude kofa. Ban dago kai ba amma na san shi ne, saboda kamshin turarensa da na gama haddacewa.

A kan bedside ya dora abin da ya shigo da shi, na dan saci kallon sa, katon birthday cake ne kalar pink. Na dafe bakina, shaf na manta ashe yau ne birthday dina. Sai na ji wani irin farinciki. Allah Sarki Haidar my darling husband. Duk fushin da yake yi da ni ashe bai manta da birthday dina yau ba ne.

Har ya juya zai tafi sai kuma ya juyo, a lokaci guda muka hada ido, na dan matse idon nawa wanda hakan ya sanya hawayen da ke ciki suka sauko. Ban janye duba na daga gare shi ba, kamar yadda shi ma din bai janye ba.
A hankali ya fara takowa, har ya iso inda nake, ya zauna bakin gadon hade da sanya hannunsa ya share min hawaye yana gyada min kai.
"It's okay."
Ya furta a saman lebensa, har yanzu kuma bai janye idanuwansa ba daga cikin nawa.
Ban yi shirun ba sai tashi da na yi na fada cikin jikinsa, ya kuwa sa hannuwansa duka biyun ya zagaye ni da su. A tare muke jera ajiyar zuciya.

Saurin dago fuskata ya yi ya kalle ni, a hankali ya ce,
"Your temperature is too high. Are you okay?"
Na gyada kai.
"Ta yaya zan zauna da lafiya alhali mijina yana fushi da ni?"
Na fada cikin kuka.
"Ko me zan yi maka ka daina share ni Haidar. It hurts."
A hankali yake shafa bayana, sai can kuma ya ce,
"Na dauka lafiyarki lau fushi kika yi da ni ya sanya kika share ni. Na ji haushin jin ki shiru ne; kin ba zuciyarki wahala ni ma kuma kin ba tawa wahalar. Kin bar ni da yunwa, ke ma kin bar kanku da yunwa duk da ba ke kadai ba ce. Wuni guda a cikin daki."
Ya sake rungume ni, tamkar za a bambare ni daga jikin nashi ne.

Mun jima a haka kafin ya tayar da ni ya mikar, hannuna a cikin nashi muka fita parlor, ya zaunar da ni sannan ya nufi kitchen, babu jimawa sai ga shi da gasasshiyar kaza ya ajiye a gabana. Sanyi karara, daga cikin fridge ya ciro ta don ta kai wurin kwana uku ma.
Shi da kansa yake ba ni har na koshi, sannan shi ma ya ci. Bayan ya dauke sai ga shi da yoghurt ya zuba min a kofi na sha. A take na ji cikina ya dauka.
Paracetamol ya je ya dauko ya ba ni na sha shi ma ya sha, idanuwansa da jiniyoyin kansa kawai na kalla na gane ciwon kai yake yi.
Ya sake kama hannuna muka koma daki.
"Bari in je in yi wanka. Ina zuwa."
Ya fada hade da ficewa.

Cake din da ke ajiye kan side drawer nake kallo, babba ne sosai, a sama an rubuta HBD Buttercup. Na saki murmushi. Ji na yi zazzabin ma ya tafi, saboda shiryawar da na yi da mijina.

Bai jima ba sai ga shi ya dawo, wannan karan fuskarsa da annuri, ya zauna a gefena.
Hannuwansa ya saka a cikin nawa, idanuwana a cikin nashi ya ce,
"Happy birthday baby girl, and am very sorry for yesterday."
"It's okay."
Na furta ina murmushin ni ma.
"But I have to explain everything to you."
Ya gyada min kai alamun ba ya son ji. Ni ma na gyada masa kan.
"Dole za ka sani saboda gaba, ka dinga bincike kafin ka yanke hukunci, ka daina saurin daukan zafi a kan abin da ba ka san takamaimai ya yake ba. Class rep ya kira ya fada min CA din da za mu yi karfe daya an dawo da ita takwas na safe. Malamin ya ce ya sanar da kowa, ya fadi a group amma ya ga kamar ba na online ban sani ba, kuma ba zai so in missing CA din nan ba. Shi ne nake yi masa godiya kai kuma ka fito a daidai lokacin."
Na karasa maganar da sanyin murya, hawaye yana fito min.
Bakinsa ya sanya ya lashe hawayen nan tas sannan ya kyale ni ba tare da ya furta komai ba ya janyo cake din ya dora a saman cinyata. 'Yar karamar wukar da ke makale daga gefe ya dauka, ya soka ta a cikin hannuna, sannan ya hada hannun nawa da nashi, muka yanka cake din a tare. Da na dauki cake din kai tsaye bakinsa na kai, ya fara taunawa idanuwansa a cikin nawa ya furta
"Happy birthday Buttercup."
Kafin in ce komai ya dora da
"I love you so much."
Ya ciro yankan cake din ya sanya a cikin bakina.
"Thank you."
Na fada a hankalina ina cin cake din da na matukar jin dadinsa, kuma signature dinsa ya ba ni tabbacin na Amrah's kitchen ne (07037603276).

Daga nan na dauki cake din na kai shi cikin fridge, ko da na zo dan gyara inda cream din ya bata wurin na tarar ya sanya tissue duk ya gyara. Ya bude hannuwansa na shige a ciki.

A cikin daren na sha happy birthday yadda ya kamata. Mun manta da kowa da komai. Mun manta da duk wani tashin hankali da ya shiga tsakaninmu.
Da safe ma sai da muka sha soyayyarmu kafin muka shiga kitchen tare na soya  farar doya da scramble egg. Muna yi muna hira har muka kammala.

A dining area muka yi branching, ina cikin jikinsa har muka ci abincin muka gama. Da ya mike zai tafi na ce,
"Sweatheart ban yi CA din jiya ba, and malamin, Doctor Zubair...yana da zafi sosai."
Sai da ya ba ni kyakkyawan peck sannan ya ce,
"Ki tura min lambar class rep dinku, sai ya hada ni da malamin. Zan yi magana da shi in shaa Allahu za a yi miki makeup test."
Daga nan na raka shi har bakin mota, yana yi wa cikina dariya wai kato da shi, ni kuma sai turo baki nake yi.
Shi kenan sai aka rufe chapter din. Ya samu Mallam an yi min CA lafiya lau, bisa hujjar juna biyun da nake da shi jikin ya dan motsa min shi ya sa ban samu na je na yi ba.
Wannan dan sabanin da muka samu, sabani ne da kowanne ma'aurata za su iya samun sa. A tsakanin harshe da hakori ma ana sabawa, ballantana kuma mata da miji. Duk yadda suke so da kaunar junansu dole akwai ranar da shaidan zai iya gittawa a tsakaninsu.
Na dauki hakan a matsayin ajizanci irin na dan'Adam, don duk yadda Haidar ya so faranta min tare da kaurace bacin raina, dole ne sai hakan ta gitta.

Na saki sassanyan murmushi bayan na koma cikin gida. Har ga Allah ina kaunar mijina, fushinsa ba karamin taba ni ya yi ba. Na kuma dauki alwashin zan kiyaye, ba zan sake bari ko karfe tara na dare in dauki waya ba, zan ma dinga kashe ta domin zama lafiya ya fi zama dan sarki.


Amrah A Mashi❤️

DARE DUBUWhere stories live. Discover now