Page 57- Wata Sabuwa...

125 23 1
                                    

Page 57

Ganin kiran Haidar a wayata ya sanya ni yi musu sallama, har mota suka raka ni, bakin Hannatu ya gagara rufuwa.
Haidar ma da annuri ya yi musu murnar samun nasara. Anti Khadija ta ce,
"Mun gode sosai Haidar, don Allah ka kara yi mana godiya. Duk da dai zan zo har gidan ma, duk wannan ba ta yi ba. Anti Radiya ma har gida zan iske ta in ba ta labarin karamcin Khairi."
"Babu komai ai yi wa kai ne. Kuma da ma saboda ire-iren haka ne ya sanya ta fara aiki a karkashin SARC din. Muna fatan a samu dakushewar masu aikata fyade nan gaba kadan."
"In shaa Allahu Haidar, bari mu wuce, ga Babansu can yana jiran mu."
Ta kama hanya ta tafi, mu ma muka wuce.

Gidan Mami na ce mu je saboda na dan kwana biyu ban je ba.
"Ke da ba kya jin dadi baby girl, ga gajiya. Ba gara mu wuce gida ba ki huta?"
Na gyada masa kai.
"Kadaici ga mara lafiya ai assasa ciwo yake. Mu je din dai, in shaa Allahu zan wartsake."
Ya daga kafada.
"Shi kenan to. Mu je in ajiye ki sai in wuce wurin aikina ni ma."
"Wurin aiki da yammacin nan? Uku fa ta wuce Daddy."
"To ai kwanakin nan ina kalula ne saboda uzurinki buttercup, kuma yau din akwai abin da ya kamata a ce na je na duba."
Na daga kai.
"Shi kenan to. Allah Ya taimaka."
"Amin."
Ya amsa hade da sumbatar bayan hannuna.

Da muka isa bai ko shiga ba saboda saurin da yake yi, ya ce kawai in gaishe da Mamin, idan ya dawo ya shigo.

A babban parlor na same ta zaune da bakuwa. Na duka har kasa na gaishe su, kafin in koma kan kafet na zauna.
"Sannu Khairi. Yaya gajiya?"
"Wallahi lafiya lau Mami, ai yanzu haka ma daga kotu muke. An kammala shari'ar Hannatu, kuma alhamdulillahi mun yi nasara."

Sosai fuskar Mamin ta fadada da annuri. Ta daga hannu tana mika godiyarta ga Allah.
"Allah kadirun ala man yasha'u. Wallahi ko don addu'ar da muka dukufa kanta an samu nasara. Aliyu cewa ya yi fa har yaranku ba dare ba rana sun dukufa addu'a. Da yake Allah maji kan bayinSa ne, ga shi nan Ya amsa mana."

Na saki faffadan murmushi na ce,
"Ai Mami ba ma za ku tabbatar da karfin addu'a ba ne ya yi tasiri sai kun ga yadda lamarin ya kaya. Har na fara sarewa, saboda wasu shaidun karya da aka kawo. A cikin kankanin lokaci kuma sai Allah Ya juya abun. A take fa, yadda kuka san an matsi bakin daya daga cikinsu, sai kawai ya fashe da kuka, ya hau tona musu asiri."

Gudar matar da na iske su tare ta ce,
"Allah ne Ya matsi bakin nashi ai. Shi ya sa komai mutum ya sanya a gaba ake so ya fi karkata ga Allah, ya fada wa Allah damuwarsa, ya nemi agajinSa Allahu AzzawaJalla. Sai ki ga abun ya zo da sauki."
"Haka ne tabbas."
Na fada a hankali. Sannan na mayar da duba na ga Mami ina cewa,
"Kuma Mami ba ku san wani abun mamaki ba. Abokiyar zaman Anti Khadija?"
Ta kalle ni hade da daga kai.
"Na gane ta. Uwargidan Alhaji AK kenan ko?"
Ni ma na daga mata kan.
"Ita ce ta sanya a kashe Hannatun, shi ne su kuma suka fara da nasu uzurin, babu dai rabon mutuwa."
Innalillahi Mami da kawar tata ke ambata suna maimaitawa. Mami har da tafa hannuwa fuskarta cike da mamakin abin da nake shaida mata.
"Yanzu kuma haka duniyar ta koma?"
"Wallahi kuwa Mami, ai har ma ta zarce haka. Sai ga shi ta silar wannan, asiri ya kara tonuwa ashe su dai wadanda suka haike wa Hannatun, su ne suka kashe 'yar'uwata Ummu."
Daga nan na shaida mata komai, tun daga mafarin rashin jituwarmu, har zuwa abin da Ibro ya shaida wa kotu yau.
"Duk da abun al'ajabi ne amma Mami biri ya yi kama da mutum. Matar nan wallahi ba ta da imani ko da ma can."

Mami ta gyada kai,
Ai ga shi nan Allah Ya gwada mata iyakarta tun a duniya ko?"
Ta dafe fuska cike da mamaki.
"Kai Allah Ya kyauta. Mutum sai Allah. To wai me ta ce Hannatun ta yi mata?"
"Babu wani kwakkwaran dalili fa Mami. Kishi dai ne kawai."
Na fada mata dalilin, kamar yadda aka fada a kotu.
"A yanzu haka dai hukuncin kisa ne kanta, nan da kwana daya ko biyu, highest dai a yi kwana uku ba a kashe ta ba."
Mami har da guntuwar kwallarta ta ce
"Duniya kenan...oh oh oh! Duniya budurwar wawa. Wai saboda abun duniya kawai mutum ya jefa kansa a halaka. Ta janyo wa yaranta abun fade har diyan-diya ba zai bar su ba. Allah Sarki!"

DARE DUBUWhere stories live. Discover now