Page 07- Tushiya...

210 27 6
                                    

Page 07

Barka da zagayowar ranar Hausa ta duniya (26th/8/2023)

***

Cikin dauriya na ce
"Na gode Baba, Allah Ya kara girma."
Kuka sosai nake yi, tuna da a ce Ummu na nan da yanzu ta harare ni jin ina yi wa iyayenta godiya, abin da ta ki jini kenan, wai kamar ban dauke su nawa iyayen ba.

"Ya isa haka, ki daina kuka Khairi."
Mama ta furta cikin nata raunin.

"Babu ranar da zan daina kukan rashin Ummu, rashinta wani irin babban gibi ne a rayuwata, irin wanda babu abin da zai iya cike shi. Ban san dalili ba, amma ji nake tamkar ba ni da sauran amfani a duni..."
"Ki daina fadan haka mana Khairi kar ki yi sabo."
Mama ta yi saurin kwaba ta. Na yi shiru kawai amma ina jaddada wa kaina hakan ne, babu ko tantama rayuwar nishadi ta yi kaura a duniyata.

Na mike cikin sanyin jiki na yi musu sallama. Baba ya kara jaddada min a kan in kawo abubuwan da ya ce din daga na koma gida, ko kuma idan su Sadiya sun dawo daga makaranta in ba su su kawo na amsa da to sannan na tafi, zuciyata na kara ingizo hawayen da na gagara dakatar da shi.

Bayan sati daya aka bukaci in je domin a dauki thumb print dina. Ko da na je makarantarmu malamai da yawa tambaya ta suke ina UmmulKhairi lukuta, kamar yadda ake kiran mu ni siririya ita kuma lukuta. Wasu sun ji labarin rasuwarta suka yi min gaisuwa amma wasu ba su sani ba su ne dai masu tambayar ina Hassanar tawa tunda ba su saba gani na babu ita ba. Ko larurin ciwo ba ya sanya a ga daya ba a ga daya ba sai dai idan kar a gan mu mu duka.
Ta rasu kawai nake fada musu ba tare da wani dogon bayani ba. Wadanda suka san da zancen garkuwan da aka yi da mu suka hau jajanta min, suna karawa da tambayar ko dai a can ne aka kashe Ummu ko kuma wani ciwon ta yi?
Ni dai babu mai samun amsa daga gare ni sai hawayena kawai da nake sharewa.

Da muka gama duka ofishin rijistar JAMB muka je tare da Baba. A can aka yi mini komai na cike, sai dai wani al'amarin Allah, a maimakon in cike medicine din da ya kasance mafarkinmu, sai na kasa. Na juya na kalli Baba da shi ma din ni yake kallo. Sannan na kalli mai cikewar na ce
"Don Allah idan ina son zama jami'ar tsaro me ya kamata in cike?"

Murmushi mutumin ya yi, ya ce
"Jami'ar tsaro kuma kina mace? Wannan aikin ai bai cancance ki ba gaskiya. Ki bar wa maza dai su ya fi dacewa da su. Idan har kika ga mace jami'ar tsaro to sai dai yare ba Bahaushiya ba."

Ko kadan kalaman nashi ba shiga ta suke ba. Fahimtar hakan ya sanya shi cewa
"Me zai hana ki cike mass com? Ma'ana aikin 'yar jarida. Kusan duk inda jami'in tsaro zai je to shi ma dan jaridar zai je har ma ya zarce. Sannan babu ruwansa da mace ko namiji kowa zai iya yin sa. Ni dai ina mai ba ki shawara da ki karance shi, zai dace da ke sosai."

Ko kadan ba wai burge ni yake yi ba, ina nan kan baka ta ba gudu ba ja da baya. Sai dai kafin in ba shi amsa, Baba ya ce
"Abin da ya fada gaskiya ne UmmulKhairi. Ke diya mace ce kuma Hausa-Fulani. Aikin jami'an tsaro ko kadan bai dace da ke ba. Na san dalilin da ya sa kike son ki yi shi, saboda daukan fansar abin da aka yi wa 'yar'uwarki. Ki jingine wannan tunanin don ba lallai burinki ya cika ba. Ki cike likitanci abin da kuka jima kuna mafarki ke da 'yar'uwarki Ummu."

Kuka nake sosai ina gyada kai,
"Ba zan iya ba Baba, ba zan iya zama likita ba alhali babu Ummu. Da burin zama likitoci muka girma, da shi muka yi wayo tun kafin mu san kanmu, kafin ma mu san mene ne likitancin. Don haka ba zan iya zama likita ba a lokacin da babu Ummu a duniyar."

Baba ya sauke ajiyar zuciya ya ce
"Shi kenan to ki daina kukan. Bawan Allah ka cike mata mass com din sai ta karance shi."

DARE DUBUWhere stories live. Discover now