Page 45- WTTW

143 21 2
                                    

Page 45

Rayuwa ta ci gaba da tafiya har zuwa lokacin da cikina ya shiga wata tara, haihuwa ko yau ko gobe. Kuma Allah Ya taimake ni daidai lokacin mun tafi hutun session wanda akalla za mu iya kai wata biyu zuwa uku muna hutun.
Nusaiba da Safra ne suka dawo gidana da zama. Ita ma Safrar an sanya ranar aurenta saura wata biyar yanzu.

Muna zaune a daki na yi pillow da cinyar Haidar, cikina ya dan motsa, marata ta karta. Da ma tun da safe na dan fara jin alamar, amma kasantuwar ba ta tsananta ba ya sanya ban wani damu ba na ci gaba da sha'anina. Sai dai lokaci zuwa lokaci ina jin ciwon.
A yanzu ma da ciwon ya karta, sai na dauka irin wancan ne. Amma jin na yanzu ya fi tsanani ya sanya na yi saurin tashi zaune ina cije baki.
"Ya dai?"
Haidar ya tambaya yana kallon yanayina.
Na kirkiro murmushi na ce,
"Babu komai."
Bai gamsu ba amma sai ya kyale ni.
Har zuwa sha dayan dare ina jin ciwon. Can cikin bacci na ji marar ta sake katsawa, na tashi na shiga toilet, wurin yin fitsari ne na ga wani abu yana bi na wanda ya ba ni tabbacin alamun haihuwa ne, na kwaso jikina na dawo kan gadon da kyar, ina yi ina cije baki.

Na dan jima a hakan, ina jin ciwo sosai, kafin na bigi Haidar da karfi, ya yi firgigit ya tashi zaune.
"Tashi ka kai ni asibiti."
Na fada cikin sanyin murya.
"Haihuwar ce? Oh my God! Sorry babyna...ba ki jin dadi? Ai tun dazu jikina ya ba ni kina boye min ciwo baby girl."
Yana maganar yana sanya jallabiyarsa. Ya zo ya kama ni a hankali muka fita, ko ta kan Nusaiba da Safra ba mu bi ba muka tafi asibitin da nake yin antenatal.

Muna zuwa aka karbe ni da sauri, ko da aka duba har na kai 6CM. Mamaki sosai suka yi tare da jinjina wa dauriyar da na yi duk da haihuwar farko ce amma ban ce a kai ni asibiti ba sai da na yi nisa.

Delivery items suka bukata na ce babu. Tare da wa nake? Nan ma na ce ni kadai ce sai mijina yana waje. Ina kayan welcoming baby? Su ma din ban dauko komai ba duk da tarin sayayyar da muka yi ta haihuwar.

Mamaki da dariya suka kama, ganin zallar yarinta a cikin lamarin nawa. Wata daga cikinsu ta fita, sai ga ta ta dawo da delivery items din. A take aka yi admitting dina sannan aka tura ni labour room.

Tun ina ganin ga haihuwar nan har sai da na fara galabaita, a lokacin Haidar ya tafi gida, sai na jiyo muryar su Nusaiba da alama su ya tafi daukowa da ma. Nurse din da ke tare da ni ce ta fita, babu jimawa ta shigo da kayan babies din da muka saya musamman domin tarbar babyn ranar farko.

Karfe bakwai na safe na haihu. Tsananin azabar da na ji ta sanya ni cewa ta janye min yarinyar, sadda ta dora ta a saman cikina.
A hankali kuma kamar zarar kaya na ji ciwon babu shi. Na daga kaina, na dubi yarinyar da ke nannade cikin shawul din setin kayan da aka sanya mata. Mun riga mun san mace ce tun wurin scanning, don scanning uku aka yi min kuma duk sakamako daya ya bayar, shi ya sa da muka tashi duk sai muka yi sayayyar kayan mata, muka yi ta da wajewa da masu wurin a kan idan ba mace aka samu ba za a mayar, suka kuma amince.

Ganin irin kallon da nake bin yarinyar da shi ya sanya nurse din dauko ta ta miko min bayan ta gama sanya mata socks. Na karbe ta, sak fuskar Haidar, har shape din idanuwan nan nashi da ke burge ni. Kamar yarinyar ta san me nake kallo sai kuwa ta bude idonta ta saita su cikin nawa, a take na ji wata irin soyayyarta ta shige ni.
Ganin ba ni da niyyar mika ta ya sanya nurse din cewa
"Ki kawo a kai musu babyn, na dai fada musu kin haihu ne amma ko gender ba su sani ba."
Na mika mata ita, ina bin su da rakiyar ido.

Kusan minti talatin muka dauka ana shirya ni, kafin aka mayar da ni can amenity inda na tarar da Haidar da su Nusaiba sai kallon baby suke.

DARE DUBUWhere stories live. Discover now