Page 58- Women Leader

128 26 0
                                    

Page 58

A hankali cikin sanyin murya ta ce,
"Farouk ne..."
Sai kuma kuka ya ci karfinta ta dakata.
"Wane Farouk? Me ya faru da shi?"
Ta fado cikin jikina, kuka take yi sosai tana fadin,
"Wai ba zai aure ni ba, ya rabu da ni tunda kaddarar Fyade ta fada kaina. Ba zai iya runguma ta tare da kaddarata ba Anti Khairi."
Kuka sosai take yi, ta yadda duk mai zuciyar imani idan ya gani dole ne sai ya tausaya mata.

"Da ma ina ta kiran sa ya daina dauka. Jiya da aka gama shari'a na masa kira fiye da goma bai daga ba, bai kuma biyo kiran ba. Na yi masa texts shiru babu reply. A whatsapp ma ina ganin shi online amma ya ki kula ni. Shi ne yanzu abokinsa yake fada min, wai Farouk din ya ce ba zai iya aurena ba, saboda na riga na zama second..."

A hankali nake dan shafa bayanta, cike da tausayi na ce,
"Ki yi hakuri to ki daina kukan. Watakila da ma can babu alkhairi a cikin tarayyar taku shi ya sa Allah Ya kawo karshen alakar a yanzu. Kin san sau da dama mutum zai so abu amma sai ya kasance ba alkhairi ba ne gare shi. Haka kuma kana iya kin abu da dukkanin zuciyarka, amma sai ya zama shi ne alkhairin naka. Komai yana da silarsa Hanna, ki dauka cewa fyade kaddararki ce, kuma wannan kaddara ita ce silar rabuwarki da Farouk. Kada ki taba dora hakan a kanki, kar ki dauka wai kina da laifi daidai da kwayar zarra. Da ma can Allah Ya rubuta shi din ba mijinki ba ne."
A hankali ta fara jera ajiyar zuciya, alamar kalamaina suna shigar ta.

"Kuma in ban da abunki ma Hanna, duka-duka nawa kike? Ko shekara ashirin fa ba ki yi ba, ba ki ma cika sha tara ba. Ko aure kike so?"
Ta gyada min kai hade da rufe ido alamun kunya.
"To kin gani. In shaa Allahu mijinki yana nan zuwa, watakila Balarabe ma daga kasar Saudiyya. Kila kuma Ba'indiye ne ma, Allah kadai Ya bar wa kanSa sani."

Na yi dariya, ita ma ta yi.
"Wannan shi ne babbar matsalar mutane Hannatu. Wasu suna kin ka tare da kaddararka, yayin da wasu suke kaunarka tare da kowacce kalar kaddara taka. Wanda duk zai guje ka saboda kaddararka ta munana, to da ma can ba masoyinka ba ne na gaskiya. Amma masoyin gaskiya yana tare da kai duk wuya duk runtsi, babu wani dalili da zai sanya shi nesanta kansa da kai, matukar ba kai ba ne ka kai kanka ga kaddarar da kanka."

Cikin kuka ta ce,
"Abin da Momina ta kasa ganewa kenan, ta dauki tsana a baya ta dora kanki a kan kaddarar da ba ke kika gayyato wa kanki ita ba. Ga shi nan ai, wallahi har da alhakinki..."
A bakinta na dora yatsata alamun ta yi shiru,
"Komai ya riga ya wuce Hanna, ki daina tayarwa. Ni dai gare ni na yafe wa Anti Khadija. Ina fatan hakan zai zama izina ga mutane masu kokarin haddasa fitina a tsakanin mutane. Ki manta da komai kin ji? Shi kuma Faruk, ki fita batunsa. Allah Ya hada kowa da rabonsa."

Ta daga min kai. Sai kuma cikin muryar kuka ta ce,
"Ina son shi sosai Anti Khairi."
Na sakan mata murmushi.
"Na san kina son shi mana tunda kike zubar da hawaye a kansa. Amma fa ki sani, Allah ba Ya kallafa wa rai abin da ba zai iya dauka ba. Kamar yadda kika kamu da son shi, haka zai fice daga zuciyarki ba ma tare da kin sani ba. Wanda duk zai nuna maka kiyayya a kan wani abu da ya same ka, wallahi ba masoyinka ba ne Hanna."

Ta dago kai ta kalle ni, fuskarta na bayyana nutsuwar da kalamaina suka sanya ta.
"Na gode Anti. Ki taya ni da addu'a Allah Ya zare mun son nashi, don ba abu ba ne mai sauki."
Na amsa mata da
"In shaa Allahu."

Ban bar dakin ba har sai da na tabbatar da ta samu nutsuwa sun ci gaba da hira da su Nusaiba.

A bedroom na iske Haidar, yana ganin yanayina ya tambaye ni me ya faru?
Cikin sanyin murya nake shaida masa.
"Na yarda duk abin da ka yi wa wani sai an yi maka, ko kuma a yi wa naka. Wannan alhakina ne yake bibiyar Anti Khadija. Amma ni Allah ma Ya sani na yafe mata tun ma kafin jiyan da ta roki yafiyata. Tun daga lokacin da na tabbatar da Hannatu 'yarta ce, na ba kaina amsar Allah ne ya gwada mata iyakarta. Na kuma sa a raina na yafe mata tun daga kasan zuciyata. Ita kanta Hannatu yanzu abin da take fada kenan."

DARE DUBUWhere stories live. Discover now