Page 42- Ruwan Zuma

151 20 0
                                    

Page 42

Simple breakfast na hada mana. Bayan mun karya ya ce zai je asibiti, babu halin bin sa saboda abin da ya faru, ko ba komai tafiyata ba daidai take ba, sannan ga kunya, gani nake kamar duk wanda ya kalle ni zai gane abin da ya faru.
Na hada masa soyayyar doya da kwan da na zuba wa su Mami a warmer, sannan da flask mai dauke da shayi mai kayan kamshi.

Har gaban mota na raka shi, sai kallo na yake yana min dariya wai tafiya ta kafa a bude. Takaici na ji na hau dan bubbuga kafa.
"Allah ni dai ka daina..."

Dariya sosai yake yi ya ce
"Ki zo mu je ki duba Mamin mana..."
Dariyar ta ci karfinsa. Na kuwa zari fork daga cikin kwando na kwada masa a kafada. Ya dafe wurin har yanzu yana dariya.
"I love you."
Ya fadi cikin muryar dariyar. Na ajiye kwandon a bayan mota sannan na rufe masa.
"Bari in wuce. Idan akwai wata matsala just give me a call."
Na jinjina masa kai.
"A dawo lafiya. A yi wa Mami ya jiki."
"In shaa Allah."
Ya fadi hade da kunna motar ya fice.
Bayan ya fita na je zan rufe gate din amma ya ce in bari saboda yanayin jikina. Shi da kansa ya dawo ya rufe tare da jaddada dole ma ya dawo da masu gadinsa na Office da ya sallama, a cikin kwanakin nan.

Sai da ya tafi sannan na dawo ciki. Dakinsa na fara zuwa na gyara, na bade shi da turaren wuta sannan na dawo nawa dakin na gyara, na gyara kitchen da parlor, a take gida ya dauki daddadan kamshin nan dan kullum.

Ko da na zauna kuma sai na fara tunanin da wane ido zan kalli Mami da Nusaiba, don na tabbata Haidar na fada musu ba ni da lafiya dole za su gane dalilin ciwon.
Daki na koma na dauko wayata, na yi kewar Ummana da kannena, na latsa kiran Umma.
Bayan mun gaisa ta kara min da nasiha sosai, kafin na ba ta labarin abin da ya faru jiya da yadda Mamin ta kyari Anti Khadija.
Ta ji dadi kwarai ta ce,
"Karfin addu'a ce kawai Khairi. Ki ci gaba da dagewa, ba a sanya a wannan zamanin."
"In shaa Allahu Umma. Ina su Sadiya?"
"Na aike su amma na san suna hanyar dawowa. Anjima zan tura su asibiti sai su duba Mamin taku. In ya so ko daga baya ni sai in je."
"Mami me zai hana ku je tare?"
"In bar gidan a wa?"
Ta gaggauta tambaya ta.
"Yanzu ai an daina yayin barin gida babu kowa Khairi; gidaje irin namu da komai yake bude babu wani tsaro. Ki dai bari ko daga bayan ni sai in je."
"Shi kenan Umma. Allah Ya ba da iko."
"Amin. Ki gaishe da mai gidan."
Na ji kunya kawai na kashe ba tare da amsawa ba.

Nusaiba na kira, bayan mun gaisa na tambaye ta jikin Mami, ta ce,
"Da sauki sosai Aunty Khairi. Tun dazu take jajenki sai ga Yaya ya iso yanzu ya ce bak'i za ki yi shi ya sa ba za ki samu zuwa ba kila sai zuwa dare idan sun tafi."
Wani irin sanyin dadi na ji. Allah Ya sani da ma ban san hujjar da zan bayar ba amma sai hakan ya yi min dadi kwarai.

"Eh in shaa Allah. Amma mun yi waya da Umma ta ce su Sadiya za su zo anjima."
"To shi kenan Aunty Khairi. Sai sun zo."
"Ki gaishe da Mami, ki ce ina mata ya jiki, kafin mu zo."
"Okay zan fada mata. Bye."
Na yanke kiran.

Kallo na kunna, amma bakidaya hankalina ba ga kallon yake ba, ya tafi can tunanin duniya, ta yadda Allah ke canja komai a lokaci guda. A sadda Ya ga dama. Hakika babu abin da addu'a ta bari; tana juya kaddara, ko kuma ta sassauta ta.
Duka-duka ban fi shekara ba da na kasance a hannun 'yan garkuwa da mutane. Daga nan aka samu wasu mugaye daga cikinsu suka haike min, na dawo na fara jinyar zuciya da ta gangar jiki. Da na warke na shiga hargitsin karatu inda da kyar Allah Ya daidaita min komai na fada aikin jami'an tsaro na DSS. Na fara gwagwarmayar shiga kauyen da ban taba mafarkin zuwan sa ba, na yi rayuwa a ciki har da soyayya da wanda bai dace da ni ba. Bayan nan na samu nasarar aiki, ta hanyar kokarina aka cafke kaf informers din da ke wancan yankin, sannan na dawo gida.
Yau ga ni na wayi gari a gidan Aliyu Turaki, mutumin da ban taba mafarkin samun ko da wanda bai kai shi ba, sai ga ni a yanzu ina amsa sunan matarsa, mun zama daya ni da shi.
Na saki sassanyan murmushi tare da godiya ga Allah buwayi gagara-misali.

DARE DUBUWhere stories live. Discover now