Page 11- Kewa

160 25 0
                                    

Page 11

***
Takardar na bude a hankali na hau karanta abin da yake cikinta;
Rashin ganin ki sannadi na tunanina, ya jefa zuciyata a cikin kunci.
Ba na iya bambance dare koko rana, So ne ya sa ni kun ga ba na iya bacci.
Kin kore yunwa sam ba ta tsarina, Kallon hotonki shi ya zam minni abinci.

Sai na sanya alamun rufewa, sannan a wani layin na rubuta;
Ni da ke kamar Laila Majnun muke, ko da mutuwa ta zo ba ta dau daya ta bar daya ba.
Haka na fada, ke kamar raina kike, in har babu ke, ba za na yi numfashi ba.
Ruwan zuma soyayya
Da kin ka sha ni kika baiwa
Na koshi sam ba ni da yunwa
Magauta kin sa su a kunya
In babu murna da akwai damuwa
Da ni da ke jininmu yai haduwa
Har abbada bamu batun rabuwa.

Sannan layi na karshe wakar Turanci ce;
If you were my girl, I'll take you round the world
I'll take you places where you've never ever been before
So give me your hand, I'm giving you my world
I promise I'll be loving you forever and ever
I love you forever
I'm giving you my word.

Ban san sadda na kankame takardar a kirjina ina fashewa da wani irin narkakken kuka ba. Hakika mutuwa ta yi min yankan kauna, ta raba ni da wadda na jima ina ikirarin ba zan iya numfashi ba idan babu ita.
Mahaifina ya rasu a lokacin da na fara yin wayo, amma mutuwar Ummu jin ta nake kamar ba a taba yi min mutuwa ba sai a kanta, ban sani ba ko don shakuwar da ke tsakaninmu ce ba, bacci kawai ke raba mu a kowacce rana.
Ummu garkuwata ce, ba ta taba ganin abun cutarwa zai same ni ba ta tsaya ta kare ni ba.
Ummu madubina ce, komai nata abun a kalla a yi koyi ne.
Ummu Malamata ce, abin da duk ya shige min duhu kafin in tinkari kowa wajenta nake zuwa kuma ta fahimtar da ni.
Ummu komai nawa ce, idan na ce komai, ina nufin komai din.

Na share kwallana, ina tuna lokacin da ta shigo gidan ta same ni da harara, sai kawai na fada a jikinta ina jin kewarta na tsananin shiga ta.

"Kin tafi kin bar ni da kewa Ummu."
Harara ta ta kara yi kafin ta ce
"Karyar banza kike yi Khairi. Idan har kin yi kewar tawa me ya hana ki bi ni gidanmu? Ina can ina tunaninki amma ke da alama ko a jikinki tunda ba ki neme ni ba."

Na sakan mata murmushi,
"Ba haka ba ne wallahi. Kin san Umma ba ta nan ta yi tafiya. Kanwarta Anti Marwa da ke zaune da mu kuma ba mazauniya ba ce kullum ba ta nan, kuma ta hana ni fita wai sai gobe ne ba za ta fitan ba sai ni in je wurinki. Ina nan ne amma rabin hankali da tunanina duk yana wurinki Ummuna."

Ta yi murmushin ita ma.
"Na ji to. Na ga kalaman fadanci sun shige ni. Amma ki sani matukar ba ki raba ni da zancen Yaya Nasir ba to mun dinga fada kenan."

Na kama hannunta na ce
"Na yi alkawarin ba zan sake yi miki zancensa ba. Idan ya sake tsoma ni a maganar ma zan ba shi hakuri tunda dai ba kya son shi ya hakura ya nemi wata."
"Yawwa ko ke fa."
Ta fada tana fadada murmushinta. Shi kenan sai muka manta da komai muka ci gaba da nishadinmu kamar koyaushe.

***
Ninke takardar na yi a lokacin da na dawo daga tunanin da na fada, na je na bude wata tsohuwar jakata na ciro takarda da biro, na fara rubutu.

Ina kewa, ina kewar masoyiya
Ina kewa, ina kewar aminiya
Abokiyar shawara
Ke ce kin dara
Kin san in ba da ke ba, sai in hakura...

Sannan a karshe na dora da;
My love, I think of you tonight
'Cause I no dey by your side
Just wait a little while, yeah
Know that I'm alright
And I'll see you soon
Make you wait for me, my dear.

DARE DUBUWhere stories live. Discover now