Page 20- Plan

132 26 0
                                    

Page 20

Jiki sabule na koma gida, kai tsaye dakin Amarya na wuce, da kyar na iya hadiyar ruwa don shi ma kansa dacinsa na ji, na canja kaya na nufi wurin dutse don tuni na tura wa Oga duk recording din da na yi na maganganun Mallam Shamsu.
Ina zuwa sakunana suka fara shigowa, a take nawan ma ya isa gare shi.

Ganin kamar ba ya kusa ya sanya ni kiran sa, kiran na shiga ya latse don ya san kwanan zancen. A take sai ga blue ticks guda biyu alamun ya bude sakon kenan.
Ya dan jima da budewa kafin ya kira ni, ya ce
"Kin dan so ki yi kuskuren tafiya ba tare da kin ba shi tabbacin ba za ki taba fitar da zancen ba. Amma babu komai, ba a makara ba. Gobe idan kin je ki fada masa za ki adana sirrinsa, sannan ki karbi tayin soyayyarsa."

Ya dan yi murmushi a wannan gabar. Sosai murmushin nashi ya ba ni mamaki, don bai da alaka da maganar da muke yi. Kafin kuma  ya ci gaba da cewa
"Maganar Aysha ce ta dan tsorata ni, kodayake abin da muke ta so kenan, amma ba ita na so a dauka ba ke na so. Saboda za ki fi ta sanin abin da za ki yi tunda da ke aka tsaro zancen tun farkon. Saboda haka tana dawowa ki ce na ce ta kama hanya ta bar garin cikin gaggawa."
Ni kaina ba na so wani abu ya samu Aysha a kan abin da ba ita ce ya kamata a ce ya shafa ba.

"Kar ki sake bugun cikinsa a kan kowacce magana, ba na so ya zargi wani abu game da ke. Duk sadda ya sake dauko wani zancen ki nunar masa ma ba kya son ji har sai idan shi ya dage lallai sai ya fada miki. Tunda shi mun samu tabbacin nashi, sauran ma duk za su fito. Ta hanyarsa za mu samu abin da muke so da izinin Allah."
Ya dan yi shiru, sannan ya ci gaba da cewa
"Ita kuma matar maigari da ya ce akwai ta a lissafi, ya kamata a ce by now mun gane ko wace ce, amma babu komai. Yanzu dai ki samu ki fada wa Aysha ta tafi, ba na so ta kara kwana a garin nan."
"Okay Sir, in shaa Allahu yanzu zan koma makarantar in sanar da ita."
Ya yi gaggawar tarar numfashina,
"A'a kar ki koma, idan kin koma zai iya ganewa. Ki bari har sai ta tafi, kin tabbatar da ta iso ma sannan ki fada masa ke kika ce ta tafi. Kada ma ya yi tunanin kin boye masa ne. Gara ya ga komai kina yin sa openly ta yadda ba zai taba zarginki ba. Ina fatan kin gane lissafin."
"Yes Sir."
Na ba shi amsa.

"Ki je, ki jira har ta dawo. Kafin ta dawo din ki tattara mata kayanta. Ki ce ta fada wa Maigari da matan gidan, an yi mata rasuwa ne tafiyar gaggawa ta kama ta."
"Okay Sir. Sai anjima."

Ya yanke wayar, ni kuma na koma cikin gidan, ina jinjina wa kwakwalwa irin ta Oga Ahmad, lallai aiki sai mai shi.

Bayan na koma gida ba da jimawa ba Aysha ta dawo ita ma, ta tarar kuwa na hada mata komai, na yi mata bayanin yadda muka yi da Oga Ahmad.
Ba ta wani tsaya bata lokaci ba, na raka ta har fada, a can ta tarar da Maigari ta yi masa sallama, ni kuma na raka ta har inda za ta samu abun hawa.

A cikin wannan daren sam ban yi bacci ba sai faman tufka da warwara nake yi, mamakin lamarin duniya ya ishe ni.
Kamar wasa sai na fara jiyo motsi, irin motsin da na ji ranar da na fara kwana a garin, kamar ta san a yau din nan ne na fi bukatar fitowar ta.

Sai kuwa na mike ni ma, na isa bakin taga har sai da na tabbatar da ta fice sannan ni ma na nufi fitar, amma cikin rashin sa'a sai na dan take hannun Farida har sai da ta farka. Ina cikin tunanin mafitar yadda zan iya idan Amarya ta tambaye ni ina zan je, sai kawai yarinyar ta koma bacci. A hankali na ci gaba da takawa, don yau so nake a yi uwar-watsi, ko ni ko ita. Ko ma ta halin yaya so nake in ga fuskarta, in tabbatar da wace ce saboda lamarin ya zo min da sauki.

Na janyo kofar na rufe a hankali, na ci gaba da tafiya har sai da na isa bakin kofar soro, sannan na dakata ina dan lekawa tare da kasa kunnuwana ko akwai abin da zan iya tsinta. Na kuwa ci sa'a, saboda yanayin shirun da garin ya yi, hatta kukan tsuntsaye babu, sai sautin cida da ke dan tashi a kai a kai saboda hadarin da ke garin.

DARE DUBUWhere stories live. Discover now