Page 16- Daren Farko

166 32 2
                                    

Page 16

Sai da aka dauki sati hudu cif muna hannun 'yan garkuwa da mutane amma shiru ba wani labari. Da alama har a lokacin cinikinmu ake yi tamkar wasu kaji ko raguna.
Kayan abincinmu tuni sun kare amma sai cewa Zaki ya yi wai mun yi saurin cinyewa, don haka ba za a ba mu wani abincin ba sai dai garin kwaki da gishiri.
Ko mai babu ballantana kuli-kulin cinsa. Kuma a hakan dole shi muke ci tunda ba mu da wata mafita ko zabin abin da za mu cin.

Rayuwa ta yi mana zafi, komai ya kife mana, mun zube, mun lalace. A lokacin da al'ada ta zo mana kuwa, lokacin ne muka dandani wani abu wai shi rashin galihu; don ko audugar mata babu wadda za mu tsaftace jikinmu. Kallabin kayana shi muka dinga yaga muna amfani da shi har sai da muka gama. Sannan da wando guda daya tal, tun wanda aka sace mu da shi a jikinmu. Sai dai idan mutum ya cire ya wanke da jikarsa ya mayar a jiki. Tun muna kyankyami har muka daina, muka rungumi rayuwar a yadda ta zo mana.

A cikin wannan halin ne ciwo ya zo min, wani irin zazzabi da ciwon kai, wannan ciwon kan da nake yi a wadansu lokutan wanda ba ya sauka, har asibiti aka taba kai ni amma ba a gano sanadinsa ba.
Na sha matukar wahala, saboda babu kula, daidai da paracetamol kwaya daya ba a taba kawo min ba, kuma Lanty ta zo ta gan ni a cikin ciwon na kuma tabbatar da ta fada musu.
Wahala sosai Ummu ta sha da ni, don har abinci a baki ta koma ba ni, wanka ita take kama ni ta kai ni har bakin toilet din, ta zuba min ruwa a bokiti bayan ta wanke toilet din tas, sannan ta ce in shiga in yi. Kuma tana nan tsaye tana jira na har sai na gama ta kama ni ta mayar har dakinmu da muka kara yawa zuwa mu shida, ta shafa min mai sannan ta ba ni kayana in mayar.

Tsananin wahala sai da ta kai ta kawo har hannuna wahalar dagawa yake yi min, zazzabi ya ci ni ya cinye duk na zube na lalace. Fuskata kuwa sai manyan idanuwa da katon kai ne kawai ke da auki a ciki.
An saki budurwar nan da karamar yarinyar da na ji an ce miliyan biyar aka biya kudin fansarta saboda iyayenta masu kudi ne.

Ranar da Lanty ta zo ta kawo mana kayan abinci, cikin tsawa ta ce
"Ke kuma gara ma ki gayyato wa kanki kuzari da karfin hali tun wuri, don idan Oga ya gane kina neman zame wa mutane liability sunanki sorry. Wallahi kashe ki za a yi kowa ma ya huta."

Jin hakan ba karamin tsorata mu ya yi ba. Tun daga nan sai kuwa na gayyaci karfin halin, na dinga tafiya da kaina duk da ina yi ina zama in huta ko daga dakinmu zuwa bandaki. Sannan na rage kwanciya. Wata mata ta ba ni shawarar in yawaita shan ruwa saboda shi ruwa waraka ce ta dukkan komai, musamman tun da safe kafin in ci komai. Cikin ikon Allah kuwa sai sauki ya zo, a hankali na fara warkewa har sai da na gama warkewar tas.

Ranar da muka cika wata biyu cif a hannunsu aka sake kiran mu a kan Oga na son ganin mu. Kyakkyawan mari ya dauke Ummu da shi, yana kokarin dawo da shi fuskata Ummu ta yi saurin zubewa kasa. Cikin kuka ta ce
"Na roke ka don Allah kar ka mare ta, ka juye duk sauran marukan a fuskata, Khairi na da matsalar ciwon kai, ban san me zai iya faruwa ba idan ka dauke ta da wannan zazzafan marin naka mai dauke ji da ganin mutum na wucin-gadi."

Sosai na ga karfin halin Ummu, ta yadda har ta iya samun kwarin guiwar yi wa Ogan kidnappers irin wannan maganar.
Bai fasa marin nawa ba, sai da ya dauke ni da shi guda biyu, sannan ya yi wa Ummu guda hudu bayan wancan na farkon.

Tashin hankali wanda ba a sa masa rana, ji na yi tamkar duniyar ce duka ke juyewa saboda azabar da ta shige ni, na fashe da wani irin narkakken kuka, irin wanda ke tasowa tun daga cikin zuciya yana ketowa ta tsakanin idanuwa. Haka Ummu ma, duk azabar da take ji, hakan bai hana ta rike hannuna ba tam, a tunaninta hakan zai rage min radadin marin da ya shige ni.

DARE DUBUWhere stories live. Discover now