Page 22- A Week To Go

163 28 2
                                    

Page 22

Mun jima a haka, har ta ji tsoron kallon nawa ta kara sunkuyar da kanta amma na sake dago shi da karfi, sannan na ja hannunta na kai ta can bakin soro don ma kar wani ya jiyo maganganunmu.

Yatsun nata da ke cikin hannuna na matse da karfi, ta ji zafi amma ba bakin fasa ihu, sannan na sake murzawa na sake su. Na sanya kafata na murje yatsun kafarta da ko takalmi babu, a nan din ma ta ji zafin saboda yadda take tsuke baki alamar zafi ya shige ta.

"Kin ji kunya wallahi!"
Na fada ina mata matsiyacin kallon nan.
"Ba sunana Safina ba, sannan ni ba 'yar bautar kasa ba ce kamar yadda kuka yi tsammani. Ni jami'ar tsaro ce ta fararen kaya, na zo yin aiki ne a kauyen nan, tare da zakulo mutane ire-irenku."

Bakidaya gabban jikinta rawa suke yi, kamar a ce mata kyat! Ta sheka da gudu, sai dai ko kadan rikon da na yi mata ba zai ba ta damar hakan ba.

"Ban san ke wace irin mata ba ce ba, wadda ta tsufa amma ba ta san ta tsufa ba. Ki duba ki gani, duk gidan nan ke ce babba, kin fi kowa shekaru. Kina tsammani za ki maimaita adadin shekarun da kika dauka a duniya?"
Ta yi shiru, cikin tsawa na ce
"Ki yi magana mana!"
Ta gyada kai cike da tsoro.
"To me ya sa ake hada baki da ke a yi zalunci? Anyway, duka ba lokacin wannan ba ne, akwai lokacin da za ki magantu yadda ya kamata."

Na sake tsuke fuska, na dago fuskarta yadda za ta kalle ni sosai, ta ga yadda babu ko dison imani a ciki, na ci gaba da cewa,
"Ko da wasa kar in ji maganar nan a bakin wani, ke! Kar ma ki sake fita daga cikin gidan nan har sai sadda na ba ki izini. Ki sani cewa na jima ina bibiye da dukkan motsinki, har fitar da kike yi cikin dare. Kin ga kenan duk sadda kika sake fita zan iya sani.
Ba ma dare kadai ba, har da safe ko da ranar kar ki sake barin gidan nan.
Ki sani Azumi, fitar ki daga gidan nan daidai take da fitar numfashinki!"
Da karfi na buge mata haba har sai da hakorinta na sama da na kasa suka hade wuri guda, take sai ga jini ya fito.
Na ce
"Kin ji ni ko ba ki ji ba?"
Ta daga kai cikin sauri.
"Ba da ke nake ba? Ba za ki bude baki ki yi min magana ba?"
"Na...na ji..."
Ta fada da rawar murya.
"Idan kin so ki bijire wa maganata."
Daga haka na sake murje mata kafa sannan na koma daki na rufe, ina jin wani irin sanyi a cikin zuciyata. Abu biyu ne ya faru da suka sanyaya raina, na farko, jin babu zargin Aysha jami'ar tsaro ce, sannan na biyu, abin da na jima ina son tabbatarwa ya tabbatu a yau din nan, sannan tsoron da na gani shimfide a saman fuskar Inna Azumi, ba kadan ba ya faranta raina.

Washegari ban ko samu na fita makaranta ba duk da yadda nake son magana da Shamsu, so nake in ga gudun ruwan Azumi, tun shekaranjiya na ji abokan zamanta na mata tunin zuwa barkar wata diyarsu da ta haihu, har ga shi yau suna. So nake in ga za ta fitan ko kuwa dai maganata ta shige ta?
Ina nan zaune har rana ta fito sannan na nufi wanka. Bayan na fito na shirya cikin doguwar rigar atamfa na fito tsakar gidan.

Dukkansu matan biyu sun shirya fita amma ban da Azumi da ke zaune ta rafka uban tagumi, zuwa na wurin ya sanya ta shan jinin jikinta.

"Yaya Azumi ke kadai fa muke jira, da kin shirya dan mu je mu dawo da wuri, tunda kauyen Banga ba nan kusa ba ne, tafiya ce a gabanmu ba kadan ba kuma da kafafuwanmu za mu yi ta."
Daya daga cikin matan ta fada ganin yadda Azumi ba ta da niyyar tashi ta shirya.

Sai da ta dan saci kallo na kafin ta ce
"Ku je kawai Barira, ba na jin dadin jikina tun jiya nake gudawa, kar mu je a hanya ya kama ni kuma."

Amarya ta gyada kai, yanayinta ya nuna alamun tausayi, ta ce
"Tun da safe na lura yanayinki babu kuzari, ashe jikin ne babu dadi. Allah Ya kara sauki."
"Amin."
Azumi ta furta tana kara satar kallo na dan tabbatar da ina gani ko ba na ganin ta?

DARE DUBUWhere stories live. Discover now