Page 28- Next Assignment

151 28 1
                                    

Page 28

Da daddare sai ga kiran Oga Ahmad ya shigo wayata, na yi mamaki saboda shi da kansa ya ce an ba ni hutu in fan warwarewa daga wahalar kauyen da na sha kafin in koma aiki.
Bayan na dauka da sallama a bakina na gaishe shi ya amsa, sai kuma ya yi shiru, ni ma na yi shirun ina jiran jin abin da zai fada.
Sai da ya nisa sannan ya ce,
"Mun zauna sosai muka tattauna da shugaban kidnappers din nan, inda ya fada mana manyan 'yan sanda guda biyar da suke hadakar aiki tare, ta hanyarsu ne ma suke samun makamai.
Sannan akwai wani babban maikudi dan siyasa da shi ma ubangidansu ne; Honorable Nuraddeen Sani Danya."

Cike da wani irin mamaki na zaro ido tamkar a gabansa nake, na ce
"Sir, Nuraddeen Danya dai da na sani?"
"Shi fa. Dukkanmu nan babu wanda bai yi mamakin jin sunansa ba. Kuma dai ba karya suka yi masa ba tunda sun ba mu tarin hujjoji ciki har da hotonsa a lokacin da suke wata tattaunawa tare da su."

Na yi mamaki sosai jin wannan sabon al'amari. Shamsu ya taba fada min akwai wani dan siyasa da yan sanda da suke tare da kidnappers din, amma ban taba kawowa a raina Nura Danya ba ne, saboda yadda yake da taimako ga al'umma.

"Mutum mugun icce ne Khairi. Wallahi na kara shan mamakin mutanen yanzu."
Na yi shiru kawai ina saurarensa. Ya ci gaba da cewa
"Sai dai wani abun mamaki, wai ba su suka kashe 'yar'uwarki UmmulKhairi ba."
"Ba su ba? Wa ya kashe ta to Sir? Ya aka yi suka gane wacce kake nufi?"
"Wallahi wai ba su ba ne. Sun gane ta sarai saboda ke. Wai bayan abin da yaran nan suka yi miki, ashe sun sha cases, saboda su a tsarinsu babu raping, to kuma su din sai suka aikata. Daya daga cikin wadanda ba su samu damar haike miki ba ne ya fada wa Ogansu.
Wannan case da suka sha shi ya janyo suka rike ku sarai ke da 'yar'uwarki, shi ya sa ina kwatanta masa ku ya gane. Ya kuma ba ni tabbacin mutuwar ta ba ta da alaka da su, don bayan sun karbi kudin fansarta, barin wurin ma suka yi. Abun mamaki wai bai ma san ta mutu ba fa, duk zatonsu tana raye."
"Ikon Allah!"
Kawai na iya furtawa ina tunanin to wa ya kashe Ummu?

"Anyway, duka ba wannan ba ne dalilin kiran ki ba. So nake ki ba ni dama in zo gaishe da Ummanmu, in kara ba ta labarin irin kokari da jajircewar diyarta wurin aiki."
Kwarai nake mamakin halin encourage din Oga Ahmad, musamman kuma a kaina. Na yi shiru ban ba shi amsa ba sai ji na yi ya ce
"Kika yi shiru, ko ba za ki ba ni daman ba ne?"
Na kirkiro murmushi,
"Wace ni Sir. You are welcome Yallabai. Ko gobe ka zo I will be happy."
Bayyanannen murmushin shi ma ya saki, kafin ya ce
"Na gode to. Ki tura min da address din probably gobe in zo. And guess what? Na bai wa Mamina labarinki da kwazonki. Ita ma ta jinjina miki."

Har muka gama wayar ban daina mamakinsa ba. Duk da ya ce zai zo ne ya gaishe da Umma amma me ya sa sai ni ce kawai zai zo gidanmu? Ita ma Aysha ta yi nata kokarin, tunda rayuwarta sai da ta shiga hatsarin da tawa rayuwar ma ba ta shiga ba ta silar aikin. Sannan ya ce ya fada wa mahaifiyarsa, shin har na yi matsayin da zai ba Maminsa labarina?

Ko da gari ya waye na fada wa Umma batun zuwan nashi murmushi kawai na ga ta yi. Ta tambaye ni,
"Yana da mata ne?"
Na dan yi shiru, don ni ban ma sani ba. Sai kuma can na tuna ai ya taba fada min ranan da ya kusa kade ni da mota wai yana sauri ne matarsa tana labor kuma har yaron ya rasu, amma daga nan bai kara ce min komai a kai ba.
A takaice dai ban sani ba, kuma amsar da na ba Umma kenan.
Daga nan babu wanda ya sake fadin komai har zuwa sadda ya kira ni ya ce bayan la'asar zai shigo.
Safra da Sadiya suka hau aikin tarbarsa har da su zobo da chinchin.
Ina ta kallon su har suka kammala, na dubi Safra da ke ta rawar jikin hidima na ce
"Wai sai wani rawar kafa kuke sai kace saurayina aka fada muku zai zo."
Dan murmura ido ta yi ta ce
"To da fa waye idan ba saurayin naki ba? Ai Yaya Khairi kin dai san Ogan wurin aikinku ba zai zo gidanku ba sai da wani boyayyen al'amari a zuciyarsa ba ko? Idan batun aiki ne a Office za ku yi shi."
Bayyanannen tsaki na yi, ban ga ta yadda Oga Ahmad zai iya so na ba don babu hadin danga da garafuni. Ya fi karfina fintinkau, sannan ni din nan dai ce Khairi, wadda kidnappers suka taba sacewa, wadda suka haike mata. Ni din dai ce wadda ba budurwa ba, ba kuma bazawara ba.

DARE DUBUWhere stories live. Discover now