Page 21- Suspect

160 32 0
                                    

Page 21

Da fita zan yi in tabbatar wa idona amma sai na zauna dai gudun kar a zargi wani abun daga gare ni. Ina jin yadda yaran ke tsorace da alama an saba yi musu allurar riga-kafin ne kuma suna jin tsoro sosai.
Na ji matar da suke kira da Inna Azumi ta ce
"Yara gara ma ku sanya wa zuciyarku salama don duk guje-gujen nan ba shi zai hana a yi muku allura ba. Kun fi kowa sanin halin mahaifinku, shi yake yi wa masu allurar ma masauki, sannan ya taya su shelanta wa mutane a kan su turo yaransu a yi musu allurar riga-kafi, to kuwa ta yaya za ku yi tsammanin za ku ketare ta?
Ko wancan karan dai ba yadda ban yi da shi ba a kan a rabu da ku ko dan Khalifa da ke ta kuka amma ya tilasta sai an yi din."

Haka dai suka dinga ce-ce-ku-ce da sauran matan, yaran kuwa ba su fita ba don na ji sun ce a nan masu allurar za su kwana sai washegari ne za a yi.

Mikewa na yi bayan na yafa mayafina, ina da bukatar yin magana da Oga, don haka na gaggauta fita ba tare da ko tanka wa matan da ke tsakar gidan ba na fice zuwa wurin dutsen yin waya.
Tun kafin ma in isa wurin dutsen idanuwana suka shiga cikin na Sagir, shi din dai ne sanye da fararen kaya irin na malaman asibiti masu yin allura, sannan ga wasu su uku ma daban duk da irin kayan, hannuwansu rike da wasu manyan robobi da ke dauke da kayan aiki.
Bai ko nuna alamar ya gan ni ba ballantana ya nuna ya san ni, ni ma din kuma haka, na fauze kawai hade da fiddo wayata na latsa kiran Oga.

Bayan ya dauka, ba mu ko gaisa ba ya ce
"Sagir ya iso, ya zo a yanayin da ba ki fahimta ba ko? Na san haduwa da shi za ta yi miki wahala amma mun riga mun gama tsara komai. A makarantar da kike aiki za su yi nasu aikin su ma. Ki fita da wuri, idan kin je shi zai yi abin da ya dace. Dukka aikin da zai yi ba zai wuce na kwana biyu ba zai koma Meshe, in ya so a duk sadda kike da bukatarsa sai ya dawo. Na yi tunanin duk wasu hanyoyin da suka dace ne amma babu mai bullewa saboda Aysha da ke hannunsu, a yanzu kusan komai muka yi za su iya dago mu, amma ina da yakinin wannan hanyar, ba za su iya gane komai ba.
Ki je kawai, ki kuma kwantar da hankalinki."
"Okay Sir. Na gode."

Daga nan na koma cikin gidan ina gayyato wa kaina karfin halin da ba na tattare da shi ko alama.

Washegari kuwa da wurin na shirya, ko tsayawa karyawa ban yi ba na goya jakata kawai na fice zuwa makaranta.
Da ma kuma makarantar ba wani tsari gare su ba, tun daga kan malamai har daliban ba su zuwa da wuri, wannan ne ya ba mu damar ganawa da Sagir da wani daga cikin ma'aikatanmu da ban ma san shi ba, da alama a wani garin yake aiki ba cikin Katsina ba. Sai kuma mutum biyu ma'aikatan lafiya daban.

"Hankalina ya tashi sosai Oga Sagir, tun da na ji zancen satar Aysha na gaza aikata komai face tunani."

Ya saki murmushi ya ce
"Everything is going to be alright. Ke da kike jami'ar tsaro kina karaya to ina ga sauran civilian kuma? Sai kin dake fa, wannan din ba komai ba ne. Duk abin da ake son a samu nasara dole ne sai an sha gwagwarmaya kafin a dace. Yanzu dai duk ba wannan ba, ba mu da isasshen lokaci.
Oga ya ce in fada miki kar ki yi wasa da yawo da cellular phone dinki ta aiki, sannan ki dinga ajewa a inda kika san za su yi wahalar gani. Kamar har da sakaci ne ya sanya suka yi saurin gane akwai makamai a jikin Aysha. Wannan 'yar bindigar da ba ta wuce ta sanya ta cikin pant ba ta yaya za ta bari har a gane akwai ta jikinta? Abun akwai daure kai.
To ke sai kin kula sosai dan a yanzu ke ce kadai hope dinmu, muna kuma kyautata zaton za a dace din.
Ki kara shiga jikin Shamsu, so muke mu gane kaf informers din garin nan, kuma ta hanyarsa ce kawai a yanzu nake da yakinin za mu gane din tunda ya riga ya fara ma.
And lastly, ya ce ki daina zuwa neman network idan za ki yi waya da shi, just use your cellular phone za ki samu service a duk inda kike, ki kira shi idan akwai wata matsala, ba dole sai kin tura masa komai ta whatsapp ba tunda shi dai dole sai da service mai kyau."

DARE DUBUWhere stories live. Discover now