Page 06- From God We Are...

209 28 3
                                    

Page 06

Hannuna rike da na Ummu bayan na dauki sabulun wanka guda muka nufi inda aka mana kwatance da bandaki. Shiga na fara yi sai dai da hanzari na fito saboda kazantar da na tarar a ciki. Haka Allah Ya halicce ni da kyankyami musamman na bandaki. Ummu na gani na ta gane dalili, shiga ta yi ta sheka ruwa ta dan gyara shi sama-sama sannan ta yi nata wankan ta fito.
"Shiga ki yi na gyara."
Tunda muka zo sai a sannan ne ta yi magana. Sai na ji wani sanyi a raina, na karbi sabulun na shiga na watsa sannan na fito na tarar Ummu na tsaye tana jira na.
"Kin dauko sabulun?"
Ta tambaye ni. Ni na ma manta, ta shiga ta dauko sannan ta zo muka wuce bayan mun yi alwalla.

Daya daga cikin man shafawar da aka ba mu na bude, muka shafa sannan sai sallah. Bayan gama sallar ma sai da na zauna a wurin na fada wa Allah tare da neman agajinSa AzzawaJalla. Na kai kuka sosai kafin na kishingida a wurin ina tunanin rayuwa.
Ko yaya danginmu suka kare?
Wace irin rayuwa suke cikin bayan batan mu?
Yaya makomar Mama da ba ta da wasu yaran bayan Ummu?
Na tabbata sai hawan jinin Ummana ya tashi, karamin abu ma yana tayar da shi ballantana kuma batan dan mutum, mutum din ma kuma budurwa.
Sai a sannan wasu irin zafafan hawaye suka hau ambaliya a saman kumatuna, kuka nake sosai, irin wanda ke fitowa tun daga cikin zuciyata, jikina sai karkarwa yake yi, ga wani irin zafi da zuciyata ke yi.

A hankali Ummu ta tako ta iso inda nake, bakin hijabinta ta yi amfani da shi ta hau share mini hawayena,
"Ki daina kuka Khairi..."
Kawai ta samu daman fadi ita ma nata hawayen suka fara kwaranya.
Wani irin yanayi ne dukkanmu muka shiga, irin yanayin da duk yadda zan kwatanta shi babu wanda zai taba fahimta face wanda ya shiga kwatankwacinsa.
A rana guda ka wayi gari a hannun 'yan garkuwa da mutane, ban san yadda zan ba da labarin yanayin ba.

Rarrashi na Ummu ke yi sai dai ita ma kukan take yi. Tare muka dinga kukan har sai da muka gaji don kanmu sannan muka daina.

***
Wani irin zafi gami da radadi nake jin zuciyata tana yi a lokacin da na dawo daga duniyar tunanin da na lula. Shin da gaske karshen farincikina ya zo? Wani sashen na zuciyata ya ba ni tabbacin da gaske ne, matukar dai Ummu ta tafin, to ba ni da sauran farinciki ko jin dadi a rayuwata.
Kuka nake son na yi ko zan samu sassauci, sai dai zuciyata ta ki ta ba kwayar idanuwana hadin kai, ko kadan hawayen ya gagara fitowa sai zafin nan da zuciyata ke yi tamkar danyen raunin da aka watsa wa yajin tsidahu.

"Da gaske UmmulKhairi ta rasu, gawarta aka tsinta a bayan gari."
Muryar Anti Maryam ta yi mini shigar suruf a na'urar shige da ficen sautina.
"Ta rasu Khairi, sai dai mu bi ta da addu'a."
Ta nanata min a lokacin da take kokarin hada idanuwa da ni.

"To kin ji UmmulKhairi, takwararki Allah Ya yi mata rasuwa. Na san dole za ki damu, amma dole za ki jure, dukkan mai rai mamaci ne, dukkanmu nan sai mun dandani mutuwa."
Dakta Gumel ya fada cikin sigar rarrashi.
Da fari tsoron sa nake, tsoron duk wani namiji ma. Sai dai a yanzu da yake jaddada mini mutuwar Ummu, wani irin haushi da takaicinsa ne nake ji.

"Ki yi kuka Khairi, kukanki zai taimaki aikinmu ya tafi yadda ya kamata. Rashin fitar hawayenki ba karamin dakile ci gaban da muke son samu zai yi ba."
Jin sa kawai nake yi, amma ban san ta inda hawayen da ke soya zuciyata za su fito ba. Don kuwa idanuwana kamas suke tamkar an soya gyada a cikinsu.

Ya kalli Anti Maryam ya ce
"Ku tafi gida, a kwantar mata da hankali ta dawo cikin nutsuwar ta, sannan ku dawo bayan sati biyu. In shaa Allahu komai zai wuce tamkar ba a yi ba."

A nufinsa, komai din na nufin har mutuwar Ummu? Ban taba tunanin akwai wata mummunar kaddarar da za ta shafe keta haddin da aka yi mini ba, sai dai jin zancen mutuwar Ummu, yadda ya jijjiga komai na halittata, a take na ji batun fyade ya kau, burin da na ci game da wannan aika-aikar da aka yi mini duk ya shafe. A yanzu ba ni da wani burin da ya wuce kwatar wa Ummu fansa, durkusar da wadanda suka kashe ta, da izinin Allah sai na kai su kasa, komai daren dadewa.

DARE DUBUWhere stories live. Discover now