Page 34- Matar Haidar

158 25 1
                                    

Page 34

Yau ma da wuri ya fada min zai tafi, tun kafin sha biyu na hangi motarsa ya fice. Da yawan 'yan office din mamakinsa suke, ta yadda bakidaya ya sauya, ya rage zama wurin aiki, sannan ana ganin sa an san yana tattare da damuwa. Sai dai babu wanda ya ga fuskar tambayarsa dalili.

Sai lokacin tashi aiki sannan na tafi. Na fara sauka gidan Mama na gaishe ta tare da ba ta labarin award din da za a ba ni gobe ina gayyatarta tunda Baba ba ya nan. Ta ji dadi sosai ta ce za ta zo gida wurin Umma goben sai su isa tare.
Ko da na shiga gida na tarar fuskokinsu duk da annuri. Mamaki kwarai ya kama ni musamman yadda Safra ta hau tsokana ta wai amarya. Na share ta kawai na nufi cire kayan jikina na shiga wanka. Ko da na fito doguwar rigar rubber mai bin jiki na saka sannan na tufke gashina da ke kwance har saman bayana, na dora hular turban a kai. Ina kokarin fitowa daga dakin kenan wayata ta yi ringing, ko ba a fada min ba na san Haidar ne saboda karar kiran sa ma daban take.

Ina dauka na ji ya ce
"Baby girl..."
Na nemi bakin gado na zauna.
"How was the Office?"
"Alhamdulillah."
"Sai kika ga yadda komai ya juye ko? Haka Allah Yake lamurranSa Buttercup. Idan kana ta addu'a ka dage ba tare da gajiyawa ba sai Ya ba ka solution fiye ma da yadda ka yi expecting. We have been praying, wallahi tunda na fara soyayya da ke daidai da rana daya ban taba fashin rokon Allah Ya tabbatar min da alkhairin da ke tsakani na da ke ba. Aka zo aka fara issue din can na Anti Khadija, still ban daina addu'a ba sai ma kara dagewa da na yi. Sai kuwa ga shi, Allah Ya nuna mana da tuni Ya gama komai."

Har ya yi maganarsa ya gama ban gane nufinsa ba, jin na yi shiru ya sanya shi fadin
"Duk farinciki ne ko kuwa fargaba ce? Ko dai gajiyar aikin ne?"
"Ban san me kake magana a kansa ba fa."
Na fada cikin sanyin murya.
"Lallai Buttercup, jin dadi ya yi miki yawa ko?"
Na saki murmushi, a kowanne irin yanayi nake idan ya kira ni da sunayen shin nan na soyayya sai na ji sanyi ya ratsa ni.
"Hmm! Wai ma jin dadi. Jin dadi ai yana wurin su Baby boy."
"Ko? Zan jin dai tukunna. Ba ki yi magana da kowa ba ne?"
"Ban yi ba, tunda na shigo dai Safra na tsokana ta wai amarya. Na san ba zai wuce an je neman aure kila an amince a kan an ba ka ni ba ko?"

Ya sauke ajiyar zuciyar da har ni sai da na ji ta. Da annuri cikin muryarsa ya ce,
"Tuni mun wuce wannan matakin baby girl. Daga zuwa neman aurenki Uncle Ibrahim, Yayan mahaifina, da Alhaji Khamis, suka ce idan har Kawu Danladi ya amince a daura auren a take. Don su ba su ga amfanin jan lokaci ba tunda mun riga mun fahimci juna. Irin bata lokutan nan ke janyo surutai da zuga-zugi. Sannan idan Mami ta ji an riga an daura ba ta da zabin da ya wuce rungumarsa da hannu bibbiyu. Kawu Danladi bai yanke hukunci ba har sai da ya kira Umma ya shawarce ta, ya ba ta manyan hujjojin da dole ta aminta, a take aka daura aurenmu."

Tunda ya fara bayanin na tsinci kaina a wani irin yanayi; irin yanayin da kai tsaye ba za ka kwatanta shi ba. Ni dai na san ban ji haushin daurin auren ba, sai dai kuma zuciyata cike take da tsoro da shakkun yadda Mami za ta karbe ni tunda an daura aurenmu ba tare da izininta ba. Sai kawai na ji gumin hawaye, cikin rawar muryar kuka na ce,
"Haidar kana ganin wannan solution ne?"
"Solution ne babba Khairi. Ba kuka ya kamata ki yi ba, godiya za ki yi ga Allah madaukakin Sarki da Ya takaita mana komai aka daura auren nan. Idan kika ci gaba da kuka tamkar kina butulce wa rahamarSa ne. Sai in ga kamar ba kya farinciki ma."

Na sharce hawayena hade da fadin,
"Ina farinciki, sosai baby boy. Kawai dai ina tsoro ne."
"Ki daina tsoro kin ji? Everything is going to be alright. An riga an yi mai wuyar. Ki gode wa Allah."
"Alhamdulillahi."
Na furta amma ban daina kukan ba.

"Ki adana hawayen nan naki baby girl, an jima zan zo, sai ki yi a gabana. Kin ga sai in samu damar shanye su tas, sannan in rarrashe ki, irin rarrashin da ya kamata miji ya yi wa matarsa."
Cikin wata irin murya mai kama da shagwaba na ce
"A'a ni dai kar ka zo."
"Au, yau kuma ba kya so in zo gidanku? Guduna kike yi Buttercup? Yau ni na ga inda mata ke gudun mijinta."
Cikin siririyar murya kamar mai shirin yin kuka na ce,
"Uhm, na ji. Ni dai kar ka zo Allah. Dan ko ka zo ba zan fito ba."
"Sai in shiga har dakin ai in iske ki. Kin san a yanzu dai ba ni da shamaki da ke ko?"
"Allah ni dai..."
"It's okay to. Ki huta sosai na fasa zuwa. Sannan na hutar da ke daga zuwa wurin aiki tukunna, har sai mun ga yadda hali ya nuna. Amma dai dole gobe za ki je ki karbi award dinki. Su Umma su shirya zan turo a tafi da su su ma. Taron karfe goma na safe ne."

Sam-sam wannan zancen bai shige ni ba. Ko zai hana ni aikina na fi so ya bari tukunna har sai bayan na tare, kafin nan na samu mafita, don ba ni da burin zama haka nan, babu karatu babu aiki.
Amma na bar maganar tukunna har wani lokacin don ba na son bata masa mood dinsa da na lura a yanzu duniyar ta masa dadi sosai.

"Ki huta sosai baby girl. Ina gaishe da Umma. Take care."
Ya yanke kiran.

Ko da na fita waje na tarar Anti Maryam da diyarta Rukayya sai karamar mai suna Amra. Na ji dadin ganin su, da fara'a a fuskata na gaishe ta, ai kuwa ta hau tsokana ta wai amarya. Na share da zancen hade da shigewa kitchen na zubo wake da shinkafa da mai da soyayyen kifi na fito.
Umma na ji tana shaida mata duk yadda abubuwan suka juye daga neman aure ya koma daurin aure.

"Da farko ban yarda ba Maryama, don ban shirya ba, Allah na gani ba mu da mataimaki sai Allah. Irin wannan karaf da rugus haka ai masu kudi ake yi wa. To sai da Kawun nasu ya yi min bayani sosai wai ba yanzu za a tare ba har sai sadda muka shirya don kanmu sannan. Shi ya sa na amince a daura. Kuma surutan mutane, ba za a taba fita daga zancen ba idan ba gani suka yi an daura auren ba. Na yarda, na kuma gamsu da cewa duk ire-iren auren nan bai kamata a ja zarensa ba, duk da gaggawa aikin shaidan ce amma ba a ce a gaggauta ba, sai dai kar a mugun jinkirtawa don komai zai iya faruwa."

Cike da farinciki Anti Maryam ta ce
"Ai gara da aka daura Umma. Yanzu kin ga komai ya riga ya wuce. Masu gulma kuwa aikin banza ne ko sun yi don mai faruwa ta faru."
"Haka ne. Sai dai mahaifiyar nan tashi ce har yanzu ba ta sauko ba, da alama sai mun ci gaba da hada ta da Allah sosai, Ya sassauta mana zuciyarta ko Khairi ta ji dadinta. Ba na son aure babu soyayyar uwar miji, bai da dadi sam."
"Tunda dai mijinta yana son ta Umma duk wannan mai sauki ne. Babu dadi don dadi, amma in dai ta kyautata mata sosai da zuciyarta daya, ta kuma ci gaba da fada wa Allah duk komai zai zama labari. Kuma ita danginsa ma suna son ta, ai ko su za su iya shawo kanta nake ga."
Umma ta dan yi jim, sannan ta ce
"To Allah Ya sa."
"Amin Umma. Goben da karfe nawa ne?"
"Goma na safe."
Anti Maryam ta shafi fuskarta hade da fadin,
"Ina da morning duty gobe amma in shaa Allahu zan kira Sista Asmaa ta je, ni sai in je afternoon nata duty din. Ai ba zan bari a yi babu ni ba in shaa Allah."

Daga nan kuma sai aka ci gaba da hira, su Safra na ta murnar auren da aka daura babu shiri. Ni dai har suka yi suka gama ban ce uffan ba. Da na gama cin abincina ma sai na koma daki na kwanta ina tunanin rayuwar duniya.
Kawai sai Ummu ta fado min a rai. Wata rana da take fadin za ta so ganin an daura min aure, ta ga yadda zan kwabe fuskar nan tawa ina kukan shagwaba. A lokacin bige mata kafada na yi ina dariya. Ita ma dariyar ta yi tana maimaita irin shagalin da za a yi ga bikina.
"Ke kuma duk kina nan zaune ba a yi naki ba? Allah Ummu gani nake yi kamar sai kin riga ni aure, kin ga ke danginku suna kula da ku sosai, za su iya sa ido a kanki ba ma lallai mu gama karatun likitan ba a yi miki aure. Ni kuwa fa? Babu idon kowa a kaina. Babu mai taimaka mana da sisi kin ga kuwa babu wanda zai ce in yi aure ko kar in yi har sai sadda na kammala karatuna."
A lokacin dariya kawai ta yi.

Na sharce guntuwar kwallar da ta sauko min, a bayyane na furta
"Yau ga shi an daura aurena Ummu amma ba kya duniyar, kin tafi kin bar ni..."
Na ci gaba da kuka sosai, har sai da na yi mai isa ta sannan na yi shiru.
Wayata ce ta yi ringing na dauka.

"Ban gaji da jin muryarki ba sweet cherry."
Na sauke ajiyar zuciya ina kokarin saisaita muryata da ta dan disashe saboda kukan da na yi.
"Kin ci abinci dai ko?"
"Na ci, ban jima da gamawa ba."
"Good. Akwai maganar da nake son mu yi da ke, amma ban sani ba ko ke kadai ce a inda kike."
Na daga kaina na ga babu kowa a dakin, na ce
"Ni kadai ce baby boy."
"Yawwa. Uncle Ibrahim ya kira yake fada min zancen Umma na maganar su kayan daki da za su kawo tsaikon tarewar ki. Ni kuma ko kadan ba na bukatar a kawo ki da komai Buttercup, ke din dai nake so, ke kawai nake so a kawo min. Ina son yi wa Umma wannan bayanin amma ina gudun kar ta dauka ko don ina so ki tare ne ya sanya na ce kar a yi miki komai, ni kuma Allah Ya sani tsarina ne wannan, ko marigayiya Maryam duk da ba auren soyayya muka yi da ita ba na ce kar a yi mata komai, tunda ni da ke za mu more su ba Umma ba, kin ga ni ya kamata a ce na yi. Duk da already akwai komai a gidan sai dai dole za a sauya su, a yi daidai da zamani, da kuma ra'ayinki."

Wai shin Haidar wane irin mutum ne mai matukar kirki har haka? A wannan zamanin, irinsa kalilan ne. Na yarda da son da yake yi min, na kuma yarda da nagartattun halayensa.


Amrah A Mashi❤️

DARE DUBUWhere stories live. Discover now