Page 48- Kauyawa

123 23 2
                                    

Page 48

Shiga na yi cikin asibitin na kira wata nurse na shaida mata abin da ke tafe da ni. Da hanzarinta ta dauko gadon dora marassa lafiya, ta tura shi muka koma wurin motar. Da taimako na da na Babanta muka dora ta a kan gadon, ba mu ankara ba har muka fama ta ta fashe da wani irin narkakken kuka.

Sannu kawai muke yi mata har muka karasa dakin da ake ajiye su domin jiran likita.
Waigawa na yi da nufin tambayar nurse din wani abu amma sai na ga ba ta nan, sai Anti Khadija ce kawai ta rafka uban tagumi.
Yunkurin ficewa na yi amma sai ta kamo hannuna. Cikin rauni ta bude baki ta ce,
"Na san ni mai laifi ce a wurinki Khairi, don Allah..."

Na gyada mata kai kawai tare da hana ta maganar, na fice daga dakin. Yanzu duk ba lokacin wannan bayanan ba ne, ba su ba ne a gabana.

Babu jimawa sai ga likitan ya zo. Tare da shi muka shiga dakin da wasu nurses.
"Za ki iya jiran mu a nan barrister. Bari mu matsa wurin can in duba raunukan."
Na zauna kan daya daga cikin kujerun da ke jere cikin dakin. Shi da wata nurse suka tura gadon zuwa inda wani labule yake domin duba ciwukan da ke jikinta.

Sun dan jima suna dubawar, fiye fa minti talatin, sai ga su sun turo gadon nata sun dawo da shi inda yake da. Ya dubi Anti Khadija da duk ta zama wata iri, ya ce,
"Baiwar Allah ke ce mahaifiyarta?"
Ta daga kai cikin kuka ta ce,
"E, ni ce."

Gajeren tsaki ya saki,
"Ba ku kyauta ba gaskiya. Kun kuwa san irin raunukan da ke jikin yarinyar nan har sun fara rubewa saboda rashin kula? Wannan wace irin asibiti ce kuka kai ta wadda sam ba su san makamar aikinsu ba?"
Na yi caraf na ce,
"Doctor ai sun dauke ta daga asibitin ne wai saboda gudun abun kunya. Suna tsoron kar zaman asibitin ya janyo tonuwar asirin fyaden da aka yi mata."

Fuskarsa murtuke ya sake duban ta ya ce,
"Ashe a birni ma ana samun irin haka. Ni na dauka tuni an waye an daina ire-iren wadannan abubuwan? Ai ga shi nan a kokarinku na ganin an rufa mata asiri, za ku nakasa mata rayuwa. Wallahi raunukan da ke jikinta ba kanana ba ne, ga dinkin da aka yi mata shi ma babu kula, har ya fara kumbura, nan da lokaci kadan za ta fara wari in da ba a kawo ta nan ba."
Ya dubi nurses din da ke biye da shi ya ce,
"Ku buyo ni zan fada muku abin da za ku fara kafin komai."
"Doctor idan ka rubuta results ina jiran report din ciwukan."
"In shaa Allahu."
Ya fadi hade da ficewa suka mara masa baya.

***

A cikin kwana uku Hannatu ta dan fara samun saukin raunukanta. Har tafiyarta ta fara dan daidaita duk da dai har yanzu da sauran ta. Sai dai rashin walwalar nan har yanzu yana nan, shiru-shiru da ita kamar ba Hannatun nan mai son hayaniya da wasa ba. Bakidaya ta sauya, ko magana ta yi da wuya a gane abin da ta ce saboda a hankali take yi.

Dakin na shiga da file dinta a hannuna, na amsa gaisuwar da Mamanta ta yi min kafin na zauna a bakin gadonta ina murmushi.
"Alhamdulillahi jiki ya fara sauki ko Hannatu? Na gan ki zaune ba kamar kullum ba."
Ba tare da na jira me za ta ce ba na dubi Anti Khadija na ce,
"Za ki iya ba mu wuri mu yi magana? Don ba lallai ta iya fadan komai ba a gabanki."
Ba tare da ta ce komai ba ta tashi jiki sanyaye ta fita.
Na dawo da kallo na ga Hannatun, na janyo sunayen nan da Babanta ya ba ni, sannan na ce,
"Duk abin da na tambaye ki, ki bude baki ki ba ni amsa in dai kin sani Hannatu. Hakan ne kawai zai sanya mu yin nasara a kotu. Amma idan kika yi shiru, kin ga ni ban san komai ba a game da abin da ya faru. Duka-duka kwana uku ne ya rage mana mu shiga kotun. Tuni an tura wa suspects din namu sammaci."
Na dafa kafadarta, cikin karfafa mata guiwa na ce,
"Ina so ki sani Hannatu, wannan abin da ya faru ba shi ne karshen farincikinki ba. Na san ba za ki rasa jin labarin irin hakan ta taba faruwa da ni ba. Amma ina nake yanzu? Hakan ya komar da ni baya? Ba ga ni nan ba a gabanki a matsayin Lawyer, wadda ke kokarin kwatar miki fansa ba? To ki daure kin ji? Ki sanya wa zuciyarki salama, duk abin da kika ga ya faru a rayuwarki da ma can haka Allah Ya rubuta miki. Kuma in shaa Allahu rayuwarki za ta yi kyau kamar yadda tawa ta yi kyau a yanzu, watakila ma fiye da hakan."
Ta jinjina kai, tana kokarin yin murmushin da ya gagara ba ta hadin kai.

DARE DUBUWhere stories live. Discover now