Page 40- Reconciliation

149 23 0
                                    

Page 40

Da wani irin rashin kuzari Haidar ya tako ya karaso kusa da ni. Cikin idanuwansa na kalla, na ga yadda duk suka zurma, zagayensu ya fara yin bak'i-bak'i saboda rashin bacci.
Cikin sassanyar murya ya ce
"Ko za ki zo in mayar da ke gida tunda ga su Salima nan sun zo?"
Na gyada kai,
"Bai kamata in tafi ba don sun zo. Yadda take mahaifiyarsu ni ma haka take uwata. Don haka zan zauna, har sai Mami ta tashi na ga yanayin jikin nata."

Da alama ba ya son yawan magana hakan ya sanya shi kawai daga kai ya koma kan wata kujera tare da hada kansa da guiwa. Bakidaya jikina ya karasa yin sanyi; ganin mutum mai karfin hali irin Haidar a cikin wannan hali, dole hankalina ya tashi. Ji nake tamkar in je in yi ta ba shi baki har sai zuciyarsa ta sanyaya.

Can kuma sai ga Sista Khadija ta zo sanye da fararen kayan nurses da alama wurin aiki za ta wuce. Biye da ita 'yar budurwa ce wadda ko Sadiyarmu za ta iya girmanta; tsakanin shekara goma sha biyu zuwa sha uku dai.
Duk da haushin ta da nake ji hakan bai hana ni gaishe ta ba, sai dai ko kallon inda nake ba ta yi ba ta zarce inda Nusaiba, Aunty Jamila, da Anti Salima suke. Budurwar da ke tare da itan ce ta gaishe ni da murmushi ni ma na mayar mata na karfin hali. Na gane diyarta ce saboda kamar da suke yi, kuma ina jin sunan Hannatu a bakin Nusaiba tana cewa babbar diyar Anti Khadija.

Ganin su ya sanya Haidar zuwa inda nake, ya ce,
"Ba na so ranki ya baci alhali muna cikin alhinin ciwon Mami. Ki zo mu je in kai ki gida, in ya so idan kin kimtsa kin karya sai ki dawo."
Na bude baki na ce,
"Da alama wurin aiki za ta..."
"I insist."
Ya fada hade da yanke min magana.

Dole na je wurin su Nusaiba na shaida musu zan je gida in yi wanka sai in dawo. Kasa-kasa na ji Anti Khadija tana fadin
"Da ma tunda ba uwar mutum ce a kwance ba ai dole a tafi gida. Kodayake ba ma bukatar kingin..."

"Anti Khadija!"
Nusaiba ta fada cikin wani irin bacin rai da bai boye kansa ba a cikin muryarta.
"Wai sai yaushe ne za ki kyale baiwar Allah'n nan ta sarara ne? Sai yaushe ne za ki gane bawa ba ya taba tsallake wa kaddararsa?"

"Watakila sai ranar da na fito mata a mutum, na nunar mata da ina kaunar matata, sannan ne za ta fita sabgata da ta iyalina."
Haidar ne ya yi wannan maganar cikin bacin rai.

"Ya isa! Ya isa haka dukkanku. Haba! Mene ne haka wai? Ga mahaifiyarmu can kwance kan gadon asibiti har yanzu ba mu san a wanne hali take ba amma ku ga ku nan kuna kokarin tayar da hatsaniya a cikin asibiti. Da me za mu ji? Ciwon Mami ko rikicinku?"

Haidar ya dubi Anti Jamila da ta yi wannan maganar. Bai ce komai ba, sai dai ta cikin idanuwansa za a fahimci zafin da zuciyarsa take ciki. Ya ja hannuna ba tare da ko sallama mun yi da su ba muka tafi.

Tun da muka tafi babu wanda ya ce uffan har muka isa gida. Bayan na fito daga mota kai tsaye dakina na nufa. Na shiga na yi brush sannan na sakar wa kaina ruwan zafi saboda gajiyar da ke tattare da ni; ga ta hidimar taro jiya, ga kuma ta kwanan zaune.

Bayan na fito na shafa mai, na bi da body milk din Dukhan by Ayn, sai na ji wata irin nutsuwa tana sauko min, hakika kamshi rahma ne, musamman kuma kamshi irin na Dukhan by Ayn. Duk yadda aka yi wa mutum bayaninsu ba lallai ya fahimta ba har sai idan ya gwada ne zai tabbatar da hakan (+234 808 892 9221).

Doguwar rigar atamfa na saka, ko tsayawa gyara gashina ban yi ba kawai na daura dankwali sannan na hau kakkabe-kakkabe duk da babu wani datti a gidan.
Daga nan na nufi kitchen na ga komai akwai na abinci. Plantain da kwai na soya sannan na dafa shayi mai kayan kamshi na kwashe a cikin flask na kai komai dining na jera.
Daga nan na dora farar shinkafa da dankalin turawa, a gefe guda kuma na dora tafashen naman kaza na zuba kayan kamshi.

DARE DUBUWhere stories live. Discover now