Page 51- Babbar Kotu

121 22 1
                                    

Page 51

Washegari kamar ba zan je office din ba amma dole na daure na je, saboda wani irin zazzabi da ya lullube ni. Ba ni da zabin da ya wuce tafiya saboda abin da ke gabanmu dole ne ma in daure.
A makare na isa, goma saura na safe. Kai tsaye na tinkari office dinmu, ina zuwa na tarar Fa'iz da wani matashi zaune kusa da shi.

"Barka da zuwa Barrister Khairi. Ya aka yi kika makara yau?"
Na ajiye jakata cikin karfin hali na ce,
"Jikina ne ba dadi wallahi, da kamar ma ba zan zo ba sai kuma na tuna akwai abubuwa a gabanmu dole ne sai na zo."

Ya saki murmushi,
"Ai da kin yi zamanki ma wallahi sai mu yi waya."
Na zauna kawai ba tare da na sake furta komai ba. Ya ce,

"Wannan shi ne mai napep din, tun da safe muka yi waya na shaida masa komai, shi ne ya yi alkawarin zai same ni mu yi magana. Ga shi nan kuma ya cika alkawarin ya zo a kan lokaci."

Ji na yi tamkar zazzabin jikina zai tafi, don kaso tamanin da biyar na nema na rasa. Na saki murmushi na ce,
"Barka da safiya."
Ya amsa
"Yawwa, barkanmu."
"Kai ne wanda ka dauki Hannatu a ranar da abin nan ya faru ko?"
Ya daga kai,
"Tabbas ni ne. Ita da takadiran matasan nan. Na so cetonta Allah ma Ya sani na tsorata ne da ganin wukar jikinsu. Shi ya sa baki alaikum na tafi. Amma har ga Allah tana raina, sau da yawa nakan tuna ta in ce ko ta mutu ko ta kubuta? Ina kuma da na sanin rashin gayyato mutane mu je har wurin mu hana su aikata mummunar manufarsu a kanta. To shi ne kuma Barrista ya kira ni dazu ya fada min komai.
A shirye nake da bayar da shaidar gaskiyar abin da na sani."
"Alhamdulillahi."
Na furta a bayyane.
"Na ji dadi sosai wallahi. Allah Ya saka maka da alkhairi."
Ya amsa da amin.
Na fada masa ranar da za a sake zama shari'ar da kuma lokaci.
Daga nan ya tashi ya tafi bayan mun kara yi masa godiya, Fa'iz har gaban kekensa ya raka shi, ya ba shi kyautar dubu biyu amma firfir ya ce ba zai karba ba, shi don Allah zai yi ba don wani abu ba.
Hakan ya kara faranta raina, na samu nutsuwar zuciyata.

***
Kamar yadda muka tsara tafiya ranar Asabar, hakan muka yi. Har gida muka je muka dauki Fa'iz da Hannatu. Yau ma Haidar ne ke tukin har muka isa kauyen da ba mu ma san sunansa ba sai yau, wai Shi Durzum.

A daidai inda muka yi za mu hadu da yaron nan muka dakata. Nan da nan kuwa sai ga su su biyu kamar yadda muka gan su wancan karan.

Bayan mun fita daga motar, suka gaishe mu, sannan ya ce,
"Mu je in raka ku gidansu. Kun yi sa'a suna nan sun dawo jiya."
Raina kal muka bi bayansu. Babu mai cewa uffan har muka isa wani gida da bai da nisa sosai daga wurin.

Haidar ya dube ni ya ce,
"Yadda za a yi, kun ga bai kamata kawai mu afka musu a gida ba, za mu tsorata su. Buttercup ko dai ku fara shiga ke da Hannatu, ko kuma su Garbati su fara yi mana iso su ce ana sallama da mai gidan."
Na daga kai,
"Bari mu shiga din."
"Ba kya tunanin su ki yarda da ku? Kin san halin mutumin kau..."
Sai kuma ya yi shiru yana kallon yaran.

Na saki murmushi.
"Babu abin da zai faru sai alkhairi. In shaa Allah."
Ya daga kai shi ma yana murmushin.

Yaran nan suka yi mana jagoranci zuwa cikin gidan sannan suka tafi. Kalkal tsakar gidan yake ya sha shara. Daga can gefe tabarma ce shimfide amma babu kowa a kai. Muka dinga sallama shiru, can sai ga matar ta fito daga daki tana amsa sallamarmu.
"Lale marhabun."
Ta fada hade da nuna mana tabarma ta ce mu zauna. Babu jimawa sai ga mijin ya fito daga bandaki rike da buta.
"Baki muka yi ne Safare na jiyo gaisuwa?"
Ya furta yana karasowa inda muke.

Na gaishe su cikin sanyin murya na ce
"Ba ku gane wannan ba ko?"
A tare suka kalle ta, kamar matar za ta yi magana sai kuma mijin ya yi saurin gyada kai.
"Ba mu san ta ba. Lafiya kuka zo gidanmu?"

DARE DUBUWhere stories live. Discover now