Page 01- Khairi

556 35 0
                                    

Page 01

A cikin duhun da ya mamaye idanuwana nake jin wani irin zafi gami da raɗaɗi yana tsirga zuciyata. Shin nan ne muhallin da rai yake? Na sha jin ana faɗin babu wanda ya san inda ran mutum yake hatta Malakul-mauti, wato mala'ikan mutuwa. Sai dai a yau na gama tantance inda yake, wato a tsakanin ƙirjina daga gefen haggu, a can ne wurin zaman rai. Ban ankara ba na dinga jin takun tafiya, dum! Dum! Dum! Wanda ya ƙarasa tabbatar mini da hasashena; na mutu, matambaya ne har sun iso domin su aiwatar da aikinsu.

Kamar kar in buɗe raunannun idanuwana, kamar in dawwama da idanuwan a rufe, sai kuma wani irin abu ya dinga fizgar kansa da ƙarfin gaske daga cikin zuciyata, wanda ya sanya ni dole na buɗe raba-da-rabin idanuwan nawa, domin ganin da me suka zo?
Ganin su sanye da fararen kaya ya sanya ni sauke wani irin nannauyar ajiyar zuciya, ina jan hamdala a ƙasan ruhina. Ko ba komai na san na samu rabo a ƙiyama, domin kuwa fararen kaya rahma ne, don haka matambayan nawa da alamar masu rahma ne.
Sake runtse idanuwan nawa na yi, ina jin tamkar an zuba tafasasshen talge a cikinsu, na fara ƙoƙarin muskutawa, sai dai na kasa, saboda wata irin azaba da ta tsirga ta tsakanin cinyoyina.
Ina jin muryoyinsu suna magana, sai dai na kasa jiyo abin da suke faɗi, kunnuwana sun kasa tantance madosar kalamansu, sun kasa isar da saƙo zuwa ga ƙwaƙwalwata da za ta tantance abin da suke faɗi.
Ji na yi ana buɗe tsakanin cinyoyin nawa, a hankali hannu ke isa ga ƙasana, na fasa wata irin ƙara wadda ni kaina ban san sadda na yi ta ba, ban so a ce na kasa amsa tambayoyin kabari ba, sai dai azabar da ta tsirga ni ce ta sanya ni tambayar kaina 'Anya kuwa na samu kyakkyawan rabo?'
"Da ranta!"
Kunnuwana suka jiye mini, wanda a take suka isar da saƙon zuwa ga ƙwaƙwalwata, ta kuma tantance ma'anar kalmomin guda biyu. Da raina? Kenan har yanzu ina duniya? Me nake yi a cikinta? Me ya sa burina bai cika ba?
Da dukkanin ƙarfin da ya yi mini saura na sanya hannuwana guda biyu na shaƙe wuyana, a tunanina wannan ita ce kaɗai hanyar da zan bi domin cika burina. Ina jin waɗansu hannuwa na ƙoƙarin raba nawa hannun daga tsakanin wuyana. Sun fi ƙarfina, don haka dole na sadaƙas, na mayar da hannuna na dama a saitin da zuciyata take, ina jin tamkar in fizgo ta daga cikin allon ƙirjin in fiddo ta waje, wataƙila idan ta ɗan sarara zan samu sassauci.
Tun daga kalmar "Da ranta." Ɗin da kunnuwana suka jiyo, ban sake gane komai da mutanen suka faɗi ba, ba kuma na son saurare, saboda duk wani abu da zan ji a yanzu ba zan so jin shi ba, domin kuwa ni 'Man Rabbuki?' kawai na so in ji, sai dai ashe lokacin bai yi ba.
Ina jin sadda aka soka mini wata allura a tsakiyar bayana.

Na ji sadda bakiɗaya tun daga ƙuguna har zuwa tafin ƙafafuwan ya tsaya da aiki. 'Me ya faru?' Na tambayi kaina, ina jin yadda komai na duniyar yake kife mini.
Tamkar wacce ake ma susar ƙadangare haka na dinga ji ana wasa da ƙasana. Babu halin kallo, saboda an sanya labule ya shiga tsakani da ƙugun nawa. Ina kallon yadda wani mai bular hula ke miƙa hannunsa ga sauran masu fararen kayan yana karɓar abin da ban san ko mene ne ba. Ba a wani ɗauki dogon lokaci ana yi ba aka kammala, sannan aka daidaita komai aka tura ni bisa wani siririn gado, wanda da a ce farkon fara tunanin na mutu ne, da zan iya cewa wata sabuwar makara ce aka ɗora ni a kai.

Daga nan kai tsaye aka zarce da ni wani ɗaki, idanuwana a buɗe ina kallon mutane sai dai ƙwaƙwalwata ta gaza tantance ko su waye, sautin koke-kokensu kaɗai nake fahimta.
Bayan an mayar da ni bisa gadon ne sauran masu fararen kayan suka fice, aka bar waɗansu wanda kayansu ba farare ba ne ba, na ci gaba da bin su da kallo ina son gano ko su waye amma na gaza. Wannan rashin gane mutanen shi ya ƙarasa ruguza dukkanin farin cikina, ina jin su suna koke-koke da alamun makusantana ne, sai dai su waye? Na saki wata irin razananniyar ƙara, jikina ya ɗauki rawa tamkar mazari. Ina ji wasu suka zo suka tallabe ni, ina jin suna yi mini tofi da alamu addu'a ce ake yi mini. 'Su wane ne?' Na tambayi kaina.
Ba a jima ba sai ga masu fararen kayan sun sake dawowa, aka ɗaura wani abu da na gaza tantance ko mene ne, ban ankara ba na ji shigar allura a cikin fatata. Da alama ƙarin ruwa ne aka jona mini.
A hankali na rufe idanuwana, ban ƙara sanin abin da yake faruwa ba sai farkawa na yi na ga Umma mahaifiyata, da kuma ƙannena zagaye da ni sun yi jigum-jigum, a cikin zuciyata na ce 'abin na yi ne.'

Ganin na buɗe idanuwana ya sanya su sakin hamdala suna ƙarasowa inda nake. Dukkaninsu kuka suke yi, suna kallo na, cike da tausayin rashin nutsuwar da suke ganin tana yawo a duk motsina. Kiran sunana suke yi suna haɗawa da sannu, sai dai na musu shiru ina ƙoƙarin haɗa kalamai amma na kasa. Shin ta ina zan fara? Juyar da fuskata na yi ina kauce wa haduwar idanuwanmu, saboda kukansu kara diririta kuntatacciyar zuciyata yake yi. Wani irin rashin kwarin guiwa ne yake yawo a saman fuskokinsu.

"Umma ko a kira wannan Malamar? Ta ce idan ta farka a yi musu magana."
Ƙanwata Safra ta faɗa tana kallon Ummanmu da fuskarta ta wadatu da ruwan hawaye.
Kai kawai Umma ta ɗaga mata sannan ta fice, babu jimawa sai ga su tare da malamar jinya, hannunta ɗauke da kwando.
"Sannu Khairi."
Ta faɗa tana ƙoƙarin cire ƙarin ruwan domin dasa sabo.
Babu abin da nake fata a yanzu sama da mutuwa ta zo ta ɗauke ni. Da za su gane da duk sun daina wannan ayyukan, saboda ba su ne a gabana ba, burina in tafi,  in tafi inda ba a dawowa. Ba zan iya zama da wannan dafin a cikin zuciyata ba. Ba zan iya ba ko kadan!

Anya kuwa zan iya barin ta ta ci gaba da kula da ni bayan babu abin da zai iya dawo mini da MARTABATA?
Da ƙarfi na janye hannuna ina sakin kuka.
"Ba na so!"
Na zaro guntuwar magana daga kasan makoshina. Maganata ta farko kenan tun bayan abin da ya faru da ni.
"Ki rabu da ni!"
Na sake faɗi ina janye hannuna.
Cikin tausayawa ta ce,
"Ki yi haƙuri Ummulkhairi. Rayuwarki ba za ta dawwama a haka ba. Ki bari a duba lafiyarki, sannu a hankali komai zai zamto labari."
"Ba zai taɓa zama labari ba. Bayan an raba ni da martabata kike tsammanin komai zai wuce? Shin kina da abin da zai iya maye mini gurbin babban abin da na yi rashi?"
Ta gyaɗa kai ta ce,
"Ba ni da shi Khairi, ba ni da abin da zai maye gurbin martabarki da kika yi rashi. Sai dai, hakan ba zai sanya ni barin ki ba, ba za ki rasa martabarki ba kuma ki rasa mai kula da ke. Kin ga an yi miki ɗinki mai yawa, sannan rabon da ki ci abinci yau kwana biyu. Wannan drip ɗin shi ne zai zama ruwa da abincinki, burina ki samu kuzari don ki fara shan magungunanki. Na miki alƙawarin sauƙi na nan zuwa gare ki. Da izinin Allah madaukakin Sarki."

Amfani take da kalaman da take ganin za su iya sanyaya zuciyata. Sai dai ni gare ni, ba na tunanin daga yanzu har gaba da abada akwai wata kalma da za ta iya sanyaya zuciyata.
Na sakar mata hannun ba wai don na gamsu da kalamanta ba sai don girmama ƙoƙarinta na ganin ta taimaka mini.

"Ku kai ni dakin da Ummu take, ina son ganin halin da take ciki."
Raunanniyar muryata ta fito hade da wani irin sauti mai kama da kuka.

Ina ganin yadda suka hau kallon-kallo a tsakaninsu, kafin Ummata ta saki gajeren murmushi, irin murmushin da duk wanda ya gan shi sai ya tabbatar da babu nishadi ko kadan a cikinsa.
Ta matso hade da rike min hannu, sannan ta ce,
"Ki kwantar da hankalinki Khairi, Ummu na wata asibitin ta daban ana duba lafiyarta, ta jima da farfadowa, ta ce a gaishe ki. Kina kwance ne shi ya sa ban samu damar fada miki ba sai yanzu.
Ki nutsu ki bari a duba lafiyarki, idan ba haka ba kuma zan fada mata kin ki nutsuwa."

Sai na samu kaina da sauke nannauyar ajiyar zuciya, jin cewa Ummu na lafiya kadai ya sanya ni samun sassauci a zuciyata.



Amrah A Mashi❤️

DARE DUBUWhere stories live. Discover now