Page 59- Bakar Manufa

133 21 0
                                    

Page 59

Na yarda da shawarar Haidar, na latsa kiran ta. Wayar na fara bugawa ta dauka. Na ce,
"Hajiya, kamar yadda na shaida miki zan yi shawara da mijina, to mun yi din. Sai ki fada min sadda kike da dama, ki same ni a Office mu yi magana."

Ta yi murmushi,
"Ba na son mu hadu a Office ne Barrista. Kin san lamari da manya, muna da bukatar privacy gaskiya."

Haidar ya daga min kai alaman in amince. Na ce
"Okay babu damuwa. Ki fada min inda za mu hadu, gobe daga Office sai in same ki."

Muryarta ta bayyana farincikin jin na amince, ta ce,
"Akwai guess house din Honorable Sani Giginya, da ke kan sabon titin Kwado. Mind if we meet there?"
Nan ma daga min kan Haidar ya yi.
"Yes ba damuwa. Zan zo wurin biyu na rana, in shaa Allah."
Daga haka muka yi sallama, ta yanke kiran.

Washegari daga wurin aiki na wuce inda ta kwatanta min, a can muka hadu da Haidar kamar yadda muka tsara ba zan je ni kadai ba. Ya yi zaune a cikin motarsa ni kuma na shiga ciki. Maigadi ya san da zuwa na, shi ya yi min iso zuwa babban parlor mai cike da kayan more rayuwa.

Can zaune na hangi Hajiya Lami, sanye da wasu irin kaya na alfarma, hannu da wuyanta duk gwalagwalai. Sannan a kusa da ita akwai wata budurwar da a shekaru ba za ta wuce Nusaiba ba. Sai kuma Honorable Sani Giginya zaune, suna hira na karasa ciki.

Gani na ya sanya su yin shiru tare da mayar da hankulansu gare mu. Na gaishe su cikin girmamawa, sannan ta ce,
"Ki zauna da kyau Barrista."
Na zauna kujerar da ke kusa da tata.

Kwala kiran wani ta yi ta ce a kawo min abun motsa baki. Babu jimawa sai ga wani matashi dauke da babban tray ya ajiye a gabana. Na dauke duba na daga tray din, na kalli Hajiya Lami. Na ce
"Hajiya, sauri nake na bar yara a gida ban koma ba daga wurin aiki."

Ta kalli yarinyar da ke zaunen, ta ce mata ta tashi ta shiga ciki ko kuma ta fita waje. Sannan ta dawo da hankalinta gare ni.

"Kamar yadda na fada miki jiya, ko nawa kike so zan biya ki a kan ki yi min wannan aikin Barrista. Wannan yarinyar da kike gani, ita ce aka yi wa fyaden, 'yar kanwata ce ta zo daga birnin London. To an rasa gane ko su wane ne suka aikata, don ba ta san su ba, kuma babu kowa a wurin da aka yi din. A takaice dai, babu wani suspect.
A lokacin an kai ta asibiti, kuma muna da duk wasu medical reports a ajiye.
A takaice dai Barrista, so nake mu dora alhakin fyden sunkutukum ga dan gidan abokin hamayyarmu, Alhaji Kabiru Darazo, saboda muna son bata masa suna, mu bata tafiyar tashi, musamman ganin yadda mutane ke son shi, suke son zuri'arsa saboda kamilanci.
Na san ba zai zauna ba shi ma, idan aka kai masa sammaci dole za su nemi nasu lauyan, watakila ma wanda ya fi ki. To ban damu ba ko mu ci ko mu fadi. Babban burina dai ki kawo hujjojin da za su gamsar da mutane cewa yaron ya aikata, ko da ba su gamsar da alkali ba."

Kallon ta nake har ta yi ta gama tare da mamakin abin da take son in aikata din. Wannan wace irin rayuwa ce wadda mutum ke zabar duniya a kan lahirarsa? Me ya sa mutane suke manta cewa Allah na ganin kowa da komai? Me ya sa suke manta cewa akwai mutuwa akwai hisabi, sannan akwai ranar tashin alkiyama? Wannan wane irin mummunan kazafi ne suke son dora wa wanda bai ji ba bai gani ba kawai saboda neman duniya?
Jin na yi shiru ina kallon ta ya sanya ta zaro bandir guda na Dalar Amurka, kuma duk kwaya daya da ke cikin bandir din, Dala dari ce. Na kalli kudin sau daya hade da janyo kallo na don ma kar su shagaltar da ni.
Wani bandir din ta sake daukowa ta dora a kan na farkon. Kafin in dauke kallo na ta sake dire wani; bandir uku kenan.
Na dago na kalle ta, sai gani na yi ta sakar min murmushi.

DARE DUBUWhere stories live. Discover now