Page 37- Kambun Baka

146 20 2
                                    

Page 37

Ji na yi ba zan iya hakuri da tafiyar tamu a haka ba ya sanya ni shagwabe murya, cikin sanyin jiki na ce,
"To wai ba na ba ka hakuri ba? Me kuma na yi dan Allah?"

Ya dan juyo ya kalle ni hade da yin murmushin gefen baki da ya yi matukar yi masa kyau.
"Raina ne duk a bace."
"Duk saboda kawai mayafin nawa?"
Na tambaya cikin mamaki.
"Ba kawai ba ne. Na fada miki ina da kishi sosai Baby girl. Yanzu haka za mu je duk idanuwan kowa su dawo kanki, asibitin cike da maza ma'aikata. Ke ko dai gida za mu juya ne ki sauya dressing?"

Baki na tabe cikin sigar rarrashi na ce
"Haba dan Allah baby boy. Har mun riga mun fito kuma sai ka ce mu koma? Ni dai wallahi..."
Na yi shiru ina turo bakina gaba.

Lumsassun idanuwan nan nashi masu tafiya da zuciyata ya saita a cikin nawa, bai ce komai ba har ya dauke su daga gare ni yana ci gaba da tukinsa, amma yana yi yana kallo na tare da aika min da sakon da ni kadai na san ko mene ne a cikinsa. A haka har muka isa asibitin.
Har zan fita ya danna lock. Na juyo na kalle shi ina jiran jin ba'asi, sai cewa ya yi,
"Mami na nan. Ki yi hakuri da abin da zai iya faruwa don har yanzu ba ta sauko ba. Ki kai zuciyarki nesa kin ji? Sannan kar ki zauna, kina yi wa Nusaibar ya jiki ki fito. Zan jira ki."

Da sanyin jiki na fita bayan ya bude min motar ya sanar da ni lambar dakin. Ko da na isa daidai gaban dakin sai da gabana ya ce ras! Ina tsaye sai jin motsi na yi, na waiga na ga Sista Khadija ce, hankali a tashe na gaishe ta, ciki-ciki ta amsa min hade da bude dakin ta shiga. Ni kuwa ji na yi tamkar in juya in bar wurin ba sai na shiga ba. Sai kuma wata zuciyar ta tunatar da ni cewa Nusaiba ce fa, yarinyar nan da ke matukar so na da zuciyarta daya. Bai kamata in yi haka ba, gara in juri ko ma me zai faru tunda Allah Ya riga Ya gama tsara komai.

Na kuwa bude kofar a hankali na shiga. Har kasa na tsugunna na gaishe da Mami amma ba ta amsa ba, na dan daga fuskata na dube ta sai na ga ba ma ta ni take ba, ba ta kalle ni ba sai Khadija da take ja da hira.
Na matsa bakin gadon Nusaiba, tun daga nesa take sakar min murmushi har na karasa gadon.
"Oyoyo matar Yaya."
Ta furta cikin fara'a.
Na sakan mata murmushin ni ma tare da yi mata ya jiki.

Ji na yi Anti Khadija ta ce
"Na rasa me ya sa kika kasa yin komai a kan auren nan har yanzu Anti Radiya. Shin wai Haidar din ya fi karfinki ne ko yaya? Bai fa kamata a zuba masa ido ya kwaso sauran 'yan ta'adda ya kawo mana cikin zuri'a ba. Tunda an riga an daura auren ba tare da an shawarce ki ba, ai ke ma kina da damar da za ki sanya shi sakin yarinya ko diyar gidan uban waye!"

Dukkan zantukanta na farko ba su kona min rai ba kamar zagin da ta yi min. Mahaifina ya rasu tuni, to don me yana kabarinsa za a aika masa da sakon zagi?
Wani irin zugi na ji zuciyata na yi, ta yadda na kasa shanye zagin nata kawai na juyo a hasale na kalle ta. Ba ita ta haifi Haidar ba ballantana in kyale ta albarkacin haihuwarsa. Haka kuma ba uwa daya uba daya suke ba da za ta iya cin albarkacinsa. Cikin zafi na ce
"Ki daina zagin mahaifina Anti Khadija, yana can cikin kabarinsa. Idan ma abun ne ba shi ya yi muku ba, ba shi ya ce a daura auren ba. Hasali ma bai san wainar da ake toyawa ba. Saboda haka ba ki da hujjar da za ki zage shi."
Daga haka ban kuma fadin komai ba, ko Nusaibar da ke kiran sunana ban koma ta kanta ba na fice daga dakin. Tamkar kafafuwana ba za su iya daukar gangar jikina ba haka na isa wurin motar Haidar. Da karfi na bude na shige, na soka fuskata a cikin cinyoyina ina sakin wani irin kuka mai zafi da ciwo.
Hankalinsa tashe ya hau tambaya ta ya aka yi amma na yi shiru ban ba shi amsa ba. Tayar da motar ya yi muka bar asibitin, ya latsa kiran Nusaiba.

"Khairi ta fito min tana kuka, akwai abin da ya faru a nan ne?"
Ban san me ta fada masa ba sai ji na yi kawai ya ajiye wayar tashi. Cikin bacin rai ya ce
"Lokaci ya yi da zan gwada wa Khadija cewa ni na yanke ra'ayina kuma babu wanda ya isa ya sauya shi. Ba zan lamunci shisshigi ba alhali ni ban shiga rayuwar kowa ba."

Ban ce masa komai ba sai kukana da na ci gaba da rerawa, ban kuma dago kaina ba har sai da na ji ya yi parking a gefen titi. Na daga kaina na ga babu kowa sai giccin motoci da sauran ababen hawa. Sannan na kalle shi ina jiran jin karin bayanin dalilin tsayuwar tamu.
Ban ankara ba kawai sai ji na yi ya kama hannuwana duka biyun ya saka a cikin nashi. A karo na farko da na ji wani irin yanayi ya darsu a jikina.
Ya janyo ni a hankali na fado cikin jikinsa, sannan ya saki hannuwan nawa, ya dago fuskata ya saita ta da tashi.
A cikin idanuwansa nake hangen tafasar da zuciyarsa take yi. Na yi saurin runtse idanuwana saboda bakon yanayin da ke ziyarta ta. Kafin in sake budewa na ji tattausan lips dinsa a kan nawa. Na gaggauta bude ido ina kokarin janyewa amma ko kadan bai ba ni damar hakan ba. A hankali ya saki guntun peck, kafin ya dago idonsa ya kalle ni, a take jikina ya karasa mutuwa.
"Ki daina kuka..."
Ya fada a hankali idanuwansa a cikin nawa. Na jinjina masa kai wasu hawayen na saukowa.
Sake hade lips dinmu ya yi wuri guda, a wannan karan ba iya peck ya ba ni ba, lebena na kasa ya kama, ya yi masa wata irin tsotsa da ta gigita tunanina, kafin a hankali ya karasa cusa bakin nashi cikin nawa, ya janyo harshena ya hau yi masa wata irin tsotsa a hankali.
Fiye da minti biyu yana kissing dina cike da zallar soyayya, kafin ya dakata ya janye bakin nashi daga nawa, bai kuma daina kallon cikin idanuwana yana aika min da tarin sakuna ba.

"Za ki daina kukan ne ko sai na kara wani abun?"
Cikin daburcewa na ce,
"Zan daina baby boy...Allah kuwa na ma daina."
A tsorace sosai nake, ga wani irin yanayi da na shiga ciki, jikina sai rawa yake yi.

Raba jikin nashi ya yi da nawa, ya mayar da ni kan kujerata tare da daidaita min zama, sannan shi ma ya daidaita nashi zaman, ya kunna motar muka tafi.

Babu wanda ya sake cewa uffan har muka isa kofar gida, daga gefe ya faka sannan ya janyo hannuwana ya saka a cikin nashi. Cikin sassanyar murya ya ce,
"Ki yi hakuri baby girl, I mean, ki yi hakuri da dukkan komai. Bai kamata ba a ce tun kafin ki shigo gidana har kin fara facing ire-iren wadannan abubuwan. In shaa Allahu komai ya kusa zuwa karshe."

Ban ce komai ba sai jinjina kaina da na yi ina kokarin gayyato wa kaina karfin hali.

"Idan kuma na ji labarin ko hawaye kin fitar yau din nan, zan dawo, abin da ya fi wanda ya faru shi zan miki. Kuma a kofar gidan nan. Idan ta kama ma daga nan sai mu wuce gidanmu. Kin ga sai su Safra su biyo ki da sauran kayanki ko?"

Na turo baki ina ganin shi yana dariya.
"This is not funny baby boy."
"Ni ma ban ce abin dariya ba ne ai. Gaskiyata ce na fada miki."
Ya ba ni amsa yana ci gaba da dariyar.
"Tabdijam! Da ina ga da ba zan sake hada ido da kowa ba. Ai abun da kunya a raka bako ya ruga."
"Ba wata kunya fa. Sai ma kin samu ciki za ki fara fita. In ya so sai ki kalli mutane da kyau su ma su kalle ki."

Dariyar ni ma na kama yi ina kallon yadda yake kallo na cike da kauna.
"Da gaske nake zan saka kannena su zuba miki ido, matukar suka fada min kin yi kuka to kin san sauran."
"Ba ma zan yi ba Baby boy, ai ka riga ka yakice duk wanin kuncin nawa. Fatana dai Allah Ya daidaita lamarin, ya juya ra'ayin Mami ta so ni ko da rabin yadda ta dauko ne a baya kafin a shiga tsakaninmu."
"To amin. Ai tana son ki fa, bakin da ya furta so ko ya furta ki ba gaske yake ba. Tun farko da na ba ta labarinki, na fada mata irin kaunar da nake yi miki da kuma kokarin da kika yi wurin aiki, wallahi ba ki ga yadda ta nuna farincikinta ba, ta zaku da ta gan ki. Kambun bakan mahassada ne kawai ya kama ta..."
Na dafe bakina ina dariya.
"Anti Khadijar ce mai kambun baka?"
Na tambaye shi cikin muryar dariya.
"E mana, tunda bakinta ya yi tasiri ga Mami ai dole in ce tana da kambun baka."
"Allah Ya shirya min kai."
"To amin."
Ya amsa yana dariya. Tunowa na yi da maganarmu da Umma. Na shaida masa yadda muka yi da ita a kan cewa karshen wata za a yi hidimar biki in tare.
"Lallai, har wani karshen wata za a kai? Ni wallahi na dauka ma nan da sati daya ko kwana goma za a yi komai a wuce wurin."
Na kalli fuskarsa ganin yadda ya dakune ta, duk sai na ji wani iri kuma saboda ba na son bacin ransa kamar yadda shi ma din ba ya son nawa.

"Ka yi hakuri my handsome. Daure fuskan nan sam ba ya yi maka kyau Allah."
"Ban yi don ya yi min kyan ba ai da ma."
Ya gatsine min baki kamar wani mace.

Na kuwa sanya hannu na murje labban nasa har sai da ya saki 'yar kara yana dariya.
"Kin ci bashi wallahi cupcake. Zan rama."
Na yi saurin bude motar na fice ina masa gwalo. Sai da na tafi sannan na juyo na daga masa hannu ina dariya na tsallaka na shige gida.



Amrah A Mashi❤️

DARE DUBUWhere stories live. Discover now