Page 38- Kai Amarya

154 22 0
                                    

Page 38

Sakon gaisuwa, tare da jinjina ga masoya labarin DARE DUBU...a duk inda kuke. Na gode kwarai da soyayya tare da jimirin bibiyar labarin.
Matar Haidar na gaishe ku kyauta.

***
Kwana biyu muna waya da Nusaiba take shaida min an sallame ta. Na ji dadi sosai na kara yi mata fatan samun sauki. Ga shi babu halin zuwa duba ta gudun kar a sake fada min abin da zan kwana yana cin raina. Duk da na san ko da a ce na ce zan je din ma Haidar ba zai bar ni ba gudun bacin rayuka. Maganin kar a yi, kar a fara.

A lokacin da ya rage sati daya bikin tarewa Haidar ya zo, muna zaune a cikin mota daddare ya zaro wayarsa ya fara nuna min admission din da ya samar min a Umaru Musa University.
"Wannan shi ne big surprise din da na ce zan yi miki. Ba tare da sanin kowa ba na sa kanwata Halimatu ta dauko min takardunki duk wanda na san za a bukata. Ga shi dai an saman miki Law. In shaa Allahu nan da wata daya za a fara registration, daga nan sai lectures. Ina fatan hakan zai faranta miki rai kamar yadda nake fata."

Tsantsar farinciki ya sanya ni shigewa cikin jikinsa ina sakin wata irin dariyar jin dadi. Har ga Allah a yanzu ina son karantar Law, musamman saboda abin da ya faru da ni; ina son supporting mata 'yan'uwana da ake haike mawa. Karin abin da ya sanya ni jin ina son karantarsa, tun da Mami ta ki ni saboda kaddarar da ba ni na janyo wa kaina ba. Yadda na muzanta, da a ce Haidar ba tsayayyen mutum ba ne da shi kenan an cusa min bakincikin da ya jima da shafewa daga babin rayuwata.
Idan kuwa har ana samun mata lauyoyi watakila za su yi tsayuwar tsayin-daka don ganin an samu saukin yawaitar fyade.

Na jima a cikin jikinsa ina sauke ajiyar zuciya, kaunar Haidar na rubanya kanta, ina jin cewa idan har ba Haidar ba to lallai sai dai in fasa yin aure gabadaya.

Dago fuskata ya yi a hankali ya dinga shafawa, tun daga karan hancina har zuwa dan karamin bakina da ke washe, cike da farinciki. Ba zato ba tsammani sai ji na yi ya hade bakinsa da nawa, wata irin kyakkyawar tsotsa ya yi masa kafin ya saki, ya dinga sumbatar ko'ina ya samu na jikina tun daga wuya har zuwa kafadata da ke dan bude saboda wuyar rigata da ke down shoulder.
Jin lamarin yana neman fin karfina ya sanya ni kokarin raba jikina da nashi amma bai ba ni damar hakan ba. Romancing dina yake sosai har sai da jikina duk ya gama macewa na hau yi masa kukan shagwaba.
Cikin sanyin muryarsa, ya ce
"Saura kwana nawa ne wai ya rage?"
Na yi masa shiru ina turo bakina. Ai kuwa sai sake cafkar bakin nawa ya yi ya ci gaba da aika min sako ta ko'ina cikin bakina.
Da kyar na samu na kwaci kaina daga hannuwansa, tun daga nan kuwa sai muka koma wasan buya. Ban sake yarda na hadu da shi ba, idan ma ya kira ya ce zai zo sai na san yadda na yi na dakatar da shi, ko kuma in fada masa ya zo da rana mu gaisa kawai ya tafi.

An gama tsara komai, walima da yinin biki ne kawai Umma za ta yi, ta gayyaci mutane sosai don ni har mamaki ma na yi na adadin abincin da na ji ta ce wai duk za a dafa na bikin. Haidar shi ya dauki nauyin duk wani abinci da za a ci, shahararriyar mai girkin nan Amrah's Kitchen ita aka ba order, tun daga kan su fried rice, fried spaghetti, peppered chicken, moimoi, salad, sai kuma natural drinks dangin su zobo, kunun aya, tamarind juice, har ma da chapman (ku tuntubi Amrah's Kitchen a Abuja domin kayatattun abincin biki har ma da snacks kowanne iri. 07037603276 ko kuma instagram da TikTok a Amrah's Kitchen).

Da farko har sai da Umma ta hana shi, a ganin ta ba hakkinsa ba ne ciyar da 'yan taron biki, amma ya nace a kan ya yi niyya, yana tausayinta sosai don haka idan har ta kashe kudinta sai dai don ra'ayi kawai.

Anti Maryam ita ta dinga kokarin nema min ingantattun kayan mata ta hanyar wata kawarta da ke Sokoto. Haka ta dinga dirka min su tun ina ki har na fara karba da kaina, don ni kaina ba karamin sauyi nake ji a jikina ba saboda har da magungunan sanyi ne take ba ni.
Sau biyu ana ba ni dahuwar kaza mai cike da abubuwa, da kyar na cinye don a kalarta babu birgewa a baki ne take da dandano mai dadi.
Su dai burinsu komai nawa ya koma tsaf-tsaf tamkar ban taba haduwa da wata kaddara a baya ba.

DARE DUBUWhere stories live. Discover now