Page 41- Karshen Munafuki...

159 21 10
                                    

Page 41

Tsananin nishadin da ake yi a cikin dakin ya sanya wata nurse shigowa, amma tana zuwa ta ga har da marar lafiyar ne ake nishadin ya sanya ta yin murmushi ta ce,
"Alhamdulillahi. Na zo ne fa da nufin cewa ku rage hayaniya saboda mara lafiyar, ashe ma ta ji sauki sosai tare da ita ake yin nishadin. Hakan ya yi kyau sosai ai. Da ma kuma an fi son mai cutar hawan jini ta kasance a cikin nishadi. Don haka a ci gaba da gashi..."
"Suya sai ranar sallah."
Nusaiba da Hannatu suka hada baki wurin fadi. Nurse ta kama hanya ta fice tana murmushi.

Ana cikin haka sai ga Anti Khadija ta shigo dakin. Ganin ta ko kadan bai sanya ni fargaba ba kamar yadda na saba a baya, farincikin karba ta da Mami ta yi ya sanya na ji ko kadan ba na jin haushin ganin ta. Tana zuwa ta fara harare-harare, na lura da kallon da Hannatu ke yi mata na alamun ba ta ji dadi ba.

"Aunty Radiya ya karfin jiki?"
Ta furta bayan ta isa kusa da Mami. Mamin ba ta sakar mata fuska ba ta amsa.
"Sai kuma kika bude ido kika gan ki tare da kingi..."
"Ya isa haka Khadija. Ba na son wannan maganar."
Duban Mamin sosai Anti Khadija ta yi, ta ga dai babu alamun wasa ko kadan a cikin maganarta. Ta ce
"Wai Aunty Radiya kin kuwa gane wa nake nuf..."
"Na ce ki bar maganar ko? Idan kin san kin zo ne ki karasa ni don Allah ki tafi ni dai. Kin gama shigar da ni a kan yarinyar da ba ta ji ba ba ta gani ba. Da ma can ina son ta ke ce kika shiga tsakaninmu."

Kame-kame Anti Khadijar ta hau yi amma Mami ta ki ba ta damar yin magana. A karshe dai dariyar yake ta koma yi, kafin ta ce da Hannatu ta tashi su tafi gida.
"Momi ni dai ina nan, da daddare idan su Yaya Haidar za su koma sai su sauke ni gida. Ko Aunty Khairi?"
Ta juyo ta kalle ni tana murmushi.

Tsawar da Anti Khadijar ta sakar mata dukkanmu sai da muka kalle ta. Ta kuma tilasta ta a kan dolenta ta tashi su tafi. Ba don ta so ba, ta turo baki ta bi bayan mahaifiyar tata suka tafi. Har sun kai bakin kofa ta juyo ta kalle ni hade da fadin,
"Sai na zo har gida kawo miki ziyara Aunty Khairi."
Na sakan mata murmushi.
Fizgar ta Anti Khadijar ta yi hade da banko kofar suka fice.

Mami ta dube ni da annuri a fuskarta, duk sai tausayinta ya kama ni ganin yadda bakinta yake jirkice amma da tsiya murmushi take yi.
Ta kira sunana na amsa.
"Ki zuba min abincin da kika zo da shi, da kanki nake so ki ba ni a baki."

Wani irin dadi na ji. Na kuwa gaggauta zuba mata makimanci a cikin plate, sannan na zuba miyar kazar a wani bowl daban, na matsa inda take.
Ina jin kunyar zama kusa da ita amma sai cewa ta yi,
"Ni ba surukarki ba ce Khairi, Mamanki ce. Idan kina dari-dari da ni sai in ga kamar ba ki yafe min ba ne."

Jin haka ya sanya na saki jiki na zauna kusa da ita, a hankali na tallabo ta cikin jikina, na zuba miyar a cikin shinkafar sannan na hau ba ta a hankali tana karba, har sai da ta dan ci da yawa kafin ta ce ya ishe ta. Haidar ya zuba ruwa a kofi ya miko min na ba ta.

"Na gode sosai, Allah Ya yi muku albarka."
"Amin Mami..."
"Ya ba ku zuri'a tagari."
Ta karasa tana murmushi.

Nusaiba da Aunty Jamila ne suka amsa. Don a lokacin ita Aunty Salima ta tafi don yin wanka ta dawo.

Da yamma na kira Haidar cewa ya zo ya dauke ni in je gida in dafa wa Mami abincin dare amma ya ce in bar shi kawai zai sayo da yawa duk mu ci. Na so kwarai in girka matan don na ji dadin yadda ta saki jiki ta ci nawa dazu amma ya tilasta a kan in bar shi din.

Sai bayan mgahrib ya zo dauke da robobin abincin Magama restaurant. Tuwon semo ne da miyar danyar kubewa, sai wata ledar kuma fresh sugarcane juice mai sanyi.

DARE DUBUWhere stories live. Discover now