Page 29- Soyayya

154 26 3
                                    

Page 29

Wasu irin tsumammun hawaye ne na ji suna sauka a bisa kumcina, wadanda suka jima suna son saukowa ina danne su saboda son shafe duk wani babin fyaden da aka taba yi min.
Na dukar da kaina, kuka nake sosai, irin kukan nan da bai da sauti mai yawa, sai dai karkarwar jiki.
Ganin yadda kafadata ke hawa da sauka ya sanya shi fadin
"Kina tayar min da hankali Khairi, kukanki daidai yake da duk wani tashin hankalina. Gabana yana faduwa, ina jin kamar ban samu karbuwa ba ne."

Ta ina ma zai samu karbuwar kuwa bayan babu tsarin aure a rayuwata? Me ya sa yake neman dagula tsarina a lokaci guda? Na tabbata idan Umma ta ji zancen nan da gudu za ta amince, ta kuma tilasta min ko ina so ko ba na so.

"Ban zo nan da nufin sanya ki kuka ba Khairi, ki daina zubar min da wannan precious hawayen naki don Allah. Ba na so."
Rarrashina yake sai dai ko alama ba shiga ta yake ba. Yadda aka haike min nake tunawa, sai kuma darajar nan da ake yawan nanata duk budurwar da ta yi rashinta ta yi babban rashin da babu abin da zai iya cike gurbinta.
Budurcin nan da kowacce mace ke burin isar da shi ga mijinta; yadda nake yawan jin ana girmama budurci amma ni na yi rashin nawa. To me ya yi saura wanda zan kai wa mijin aurena?

Ina kallon sa ya dafe keya da dukkanin tafukan hannuwansa, ya ma rasa abin da zai fadi sai idanuwansa da nake jin suna bibiyar duk wata halitta tawa.

Mun jima a haka kafin na ce
"Ba zan boye maka komai ba Sir, ba zan iya aurenka ba. Ba wai don ina kin ka ba face dalilai guda biyu..."
Na yi kokarin shanye kukana, sannan na ci gaba da fadin
"Dalili na farko shi ne aure shi ne abu na farko da na cire rai da shi a rayuwata. Sannan abu na biyu, ina tsoron abin da zai je ya dawo..."
"Kamar me kenan?"
Ya yi saurin tarba ta.
"Gori..."
"Wane irin gori? Wace irin magana ce kike yi haka Khairi for God's sake kamar wani dan yaro? Ina ce na san da raping din naki da aka yi amma duk da haka na kawo kaina? Ya kamata ki san ni ba irin wasu mazajen ba ne, na san me nake yi fa."

Shiru na yi ina samun 'yar nutsuwa da kalaman nashi, sai dai ni ba wai shi din nake ji ba, dangi; ba lallai ba ne su karbe ni tare da mummunar kaddarata ba.
Kamar ya san abin da nake tunani kuwa sai cewa ya yi
"Ba wani zai zauna min da ke ba, ni na ji zan iya. Da kaddarar da ta taba afka mikin nake son ki, don zan iya cewa ma tana daga cikin dalilan da suka assasa kaunarki a cikin zuciyata. Da tausayinki na fara, ashe da gaske ne da ake cewa tausayi soyayya ce. Har ga shi zuciyata ta cika taf da kaunarki, irin cikar da ke daf da fara ambaliya."
Ya saki guntun murmushi.
"Da dukkanin zuciyata nake kaunarki Khairi. Burina ki zama matata nan da dan lokaci kankani."

Ya daure ni mini zuciya tam! Sai kawai na yi shiru ina tunanin ta yadda zan iya kauce masa. Kafin in samu mafita ya mike tsaye tare da fadin,
"Idan kin shiga ki turo min kanwata Halimatu. Sannan Allah na ganin ki idan kika ci gaba da zubar min da tsadaddun hawayen nan naki. I love you so much Buttercup."

Tamkar wadda aka daure wa kafafuwa haka na ji, na yi yunkurin tashin amma sai ji na yi tsayuwa ma tana Neman gagara ta. Da kyar dai na samu na taka na shiga daki. Tun kafin in fada wa Sadiya sakon kiran ya da yake ta fita don babu tazara ana iya jiyo duk maganganun da ake yi.

"Allah Yaya wannan kukan samun wuri ne kike yi. Ki samu mutum mai yi miki irin wannan kaunar ai sai ki daga hannuwa ki gode wa Allah. Mutum kyakkyawa da shi ga kudi ga kwarjini, komai ya hada fa."
Tsaki kawai na yi ina jin yadda kaina ke sarawa saboda kukan da na yi. Sai ga Sadiya ta shigo da rafar 'yan dari biyar ta watso su a kan gado hade da sakin ihu tana tsalle.

"Na rantse muku mutumin nan karshe ne. Yaya Sadiya kin amince kamar yadda na amince ko kuwa dai za ki je ki yi tunani ne irin na Yaya Khairi?"

DARE DUBUWhere stories live. Discover now